Sashe 14
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bakomai ne yasa ta faɗin haka ba sai dan tunawa da ta yi cewa Daddy Ya na so ya haɗa ta aure da babban ɗansa wato Sameer, kuma ba za ta iya tozarta Daddy ba, ba ma yadda za'ayi ta ƙi jininsa Tun da ya so ta ya nuna mata gata ya ɗauke ta tamkar y'ar cikinsa (Real mimie) da ya haifa, ita kam ta na jin kamar ta karɓi zaɓin sabon Abbanta da ya nuna mata gata fiye da kowa a duniya, to amma ya za ta yi da zaɓinta babban masoyinta a duniya? Dole ne dai ɗaya za ta aura acikinsu ko dai Sameer ko Bassam.
Ta na kai nan a tunaninta ta kuma jan dogon numfashi tare da dafe kanta da Tafin hannunta ta na faɗar "Oh! Ni Mimie ina mafita?, Allah ka fitar da ni daga wannan matsalar."
Mirginawa ta yi akan katifar ta na cigaba da cewa "Amma fa ya kamata na yi tunani sosai tsakanin masoyan nan nawa guda biyu, waya kamata na aura ne?"
Ajiyar zuciya ta yi kana ta ci gaba da tunaninta.
Sameer dai ɗan Alhj ne kuma ko da bai faɗa ba ta san shine zaɓinsa tun da ba zai ƙi ɗansa ba, amma fa ya gaya mata ba tursasawa idan dai har bata son Sameer ka da ta ji kunyar gaya masa don ta na ganin cewa Sameer ɗansa ne, ai itama y'ar tasa ce da ya ke ji da ita wacce ta ke a matsayin Mimiensa y'a ɗaya tilo da ya ke da kuma ya ke ji da ita tamkar Rayuwarsa, sai ga shi mutuwa ta masa yankan ƙauna.
Ya yi baƙin cikin matuƙa a lokacin mutuwarta, amma yanzun da ya sami wace take a madadinta sai ya ji baƙin cikinsa ya gushe to me zai saka ya tursasa Mimiensa?
Ya gaya mata cewa idan da wanda ta ke so ta sanar da shi, shi zai shige mata gaba ayi komai na auren.
Sai dai ita fa ta na matuƙar jin kunyar Alh Salman, ta ya za ta buɗi baki ta ce ba ta son ɗan cikinsa? Inah! Ba zai yiwu ba.
A zahirin gaskiya kallon yaya ta ke masa ba masoyi ba ba zata iya aurarsa ta bar Bassam ba, idan ta yi haka tamkar ta yaudari masoyinta Bassam ne.
Duk da cewa iyayenta suna ƙarfafa mata gwuiwa ta auri Sameer domin ƙin aurensa kamar butulcewa Alhaji ne, amma inah! Sam ita ba za ta iya ba ko alama...
Ta na ganin daurewa kawai za ta yi ta fuskanci Daddy ta sanar da shi gaskiyar lamari cewa.......
🤔🤔tirƙashi!
Idan baku manta ba a farkon labarin kunga Mimie a gidan Bassam ana gallaza mata.
Tambayar anan ita ce: Shin ina yawan ƙaunar da ya ke mata ta tafi?
Me yasa ya juya mata baya?
Ina kuma labarin Sameer?
Tayaya ta auri Bassam ta bar zaɓin iyayenta?
Domin jin cigaban wannan ƙaryata cen labarin sai ku biya kuɗin ku 200 ba yawa.
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa ƙarin bayanin yanda zai biya kuɗin.
Ka da ku manta wannan shine last free Page duk mai buƙatar jin cigaban wannan labarin sai ya biya kuɗin da ₦200 kacal ba yawa, a tura katin ta number da ke sama.
Follow me on wattpad @ummu inteesar.
Vote, share& Comment
UMMU INTEESAR CE💚💙💛💙
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH
Y'AR GANTALI
RIKICIN MASOYA
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL.
GA MAI BUƘATA YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER
08109634202
KA DA KU MANTA WANNAN PAGE ƊIN NA WANDA SU KA BIYA NE SU KAƊAI, IDAN KA SAN BAKA BIYA BA KADA KA KARANTAMUN DOMIN HAƘƘI NA NE, IDAN MA KA BIYA KUƊIN KADA KA FITARMIN DA LITTAFI DOMIN KUƊIN KARATU KA BIYA BA MALLAKA NA BAKA BA.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 3️⃣1️⃣↪️3️⃣2️⃣
Cewa ita fa gaskiya Bassam ta ke so shine cikar burinta kuma farin cikinta.
A haka ta wanzu ta na ta tunanin mafita har bata san ta shafe tsawon lokaci haka ba, sai da ta ji kiran sallar la'asar.
Miƙewa ta yi ta tada Sallah dama da arwallarta, a haka Mama ta dawo ta same ta.
®®®®®®®®®®®
A haka rayuwa ta cigaba da gudana ko yaushe Mimie na cikin zullumi da tunanin mafita don gudun kada a rabata da masoyinta..
Dama tuni an koma hutu don haka ta cigaba da zuwa makarantar ta kamar lokutan baya sai dai yanzu rayuwarta ta samu sauyi ba kamar da ba, domin yanzu su na da wadataccen abinci da suturu masu kyau sakamakon shigowar Alhaji Salman cikin rayuwarsu.
®®®®®®®®®®
A bangaren Mommy kuwa ta gama cika fam! Fashewa kawai ya rage ta yi, domin yanzu wata tsanar Mama da ƴaƴanta ta ke ji, domin a ganinta su suka hanata damar cika burinta na shiga cikin daular dukiyar Alhaji Salman.
Bayan tafiyar Mimie Mommy bata kira su ta ji ya su ka sauka ba, duk ta watsar da su saboda hassada, yanzu babban target ɗinta shine ya za'a yi ta aurar da y'arta Ruma a gidan Alhaji Salman?, Domin a gaskiya ba zata iya ƙyale wannan daular ta wuce ta na ji ta na gani ba, saboda haka akai-akai takan kira Mamy su gaisa a waya, shima Alhajin haka wani lokaci ma har su mata kyautar kuɗi, domin su nuna musu ta ke duk duniya ba wanda yafi ta son Mimie.
®®®®®®®®®®®
Alhaji Salman kuwa ya na matuƙar son ya ga aure ya ƙullu tsakanin Mimie da Sameer domin ta dawo cikin iyalansa kamar baya, amma ba ya son ya takura ta, hakan ya saka ya yi gum da bakinsa ya ƙara bata dama daga nan zuwa lokacin da za ta yi candy.
Mamy da ta ji zancen soyayyar da Sameer ke yiwa Mimie ba ƙaramin daɗi ta ji ba, don haka a kullum ta kai goshinta ƙasa sai ta roƙi Sarkin talikai da ya ƙaddara wannan aure na yaranta.
®®®®®®®®®®®
Zancen soyayya tsakanin Mimie da Uncle Bassam ɗinta kuwa sai ma abinda ya ƙaro, ya na tarairayarta gami da bata kulawa baya son damuwarta ko kaɗan.
Wata rana da dare Mimie na kwance akan katifarta (sabuwa da ta siya da kuɗin da Daddy ya tura mata)
Kawai sai wayarta ta hau ruri, acikin magagin barci ta lalubo wayar ta katse kiran tare da koma kwanciya, domin ta tsani abinda zai katse mata barci mai daɗi irin wannan.
Wayar ce ta kuma ruri a karo na biyu a ɗan fusace ta ɗaga wayar ta ɗora a kunnanta bata ce komai ba, still idonta na rufe.
Daga can ɓangaren Sameer ne ya ce "Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu, da fatar ban katsewa sweet sis daddaɗan barcinta ba."
Zumɓur ta yi ta tashi zaune ta na waro ido a ranta ta ce "Yaya Sameer?"
"Meyasa zai kirani kuma a wannan lokacin?." Mamaki ta ke sosai, domin wannan ne karo na farko da su ka fara magana a waya.
A daƙile ta amsa mai da cewa "Wa'alaikamus Salam, Yaya Barka da dare."
"Yawwa Barka dai, kin fara barci ne?"
"Eh." Ta basa amsa a taƙaice.
Ya ce "Ayyah! Sorry sweet sis, na katse maki barci amma ki yi haƙuri a bar ƙaunata zuciyata ce ta azalzalamun akan son jin muryarki har ta saka na manta cewar yanzu dare ne, mai yiwuwa kuma Sweety barci ta ke."
Kalamansa sun bata mamaki duk da cewa bai kamata ta yi mamakin ba domin ya riga ya sanar da ita cewa ya na sonta.
Mamaki da fargaba ne ya hanata maida masa da amsa.
Shi kuwa jin shirun ya yi yawa ya saka ya kashe wayarsa domin a zatonsa ko barcin ne ya wuce da ita tunda dama ta fara.
Murmushi ne kwance a fuskarsa yayin da ya katse wayar, ko ba komai dai ya yi farin ciki tunda ya ji muryarta kuma ya tabbatar ta na lafiya, a bayyane ya ce "Allah ka mallaka mun zuciyar wannan yarinyar, Allah ka bani ita a matsayin uwar ƴaƴana, ameen."
Ita kuwa bayan katse wayarsa barci ne ya ƙauracewa idonta ta rasa ma tunanin me za ta yi, tabbas ta na cikin sarƙaƙiya, ƙwaƙwalwarta na dab da tsayawa cak akan tunanin mafita, to ita yanzun wa za ta aurah, Sameer ko Bassam?
Dogon numfashi ta ja tare da mirginawa ta sauka daga kan katifar ta je ta ɗoro Alwala ta tada Sallar nafila ta na roƙon Allah da ya kawo mata mafita acikin wannan lamarin (dama Mimie yarinya ce mai ibada sosai, wannan na daga cikin ɗabi'unta duk lokacin da wata matsala ta tunkaro ta, tana mayar da dukkan lamuranta ga Allah ta hanyar yin nafilfili da riƙon Allah domin ya kawo mata mafita)
A kullum iyayenta su na ƙara ƙarfafa mata gwuiwa da bata shawara akan ta auri Sameer ko don halaccin da iyayensa su ka mata, amma har zuwa yanzu bata jin za ta iya barin Bassam domin a ganinta ba zata taɓa jin daɗin rayuwa in ba shi ba.
®®®®®®®®®®®
Bayan shekara ɗaya da rabi, abubuwa da yawa sun faru a ciki kuwa harda sabon gidan da Alhaji ya siya ma Baba a unguwar geza, gidan bene ne babba, dai-dai wanda zai ishesa yin rayuwa da iyalansa cikin farin ciki, wancan gidan na Tukuntawa Baba ya saka yan haya aciki, yanzu kam alhamdulillah komai ya wadata agaresu.
Yan uwan baba da su ka guje shi saboda talauci da ya ke fama dashi, yanzu duk sun laɓaɓo sun bashi haƙuri su na neman yafiya a gareshi na gudunsa da su ka yi abaya don suna ganin sun fi shi arziƙi(Rayuwa kenan, dama duk lokacin da baka da shi to kai ba kowa bane, yan uwanka ma gudunka su ke amma daga lokacin da ƙofofin arziki suka fara buɗe ma kuma sai ka dawo kaine abun girmamawarsu.)