← Book details A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 36

Sashe 24

A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki ne ya cika ta "Ashe ya gane ni? Taya ya yi saurin gano ni haka? Wannan na nufin bai manta da ni ba kenan?"

Muryarsa ta dawo da ita daga tunani inda ya ke cewa "Baby ko ba ke bace? ko abinda na saba ji a kunnena ne yau ya zo min a kiran waya? Lallai na fara zaucewa." Ya faɗa cikin rawar murya.

Jin haka yasa ta tattaro duk wata nutsuwarta, daƙyar ta haɗo kalmomi ta ce "Ni ce yaya Sameer, Mimienku ce, ya kake? Ya karatu? Da fatar kana nan lafiya." Cikin mutuwar jiki ta ke zance domin a kunyace take, saboda ba ta manta irin cin kashin da ta masa ba, a lokacin da yake neman aurenta.

Komawa ya yi ragwaf ya zauna kan kujerar ya na faɗar "Sweety ba lafiya ba, ina nan ciwon son ki ya murƙushe ni, ba ni da aiki sai tunaninki, ba na iya karatun da ya kawo ni, Dubai ta kasance mun gurin jinya a maimakon gurin karatu, na shiga wani mugun yanayi Baby, na sani yanzu ki na can zaune ɗakinki cikin farinciki yayin da na ke cikin damuwa, idan ba ki manta ba a baya na gaya miki muddin ba ki aure ni ba tabbas zan iya rasa raina ko na rasa hankalina, to hakance ta faru ina daf da rasa hankalina Baby ki taimake ni..." Daga haka ya fashe da kuka cikin wani yanayi mai ban tausayi.

Hakan ya kashe mata jiki sosai, lura da ta yi cewa idan ta cigaba da saurararsa tabbas su na daf da faɗawa halaka musamman shi, hakan ya sa ta fashe da kukan tausayinsa tare da kashe wayar ta ajiye.

Cigaba da kukanta ta yi, a zuciyarta ta ke cewa "Shin yaya Sameer ya manta cewa ni matar aure ce ya ke faɗar waɗannan kalaman."

Nan ta ke ta ji ta yi nadamar biyewa son zuciyarta, ga shi ta saka wannan bawan Allahn cikin tashin hankali da ɗimaucewa.

"Kaicona ni Zuhra, Daddy baka cancanci wannan sakayar daga gare ni ba, yaya Sameer ku yafe min." Ta faɗa ta na cigaba da kukanta.

®®®®®®®®®®

Sameer kuwa jin ta na kuka ya saka shi gigicewa faɗar "Ya ke Baby kuka ki ke?"

Jin ta yanke kiran ya saka shi fara neman layinta hankali a tashe ya na kuka.

Kusan sau biyar ya na kira amma bata ɗaga ba, hakan ya saka shi faɗuwa a ƙasa ya na cigaba da kuka ya na sambatun kiran "Sweety meyasa ki ka mun haka? Me na rasa da ki ka ƙi ni? Me wanda kika aura yafi ni da shi?"

Wisam da Zaroon da su ke zaune a falon kowannen su ya na rungume da budurwarsa, kallonsa su ke cike da tausayawa.

Wisam ne ya tashi, ya je gabansa ya fara rarrashinsa faɗar ya ke "Haba Sam! Me ye haka? Ka zama namiji mana, akan mace ne ka ke wannan kukan? Ka da ka ba ni kunya mana."

Maliha budurwar Wisam ce ta ce "Haba my love, ka tausaya masa mana, shi kaɗai ya san me ya ke ji a zuciyarsa, ina ga kamar ba ka gama fahimtar miye so ba."

Zaroon ne ya taso shima ya ƙarasa wurin su ka tayar da shi zaune, Zaroon ya dubi budurwarsa ya ce "Janan ba ni kwalbar barasar nan."

Ɗaukowa ta yi ta na kwarkwasa ta iso gun ta miƙa masa.

Buɗe bakin kwalbar ya yi ya miƙawa Sameer ya na faɗar "Karɓi wannan Sam, ga maganinka ka na sha shikenan."

Ai kuwa ba musu ya karɓa ya kwankwaɗa tare da komawa ya lafe jikin kujera ya na cigaba da sambatun kiran sunan Mimie.

®®®®®®®®®

Saheen kuwa ya gama susucewa kullum ya na gidan Mommy maƙale, abin har ya fara bawa Ruma tsoro, "Anyah! Mommy ba wani abun ta aikatawa Saheen ba kuwa?" Wannan tambayar ce ta faɗo ranta.

Ras ƙirjinta ya buga da ƙarfi "in kuwa hakane tabbas Mommy ta cika mai son zuciya."

Haka Saheen ya ke yiwa Mommy ɓarin kuɗi, ita kuwa Ruma tausayinsa ne ya saka ta fara kula shi.

Farincikin Mommy kasa ɓoyuwa ya yi har sai da ta kira ƙawarta Hajiya hafsat ta shaida mata magani ya ci, su ka yi ta murna anan ta ke labarta mata irin barin naira da Saheen ke mata da ɗan abin hannunsa, kafin ta shiga dukiyar Mahaifinsa.

®®®®®®®®®

A haka lokaci ya cigaba da ja, a wani zuwa da Bassam ya yi gida anan ne komai ya ƙara rikicewa Mimie, domin bayan komawarsa Kano ya tafka hasarori waɗanda ba sa faɗuwa duk ya fara tsiyacewa motar da ya ke hawa ma ya na gaf da zuwa gida aka sace ta.

Da dawowarsa gida ya sami matarsa da zancen ta taimaka masa da kuɗi ya ja jari koda aro ne ya na so ta ba shi, ita kuwa saboda tausayin mijinta ta ba shi dama anan ta ke cewa "Uncle ai dukiyata taka ce, da ni da duk abinda na mallaka mallakinka ne, ka yi yanda ka ga ya dace."
Ai kuwa ya yi farin ciki sosai, da wannan damar ya yi amfani ya je ya siyar da tarin kayanta da su ke a can gidansa ajiye ya karɓi kuɗi da zimmar ya na komawa Kano zai siyo wa su kayan a fara kasuwanci.

Tun dawowar su gidan nauyi ya dawo kansu, domin duk wani cefane na gidan shi ke yi tun da babansu baya raye, matarsa kuwa ta kasance ita ke yin duk wani girkin da za'a ci agidan, sai dai idan ta gama ta kai masu na su, sauran kuma ta ci ita da mijinta.

Duk wannan abin da ake bata sanar da kowa ba ta yi haƙuri ta jure, sai da ta ga abun ya fara yawa ne ta sanar da Mama ta na kuka tare da neman addu'ar ta da yafiyar ta.

A wannan dawowar da ya yi ne kuma Zinnira ta zo ta tare a gidan, nan fa abubuwa suka ƙara caɓewa Mimie, domin baƙar magana da habaici kam kullum sai ta sha shi, kasancewar Zinnirar na matuƙar son Bassam tun kafin ya yi aure, shi ne bai ba ta fuska ba.

Ana haka ne ta nemi izinin zuwa ganin gida daga can kuma ta na so ta wuce Abuja gun Mommy da kuma gidan Daddy, ba musu mijin nata ya amince mata, amma ita kaɗai za ta tafi kasancewar bai jima da zuwa ganin gidan ba lokacin komawar sa bai yi ba, dama can sun samu hutun makaranta.

Da haka su ka yi sallama ta wuce Kano satin ta ɗaya anan ta wuce Abuja gidan Daddy ta sauka domin tunawa da ta yi cewa yanzu bata da gurbi a zuciyar Mommy, amma a ranar ba ta kwana ba sai da ta je gidan Mommy ta kwana biyu, a can ne ta ga irin susucewar da Saheen ya yi akan Ruma.

Ta yi murna sosai da wannan haɗin, acewar ta idan ba ta auri yaya Sameer ba ga yar uwar ta za ta auri yaya Saheen ta san wannan haɗin zai rage ma su damuwar da ta jefa zuciyoyinsu aciki.

A daddafe ta kwana biyu gidan saboda hantarar da ta ga Mommy na yi mata.

®®®®®®®®®

Rashin sani ya fi dare duhu, da Mimie ta san cewa wannan tafiyar tata za ta bawa maƙiya damar shiga tsakaninta da mijinta tabbas da ba ta yi ba.

Domin a lokacin da ta bar shi gida ne, Zinnira ta je gida ta karɓo magani hannun Mamanta wanda su ka karɓo gurin boka na karkato da hankalinsa zuwa gare ta ta kawowa Innarmu, su ka saka masa acikin abincin da ya fi so wato dambun hatsi aka basa ya ci, tun daga ranar ya fara mantawa da al'amarin matar tasa, kuma ya fara jin sabon al'amari game da y'ar uwar tasa......

Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number

08109634202

Follow me on wattpad @ummu inteesar

UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*A SANADIN KAMA*

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*

DA KUMA
*A SANADIN KAMA*

WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL

GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202

DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*BISMILLAHI RAHMANIR-RAHIM*

Page 5️⃣7️⃣↪️5️⃣8️⃣

Tun ta na Abuja ta fuskanci sauyi daga mijinta, domin ada kullum sai su yi waya sama da uku, amma a y'an kwanakin da ta yi a garin sai a kwana a yini bai kira ta ba, sai ita ce ta ke kiransa, nan ma suna gaisawa sai nemo wani uzurin ya faɗa mata, a kan dole take ƙyale shi.

Bayan da Mamy bata yi ba don ta gaya mata damuwarta amma ta kafe a kan cewa ba komai, a haka ta ƙaraci zamanta a Abuja ta juyo zuwa birnin Kebbi.

Ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya zo ganin gida ta ga ya daina kula ta kamar da, sai ma wulaƙanci da ya ke mata, bashida wani lokaci ta sai na y'an uwansa.

A gabanta zai je ya kira Zinnira su zauna a falonta su na hirarsu su na dariya.

Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yiwa Zinnira ba, anan ne ta ke samun damar gasawa Mimie magana cikin ruwan sanyi, kuma a gabanta ta ke kanainaye shi da kalaman soyayya.

Ba yanda ta iya dai dai idan abin ya dame ta ta shige ɗaki ta yi ta kuka har ta gode Allah, ta rasa wa za ta tunkara da matsalarta, a duniya bata da waɗanda su ka wuce su Baba,Mama,Daddy da kuma Mamy amma kuma rashin kunyar ta ba ta yi ƙwarin da za ta iya fuskantar ɗayan su da damuwarta ba, yaya Farida ce ta faɗo mata a rai, aikuwa ta kira ta tana kuka ta zayyane mata komai.
Chapter 24 · 0% Book details