Sashe 12
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ruma da ke tsaye jikin motar ta na bankwana da y'ar uwarta sai hawaye ta ke ta na ɗaga mata hannu.
A haka drivern ya ja su ka bar ƙofar gidan.
Tafiya su ke a nutse, banda sanyin a.cn motar ba abinda ke tashi, Sagir ne ya ke ta damunta da surutu, Daddyn na jinsu sai dariya ya ke masu, anan shima ya sako bakinsa a hirar ta hanyar ƙara tambayarta wasu abubuwa da su ka shafi tarihin rayuwarta., Ita kuwa ta na bashi amsa.
Tafiyar awa uku da rabi ce ta sada su da garin Kano kasancewar motar da su ke ciki lafiyayya ce, sabuwar mota ce dal ƙirar Land cruiser prado.
Ita ce ta ma su kwatancen hanya har su ka ƙarasa unguwarsu, su na zuwa ƙofar gidansu ta cewa driver "Nan ya yi ai mun zo gidan."
Cike da fara'a a fuskarta ta yi zancen.
Cike da mamaki Alhajin ke ƙarewa gidan kallo a ransa ya na mamaki "Ashe akwai mutane da ke rayuwa a irin wannan wajen."
Driver ne ya zagayo cikin sauri ya buɗe ma su motar, ta sauka cikin zumuɗi ta na faɗar "Daddy bari na je na sanar masu mun ƙaraso."
Daga haka ta nufi cikin gidan da gudu, Sagir na ganin haka shima ya bita a baya da gudunsa.
Fitowar mama daga banɗaki kenan, ta na riƙe da buta a hannunta, ta ga yarinya ta shigo gidan da gudu ɗauke da Sallama a bakinta.
Kallon yarinyar ta yi ta ce "Lafiya dai yarinya, biyo ki akayi ne da ki ka faɗo mana gida da gudu haka?"
Dariya sosai ta yi ta ce "Kai mama ki na nufin baki gane Zuhranki ba?"
Sai a lokacin ta ƙare mata kallo tabbas ita ce da sauri ta rungumeta ta na faɗar "Allah sarki Zuhrana ki yi haƙuri banganeki bane, tabbas zaman Abuja ya karɓe ki, kinga yanda ki ka mulmule ki ka yi haske kuwa?, Kin ƙara kyau."
Zame jikinta ta yi ta na faɗar "Allah mamata?"
"Ƙwarai da gaske." Maman ta bata amsa.
Af mama kinga har zan sha'afa, kin san fa tare mu ke da Daddy ya na waje, shine na zo sanar daku, Baban namu yana nan kuwa?."
"Allah sarki! Gashi kuwa babanki ya na gun sana'arsa Kira mun shi a waya na sanar masa, bari na shimfiɗa tabarma je ki shigo da alhajin."
Sai a lokacin su ka lura da Sagir da ke tsaye a bayan Zuhra.
Mama ta ce "Wannan yaron fa?"
Da murmushi shimfiɗe a fuskarta ta ce "Ƙanina ne ɗan autan Daddy." Ta faɗa ta na janyo shi a cikinta.
Kafin ta ƙarasa ƙofar gidan ta kira baba a waya ta sanar masa sun iso.
Kayan aikin da ke hannunsa ya watsar tare da miƙewa ya sanar da yayansa su kula da gurin shi zai je gida yanzu.
®®®®®®®®®®®
A ƙofar gida Zuhra ta same sa har gumi ya fara karyo masa saboda zafin rana, ta ce "Ayyah! Yi haƙuri Daddyna na Barka ka sha zafi koh?, Muje daga ciki."
Ba ta jira amsarsa ba ta juya ya bita a baya, tun shigarsu zauren gidan ya ke ƙarewa gidan kallo, kallo ɗaya za ka yiwa gidan ka gano waɗanda ke rayuwa ajikinsa talakawa ne, filasta ce kawai a bangon gidan ko fenti babu, simintin gidan duk ya tashi ta wasu ɓangarori na gidan.
A haka su ka ƙarasa ciki,yayin da ya ke cike da al'ajabin yadda su ke iya rayuwa acikin wannan gidan.
A kan tabarma ya zauna su na gaisawa da Mama.
"Sannu da zuwa Alhaji, ya hanya? Ya iyali?" Mama ta faɗa cikin sake fuska.
"Alhamdulillah, iyali kuwa su na nan ƙlau."
"Alhaji mungode da ƙoƙari fa, Zuhra ta na ta bamu labarin abubuwan alkhairin da ku ke mata, mun gode, mungode Alhaji."
"Ah! Bakomai wallahi, ai yiwa kaine ita ɗin tamkar y'a ta ke a gurina."
Har mama zata ƙara magana su ka jiyo Sallamar Baba da ya ke shigowa gidan yanzu.
Ƙarasowa ya yi ya na miƙawa Alhaji hannu.
Duk da cewa daga wurin kanikancinsa ya ke, ko wanke hannu bai yi ba ya zo, hakan bai hana Alhaji miƙa masa hannunsa su ka yi musabiha ba.
Nan fa Baba ya zauna aka cigaba da gaisawa, yayin da Zuhra da mama su ka tashi zuwa cikin ɗaki.
Kuɗi mama ta bata N1000 ta ce "Kinga na manta ba a siyo lemo ba, maza kije kantin ɗan liti ki Karɓo masa lemo mai sanyi da ruwan roba."
Karɓa ta yi ta fito tsakar gida, har ta kai ƙofar fita Sagir ya biyo ta da gudu.
Alhajin ya ce "Ai fa yanzu aiki ya same ki Mimie, duk inda za ki sai ya bi ki."
Yar dariya ta yi ta ce "Ai bakomai Daddy autanmu ne fa, dole a masa yanda ya ke so." Ta na gama faɗa ta sunkuce shi su ka bar gidan."
Mama kuwa kitchen ta koma ta harhaɗa sauran abubuwan da su ka rage ta kawo ɗaki ta ajiye ta na jiran dawowar Zuhra.
Bayan ta dawo ne Mama ta fito da abincin da aka shirya saboda shi kawai a tiren silver babba, cikin wasu kuloli ma su damar kyau da ta aro a maƙwafta kasancewar ita bata da su, a ɗakin Zuhran ta dire kayan.
Baba ya ja shi zuwa cikin ɗakin domin ya ci abinci.
Ba laifi sun yi ƙoƙari sosai gurin karrama baƙon na su domin a abincinsa harda kaza biyu a ciki.
Su na cikin cin abincin ne wayar Alhaji ta hau ƙara.
Ɗagawa ya yi tare da faɗar "Assalamu alaikum."
Jim ya ɗan yi alamar ana magana a ɗaya bangaren, can ya ce "To madallah, kayan sun haɗu kenan?
Nan ma ya ɗan yi shiru can ajima ya ce "Shikenan Kabir yanzu zan turo maka da address ɗin sai ka aiko mun da kayan, ba na son ɓata lokaci fa kasani."
Daga haka ya kashe wayar,ya cigaba da cin abincinsa don ba laifi abincin ya yi daɗi sosai, dama Mama gwana ce a ɓangaren girki.
Su na gama cin abincin su ka wuce masallaci don gabatar da sallar Azahar.
Bayan dawowar su daga masallaci ne saƙon Alhaji ya iso.
Dawowarsa kenan daga gun abokanansa dai-dai kan layinsu ya ga wata babbar mota cike da kaya ta na tafiya a hankali da alama su na neman wani guri ne, cigaba da tafiyarsa ya yi har ya zo ƙofar gidansu ya shige abinsa.
A dai-dai lokacin ne kuma Alhaji ya gama waya da Kabir ya sanar mai kaya sun iso kwatancensa sai dai ba a gane gidan ba.
Ƙarasawa yaron ya yi ya gaida mahaifinsa da baƙonsu har ya miƙe baba ya Kira sunansa "Ma'aruf!"
"Na'am baba."
Juyawa ga alhajin Baba ya yi ya ce "Alhaji ka kwatanta masa mutanen sai ya je ya zo da su."
Kallon Ma'aruf Daddy ya yi ya ce "Za ka ga wa su mutane a wata babbar mota mai cike da kaya su za ka...."
Ai tun bai gama rufe bakinsa ba ya ce "Wata ƙatuwar mota wacce ta ke cike da kayan abinci koh?"
Da mamaki a fuskar Daddy ya ce "Eh ita, ko ka gansu ne?"
"Na haɗu da su a farkon layi su na tafiya a hankali, bari na je kafin su kai kayan wani guri mu shiga uku."
Ya faɗa cikin yarinta da rashin wayo, ya fice da gudu.
Jim kaɗan sai ga su sun ƙaraso tare, aka fara sauke kayan abincin.
Alhaji da Baba ne su ka fito ƙofar gida baba ya tara yara aka fara shiga da kayan ciki sai godiya ya ke ta yi Wa Alhaji, harda hawayen farin ciki.
Tun da ya ke a rayuwa bai taɓa tunanin zai ajiye irin wannan kayan abincin a gidansa lokaci ɗaya ba.
A kwai wani ɗaki a gidan wanda ke jikin kitchen da basa amfani dashi, sai tarkace ne kawai a ciki a ciki a ka saka kayan abincin.
Da la'asar Daddy ya hau Motarsa ya ma su sallama za shi ya kama ɗaki a hotel inda zai kwana.
Nan ma Sagir ya ƙi ya bi Daddy ya laƙewa Zuhra, bisa ga dole Alhaji ya haƙura ya tafi.
®®®®®®®®®®®
Y'an uwa da abokanan arziƙi ne su ka cika gidan su Zuhra a na ta yi mata sannu da zuwa.....
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masu ƙarin bayani.
Follow me on Wattpad @Ummu inteesar.
UMMU INTEESAR CE❤️💙💚💛💔💙
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN NAIRA 200 KACAL.
GA MAI BUƘATA SAI YA TURA KUƊIN TA WANNAN ACCOUNT ƊIN:
Accnt name: Rukayya Ibrahim lawal
Accnt no:0431343346
Gt bank.
Ko a tura katin Mtn ta wannan number
08109634202
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO A SANADIN KAMA DA ƘURUCIYAR SAPNAH TO ₦300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU ₦200
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Last Free Page 2️⃣9️⃣↪️3️⃣0️⃣
Haka ma yaya farida da matar yaya Kabir duk sun zo sai murna ake.
Washe garin ranar da su ka zo da misalin ƙarfe sha biyu na rana Daddy ya zo gidansu Zuhra domin su tafi banki a buɗe mata account dama ya sanar da ita ta shirya kuma ta nemi ɗan rakiya.
Saboda haka ko da ya zo ta gama shiryawa dama tuni yaya Kabir ya zo, zuwan Daddy kawai su ke jira, don haka koda ya zo mota kawai su ka hau suka wuce Gt bank.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama komai take anan Daddy ya yi mata transfer kuɗi dubu ɗari zuwa account ɗinta, su ka juyo gida.
Jin kanta ta ke yi kamar tafi kowa ce yarinya Sa'a a rayuwa, wannan kuɗin da ya tura mata jin su ta ke tamkar miliyan goma sai ta ke ji yanzu ita da iyayenta sun samu waraka daga talauci.
A kwana biyun da su ka yi Sagir ya shaƙu sosai da Zuhra da kuma ɗan uwanta Ma'aruf, saboda yanda su ke kula da shi da tarairayarsa tamkar ƙwai.