Sashe 29
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da ba wani shagali a ka yi ba, saboda mutuwar mahaifin yaran, amma hakan bai hanawa mutane yin tururuwa zuwa ganin yaran ba.
Washe garin ranar su Baba suka koma tare da Mama saboda ayyukansu, amma a nan suka bar Mamy tare da Sagir ƙarami domin ita sai Mimie ta yi arba'in za ta taho tare da ita gaba ɗaya.
Bayan Mama ta koma Kano ne ta tura ƙanwarta Halima( da yake ita bazawara ce y'ar ƙanin babansu Maman ce da take zaune gidansu dake nan Kano)zuwa Bk don ta taya Mamy zama.
Bangaren Innarmu kuwa yanzu ta na masifar son Mimie, ji take ina ma yanzu ne Bassam ya ke raye tare da matarsa? Da sun ga gata, amma inah! Mutuwa bata barin wani don wani.
Kullu nafsin za'iqatul maut (dukkan rai sai ta ɗanɗani mutuwa)
Don haka ta sakawa ranta dangana, yanzu sosai take kula da Mimie duk da y'ar tazarar dake tsakanin su, amma duk bayan kwana biyu take zuwa birni don duba lafiyarsu.
Sannan ta ajiye ƙanwarta (Rashida) da Shamsiyya a can domin su riƙa taimakawa su Mamy.
Sosai Mimie take mamakin sauyawar Innarmu, duk da cewa ba abun mamaki ba ne, saboda yanzu ta fahimci wancan lokacin asiri Zinnira ta masu, yanzu kuma ya warware.
Wata rana da Innarmu ta je gidan, da kukanta take roƙon Mimie a kan ta gafarta mata abinda ta mata, hakama su Shamsiyya sun nemi yafiyarta, kuma duk ta yafe masu, yanzu komai ya dai-daita ba sauran tashin hankali.
Bayan sati Uku, komai ya lafa an nutsu, Mamy ta je da kanta ta sami Inna da maganar gadon yaran, su na so a raba a bawa yaran na su, ba don komai ba sai don haka Shari'a ta tanada, domin so suke su tafi da Mimie gida ta ƙarasa takabarta a can.
Ta yi hakan ne domin karɓarwa yaran haƙƙinsu, amma kwata-kwata su ba kuɗin ne a gabansu ba domin indan kuɗi ne kam ba za su nemi hakan ba don su na da shi har ba su san yawansa ba.
Ba musu Innarmu ta karɓa mata tare da cewa "insha'allahu Hajjiya za a yi yadda yak-kamata, gobe-gobenga zan biɗo malammai, don su zo a san yadda za a yin rabon. Amma don Allah kak-ku raba mu da Mimie ku batta nan don Allah."
Girgiza kai Mamy ta yi ta ce "A'a innar Sakina ba za a yi haka ba, dole ne mu tafi da ita, domin ta na gama takaba aure za ta yi."
A firgice innar ta ɗago kamar za ta ce wani abu game da hakan, kuma sai ta fasa.
Jiki a sanyaye ta ce "To don Allah Hajjiya ku bam-muna yaran, ke ga yanzu su ɗai su ka rage min jinin Bassam tunda shi ya mutu."
Ta ƙarashe zancen kamar za ta yi kuka.
Mamy ta ce "Hmmm! Mu bar muku su ku kashe su, yanda ku ka so kashe uwarsu da baƙin ciki koh?"
Ware ido Inna ta yi da sauri, haƙiƙa bata ji daɗin zancen nan na Mamy ba, amma ta sani wata rana dole sai haka ta faru tun da su su ka ja.
Cikin rawar baki ta ce "Hajjiya ku yi hanƙuri don Allah, abat tuna baya, ya riga ya wuce kuma insha'allahu za mu riƙe su da amana, ki tuna su ɗin jinina na, tayaya zan bari a walaƙanta su?...."
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202
Follow me on Wattpad @ummu inteesar.
UMMU INTEESAR CE😍😍❤️🌹🌹🌹
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 6️⃣7️⃣↪️6️⃣8️⃣
Bayan sun gama tattaunawar ne Mamy ta koma gidan Mimie.
Innarmu ta shiga damuwa amma ba yanda ta iya dole ta haƙura da koma me za a musu, domin tsuntsun da ya ja ruwa dama shi ruwan kan doka.
Har zuwa lokacin Zinnira da innarta ba su zo yiwa Innarmu gaisuwar mutuwar Bassam ba, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, damar abin dai yayan nata shi ya zo ya mata Gaisuwa kai tsaye ya juya abinsa.
©©©%%%%%©®®®
Bayan wani ɗan lokaci malamai suka zo aka raba gadon Bassam, domin tuni Alhaji Sale ya siyar da komai da yake mallakin Bassam a kano, da kansa ya zo ya kawo kuɗin, lokacin da ya zo gaisuwar Bassam ɗin.
Da yake ba wanda ya san zancen dukiyar Bassam da su Zinnira suka kwasa lokacin da take gidan, domin bai sanar da kowa ba, shi kansa bai san da wani abun ba, hakan ya sa ba wanda ya waiwaye su da zancen dukiyar Bassam, domin da ma ita Zinnirar ba ta da gado tun da ba ta da ko ƙwai a gidan, kuma bata masa takaba ba.
An raba masu gadon kamar yanda Shari'a ta tanada, an bawa Innarmu kashi ɗaya bisa shida na dukiyar, yayinda a ka bawa Mimie kashi ɗaya bisa takwas na dukiyar, sauran kuma aka barwa tagwayen kasancewarsu maza.
Bayan kammala rabon gadon ne a ka damƙawa mahaifiyar yaran nasu, aciki kuwa har da wannan gidan da suke zaune a ciki, don haka a ka siyar tare da bata kuɗin.
Account a ka buɗewa yaran na musamman a ka zuba masu dukiyar gadonsu a ciki.
A ranar da Mimie ta cika kwana hamsin da haihuwa a ranar Mamy ta ɗauke ta suka je yiwa Innarmu bankwana domin a washe garin ranar za su wuce Kano.
Innarmu har da kukanta a kan ka da a raba su, amma inah! Haka ta haƙura dole, a nan ta ƙara roƙar gafara a gun Mimie su Sakina ma suka ƙara roƙar gafara sun sha kuka a ranar rabuwar su, Ba ma kamar Shamsiyya da tafi zaƙewa a lokacin da suke kan ganiyar rashin mutuncinsu.
Mamy ta yiwa Innarmu alƙawarin za a dinga kawo mata y'an biyu lokaci zuwa lokaci don su ma su saba da dangin babansu.
Haka rabuwar su ta kasance cike da alhini.
Ranar wata Laraba suka wuce Kano, anan Mamy ta bar Mimie ta wuce Abuja.
©©©©©©©
Tun washe garin Ranar da Mimie ta haihu, Abba ya kira Sameer ya sanar da shi ƙaruwar da aka samu, domin har zuwa lokacin Sameer baya Nigeria, wancan karon sun so su dawo da shi daga Dubai don ganin halin da ya shiga, amma sai ya dinga roƙar su a kan su yi haƙuri, ba zai iya komawa Nigeria ba, amma zai canza ƙasa domin ya nisanta da gurɓatattun abokai irinsu Rajbir, tun daga lokacin ya wuce Saudiyya ya na zaune a birnin Madina, dama ya gama karatun zaman dole ne kawai, tunda zaman Nigeria ya gagare shi.
Ya yi murna sosai a zahiri, amma a baɗini ya ji ba daɗi ya so ace shi ta haifarwa waɗannan yaran har guda biyu, amma sai ga shi ƙaddara ta canza al'amarin.
Anan ne kuma Daddy ke sanar masa cewa Mijin Mimien ya rasu.
WOHOHO! Maimakon Sameer ya shiga jimami, sai wannan labarin ya zame masa tamkar Albishir, ji ya yi kamar an masa bushara da gidan aljanna, ya na ji cewa lokaci ya yi da farin cikinsa zai dawo tamkar da, ya na jin Allah ne ya dube shi da idon rahama shiyasa ya ɗauki rayuwar Bassam domin ya dawo masa ita a lokacin da ya gama fidda rai ga samun ta.
Har sai da Daddy ya fahimci farincikin ɗan nasa a bayyane.
Murmushi kawai ya yi ya kashe wayar, a ransa ya na yiwa ɗansa fatar samun nasara a karo na biyu, ya na masa fatar dawowar farincikinsa.
%%©©©©
Tun daga ranar Sameer ya fara shirye-shiryen dawowa Nigeria domin lokaci ya yi da zai dawo mahaifarsa.
Cike da annashuwa yake shirinsa na dawowa, kallo ɗaya za ka masa ka san ya na cikin yanayi mai kyau.
Nan fa Sameer ya haukace da siyayya komai ya gani mai kyau jibgowa Mimiensa da kuma twins ɗinsa yake, ku san duk rabin kayan tsarabar da ya siya nasu ne.
©©©©©©%%%
A wata ranar Litinin da misalin ƙarfe uku na rana jirginsu ya sauka a filin jirgin Abuja.
Cike da nutsuwa ya ke tako step ya na saukowa daga jirgin, ya yin da Saheen da Salim suke ɗan nesa da shi su na kallonsa cike da murnar sake saduwa da ɗan uwan nasu da suka yanke ƙauna da samun hayyacinsa.
A haka ya ƙaraso gunsu suka rungume juna su duka suna murnar haɗuwa.
A mota Sameer sai kalle-kalle ya ke, ya na ganin yanda garin nasu ya sauya, shekara biyar kawai da yayi ya dawo, ya ga sauye-sauye a birnin nasu.
Haƙiƙa Abuja ta cika Babban birni mai kyau da tsari, ko ina gwanin burgewa.
Haka yata kalle-kallensa har suka kusa isa gida, a nan ya kalli Saheen ya na tsokanarsa da cewa "Yaya Saheen baban Boy, ya boy ɗin namu da kuma Mamansa?."
Y'ar dariya Saheen ɗin ya yi,bai ko amsa tambayar ba, ya ce "Kai yaya Sam! Yau kuma ni ne yayan naka?."
Shima Sameer ɗin dariya ya yi ya ce "Eh, ai yanzu kai ne yayana tun da har Ka na da ɗa da mata ni kuma ba ni da, ka ga kenan yanzu ni ne ƙaninka."
Ya ƙarasa zancen ya na ɗan murmushi da alama murmushin na jin ciwo ne.
Dariya suka saka dukkansu, Salim dake zaune a bayan motar ya na sauraren dramar y'an uwansa sai murmushi yake saboda sun burge shi, sai a lokacin ya ce "Ai kar ka wani damu yaya Sam, kai ma kwanan nan za ka angwace, za mu sha shagalin aurenka da Mimienmu."
Da sauri Sameer ya waigo bayan, ya na kallon Salim ya ce "Waya gayama haka?"
"Ni na faɗa domin yanzu haka Mamy ta na can kuma kwanan nan za ta zo maka da ita, ina da tabbacin wannan karon ba za a samu matsala ba insha'allah."