← Book details A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 36

Sashe 13

A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana biyu Daddy ya yi a garin Kano sannan ya yi shirin komawa.

A ranar da zai tafi ya tara iyaye da y'an uwan Zuhra domin neman wata alfarma a gunsu.

®®®®®®®®®®®

Ga baki ɗayan su zaune su ke akan wata ƙatuwar tabarma a tsakar gidan, kowa ya hallara in ka ɗauke Ma'aruf da ya janye Sagir ƙarami su ka fita zuwa wajen abokanansa.

Anan Daddy ya dubi Kabir ya ce "To yaya babba sai ka buɗe mana taron da addu'a."

Ba musu Kabir ya yi addu'ar aka shafa, sannan Daddy ya fara jawabi kamar haka " Da farko dai abinda ya sa na nemi mu taru anan shine, ina neman Alfarma guda biyu a wajenku, duk da na san ta farkon za ta yi matuƙar wuya amma zan roƙa."

Ɗan dakatawa ya yi da zancen ya na kallonsu,
Ganin duk sun zura mashi ido Alamar shi su ke saurare ya saka shi nisawa sannan ya ɗora da cewa "Alfarma ta farko shine ina so ku bar mun Mimie ta dawo hannuna domin ta maye mun gurbin Real Mimieta, na yi ma ku alƙawarin zan riƙe ta da amana, idan hakan bai samu ba to ina roƙon ku da ku ba mu damar zama iyayenta na biyu ta yadda za mu dinga sanin duk wani abu da ya shafi rayuwarta, in ya so duk aka yi hutu sai ta je mana, wannan abun zai sanya iyalina cikin tsantsan farin ciki."

Tun da ya fara magana ba wanda ya ce ƙala, jin Alfarmar da ya nema ya sanya jikin Baba ya yi sanyi domin har ga Allah ya san ba zai iya barin Zuhra ta koma hannun wa su ba, domin da ya na buƙatar hakan da ba wanda yafi cancanta a baiwa riƙonta sai ƙanwar mahaifiyarta, tun da kuwa ya hana ta tabbas ba ya jin zai iya bawa Alhaji duk da ya na matuƙar jin nauyinsa.

Ganin kowa ya yi shiru kuma ga Baba da alama ya zurfafa a tunani ya sanya Daddy ya ce "Ka kwantar da hankalinka malam Habu, idan ba zai yiwu ba ni na haƙora ka da ka ji kunyar faɗamin gaskiya."

Dogon numfashi Baba ya ja ya sauke sannan ya ce "Ka yi haƙuri Alhaji ba wai ban yarda da kai ba ne ko kuma ba na son baka Zuhra ba ne a'a, dalilin da ya sa ba zan yi hakan ba shi ne kafin ka nemi wannan Alfarmar, ƙanwar Mahaifiyarta Khadeeja da ke Abuja ta nema ban yi mata ba, ka ga yanzu idan ta samu labarin na ba ka Zuhra tabbas ba za ta ji daɗi ba, don Allah Alhaji ka yi haƙuri, ka da ka ga kamar na maka butulci."

Haƙiƙa Daddy ya ji zafin hanashin da aka yi sosai, amma ya masa uzuri domin ya san yanda zafin rabuwa da ɗa ya ke.

Murmushin yaƙe ya yi ya ce "Kar ka ji komai Malam Habu, sai alfarma ta biyu da na ke nema ina fatar zan samu."

"Insha'allah Alhaji." Ya amsa.

Gyara zamansa ya yi sannan ya ce "Alfarma ta biyu kuwa ita ce daga yau ina so ku dinga kiran Zuhra da Mimie domin ina so ta maye min gurbin y'ata Mimie."

Cikin hanzari Mama ta ce "Ah! Wannan ai ba damuwa tun yanzun ma za mu fara faɗa."

Anan Daddy ya yi godiya sosai sannan ya sanar da su cewa ya na so ya haɗa auren Sameer da Mimie domin ƙarfafa zumunci.

A razane Zuhra ta ɗago ta kalli Daddyn su na haɗa ido ta kuma sunne kai ƙasa.

Iyayenta ma da yayyenta haka su ka ji maganar a bazata.

Lura da yanayinta yasa Daddy ya ce "Ki kwantar da hankalinki y'ata, shine ya sanar da ni ya na sonki, amma duk da haka ba zan takuraki ba, ba tursasawa idan kin gama shawara ma yi magana daga baya."

Daga haka ya tashi ya ma su sallama zai tafi, a dai-dai lokacin ne kuma Ma'aruf ya dawo gidan tare da Sagir.

Nan fa kallo ya koma sama domin Sagir saka rigima ya yi shi ba inda za shi, zai zauna da Sisternsa anan, aka yi-aka yi fafur ya ƙi, sai da Daddy ya kira Mamy a waya ya gayamata tare da bawa Sagir wayar.

Komai ta gaya masa oho, sai ga shi ya amince zai bi Daddy su koma gida.

Anan ya masu Sallama Dukansu su ka ɗunguma zuwa kofar gida don su ma sa rakiya.

Motarsa ya hau driver ya ja zuwa abuja, a ransa ya na da ƙudurin canza ma su gida, amma so ya ke sai komai ya dai-daita tukunna.

Tun daga ranar aka fara kiran Zuhra da Mimie kowa haka ya ke kiranta, domin a ɗabbaƙa Alfarmar da aka yiwa Daddy.

Bayan tafiyar Daddy Zuhra ta shirya zuwa gidansu Raliya domin ta kai mata kayan arziƙin da su ka samu a matsayin tsaraba.

Raliya ƙawarta ce tun a primary ajinsu ɗaya kuma kujera ɗaya har yanzu su na tare kuma aji ɗaya duk da cewa Raliyan ta girme ta amma sun shaƙu sosai.

Ta na matuƙar tausayawa rayuwar ƙawartata, kasancewar mahaifiyarsu ta rasu shekara uku da su ka wuce, kuma mahaifinsu mai ƙaramin ƙarfi ne kamar babansu, ga shi har zuwa lokacin bai ƙara aure ba, sai su kaɗai a gida, yayarta ɗaya ƙannenta huɗu duk ita da yayarta ke kula da su.

Sai da ta ɗibar mata komai na kayan abincin kama daga kan shinkafar har kayan maggin sannan ta nufi gidansu.

®®®®®®®®®®®®®
Bayan wata Ɗaya
Zaune ta ke a tsakar gida akan ƙaramar kujerar katako ta na wanke-wanke.

A zahiri wanke-wanken ta ke amma kallo ɗaya za ka mata ka fahimci cewa hankalinta ba ya gun, ta yi nisa acikin tunanin wannan sabon al'amari da ya tunkaro rayuwarta, mafita kawai ta ke nema.

Ta na nan a haka bata ankara ba sai ji ta yi an dafa kafaɗarta, ta juyo aɗan razane sai ta ga ashe ƙawarta ce.

Da mamaki a fuskarta ta ke kallon tasleem tare da cewa "Tasleem! Yaushe ki ka zo ne? Ban fa ji shigowarki ba."

Tasleem ta ce "Dama yaushe za ki ji shigowa ta? Tun da ki na nan ki na wannan sababben tunanin na ki, ni na rasa meke damunki ne, Soyayya hauka ce, da za ki mayar da kan ki haka?, Ke kenan kullum tunani.?"

Ɗan murmushi ta yi bata ce komai ba, Tasleem ta cigaba da cewa "Na san dai ki na tunanin Rayuwarki ne wato Bassam, Wai ni kam ƙawata wane irin so ne ki ke yiwa Bassam haka?" Ta tambaya tare da janyo wata kujerar da ke kusa da ita ta zauna kusa da Mimien.

Sai da ta ɗauraye kular da ke hannunta ta kife a cikin kwando kafin ta yi murmushi ta ce "Ba za ki gane ba ne ƙawata, ina son Bassam fiye da komai a rayuwata, ni kaina ba zan iya kwatanta iya adadin son da na ke yi masa ba, Abun da nasani shine duk duniya ba wani fa namijin da na ke so sama da shi, duk da cewa ba shi ne na farko da ya furta min kalmar so ba, Amma akansa na fara soyayya, kuma ba wanda na kamu da tsananin sonsa har na amincewa zuciyata ba zan iya rayuwa idan ba shi ba sai Bassam."

Murmushi sosai Tasleem ta yi ta ce "To ƙawata Allah ya bar ƙauna ya sa shine abokin Rayuwarki na har abada."

Miƙewa ta yi adai-dai lokacin da ta kammala aikin da ta ke tare da ɗauke kwandon ta na washe baki ta ce "Ameen ƙawata Allah ya bar mun ke."

"Ba zai bar ni ba wallahi sai na mutu." Ta faɗa

Ƙyalƙyalewa da dariya ta yi ba ta ce komai ba.

Miƙewa tsaye Tasleem ta yi tare da Faɗar "ke ba fa zama na zo yi ba, dama zan je gidan yaya Khalil ne, shine na ce bari na biyo mugaisa,kin san tun dawowar ki daga Abuja ban samu shigowa ba saboda muna exam ne, amma zan samu dama na yi miki zuwa na mussanman."

"Nagode sosai ƙawata sai kin zo, mu je na taka mi ki koh?." Ta faɗa.

"No da kin barshi tare muke da direba." Tasleem ɗin ta faɗa.

Duk da haka ba ta hak'ura ba sai da ta raka ta har k'ofar gida.

Mimie ta ce "Nagode sosai ƙawata a sauka lafiya, Allah ya kiyaye hanya."

Ameen ta ce tare da shigewa cikin motar direba ya ja su ka bar ƙofar gidan.

®®®®®®®®®®®

Juyawa ta yi ta koma cikin gidan ta cigaba da Aikace-aikacen ta dama Mama ba ta nan ta fita saboda haka ba kowa a gidan sai ita kaɗai tsintsiya ta ɗauka ta share tsakar gidan gaba ɗaya da ya ke gidan ba wani mai girma ba ne sosai cikin mintuna ƙalilan ta kammala Sharar.

Ruwa ta ɗiba a bokiti ta nufi banɗaki ta yi wanka, tana fitowa ta ɗora Alwala kasancewar lokacin Sallar Azahar ya yi.

Ɗakinta ta shige ta saka kaya tare da zura dogon hijabinta ta shimfiɗa Sallaya ta tada Sallah.

Sallamewar ta keda wuya ta ji ƙarar wayarta ƙirar iphone 6+ da ke gefe ɗaya a kusa da ita.

Da sauri ta ɗauki wayar don ta riga ta san mai kiran ko bata duba ba, Bassam ne ke kira.

Murmushi ne ya bayyana a fuskarta yayin da ta ke ɗaga kiran, Wayar ta kai saitin kunnenta tare da yin Sallama.

A ɗaya bangaren Bassam ne ya Amsa Sallamar cikin zazzaƙar muryarsa mai kama da sautin kanari.

Faɗaɗa murmushinta ta yi su ka gaisa sosai daga nan kuma su ka fara kashewa juna zuciya da tausasan kalamai masu ratsa zuciya sai da su ka shafe kusan minti Arba'in su na wayar kafin su ka yi Sallama da juna su ka datse kiran.

Dogon numfashi ta ja, haɗe da faɗawa akan ƙaramar katifarta ta tsunduma kogin tunani "Oh! Allah ga Mimie, Allah ka dube ni da idon rahama." Ta faɗa a bayyane.
Chapter 13 · 0% Book details