← Book details A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 27

Sashe 8

A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

“Ahmadu ina tunanin wannan ita ce yarinyar da kuke qorafin kun tarar da ita a gidan Modibbo?” Ardo ya jefa wannan tambayar ga mahaifin Yasmin.
“Qwarai ita ce Ardo, don ba zan manta da fuskarta da irin cin mutuncin da ta yi min ni da iyalina ba.” Mahaifin Yasmin ya amsa wa mahaifinshi cikin muryar dake bayyana bacin ranshi da irin abinda ya shiga tsakanin Aisha da su.
“Ai kuwa ya zama dole ka manta da wani batanci da ya tava shiga tsakaninka da ita Ahmadu, domin wannan yarinyar da kake gani ‘ya ce ga Aishatu qanwarka, kuma wannan taro da ka zo kai da iyalinka ku ka tarar za a yi ba na komai ba ne sai na gabatar da ita a matsayin daya daga cikin jikokin wannan zuri’a tamu. Yadda Yasmin take a gurina haka Aishatu take a gurina. Don haka daga yau ka fara yi mata kallon ‘yarka kamar yadda kake yi wa Yasmin kallon diyarka ta cikinka.”
“Amma Ardo...”Ardo
sai kuma ya yi shiru ya rasa abin cewa domin dai ya san Ardon idan ya ce
“Eh”
To e din yake nufi har abada.
“Umarnina ne bai samu kar6uwa a gurinka ba ko kuma jayayya za ka yi da ni Ahmadu?”
“Ba haka ba ne Ardo, umarninka abin bi ne a gare mu ni da iyalina, domin duk a qarqarshin ikonka muke. Allah ya huci zuciyarka.”
Da saurinshi ya yi togaciya da fadin haka. Sannan ya juyo gare ta yana murmushin da kallo daya ta yi masa ta san bai kai ciki ba ya ce
“Muna miki maraba da zamo wa daya daga cikin zuri’armu. Da fatan za ki manta da abin da ya taba shiga tsakaninmu na batanci? kamar yadda muka manta har abada ni da iyalina”
Murmushi ne ya wadaci fuskarta duk da tana tabbacin maganar da ya yi iya le66anshi ta tsaya, sanin da ta yi ba shi da wuta ba shi da aljanna, bai isa ya cutar da ita ba sai abinda Allah ya qaddara zai faru a kanta
“Na gode. Ina fatan za ku manta da mayar muku da maganar da na yi a haduwarmu ta farko?”
“Kar ki damu Aishatu, duk dan Adam ajizi ne, kuma rashin sani shi ya sa duk muka aikata wannan kuskure. In Allah ya yarda hakan ba zai sake faruwa a tsakaninmu ba.”
Mummy ce ta fadi hakan tana murmushi.
“Yasmin ba ki gaisa da ‘yar’uwarki ba, ko har yanzu kina riqe da 6atancin da ya ta6a shiga tsakaninku a zuciyarki ne?”
Ardo ne yai wannan tambayar ga Yasmin bayan ya lura kowa ya maida magana ita ce kawai ta yi shiru, kuma har a wannan lokacin ba ta saki fuskarta ba.Kafin ta furta komai sai da ta taso daga inda take zaune ta dawo kusa da Aisha, sa’annan ta miqa mata hannu suka yi sallama a tsakaninsu (musabiha), irin kallon da take wa Aisha mai hade da murmushi kallo ne mai isar da ssalon
“za ki gani in dai ni ce”.
Aisha ba ta yi qasa a gwiwa ba gurin mai da mata da martanin kallon mai isar da saqon
“In ga alkhairi, ta Allah ba taki ba.”
Ba tare da ta matsa daga kusa da Aisha ba ta dubi Ardo ta ce
“Ba haka ba ne Ardo, wa ce ni in qi bin umarnin tsohon mijina matuqar ina son aljanna? Kawai dai mamaki ne ya kama ni da wata matsananciyar kunya, ashe akwai dangantaka mai qarfi a tsakaninmu da Aiaha, amma rashin sani ya sa duk mun yi wa juna mummunar fahimta. In Allah ya yarda wani abu makamancin wanda ya shiga tsakaninmu a baya ba zai sake faruwa a gaba ba. Zan riqe ta qanwa ta jini kamar yadda nake riqe da sauran qannena na wannan zuri’ar.”
Gaba dayansu sunji dad'in abinda ta fad'a, ita ma Aisha fuskarta yalwace da fara’a duk da ta fahimci inda maganganun nata suka dosa.
“Alhamdulillahi!
Dama haka ake son duk musulmi na qwarai ya kasance mai yafiya ga dan’uwanshi musulmi. Sai Allah ya yafe mana kura-kuran da muka aikata tsakaninmu da shi. Yasmin ki jagoranci ‘yar’uwarki Aisha zuwa cikin gida inda za a gudanar da taro kamar yadda muka saba. Ahmadu kana iya shiga cikin gida kai da iyalinka kafin sauran ‘yan’uwa su gama had'uwa.”
Har qasa dukkansu suka duqa suka yi godiya ga Ardon, sannan suka yi masa sallama suka nufi cikin gidan kamar yadda ya ba su umarni.

Suna zaune cikin dakin taron, a lokacin jama’a ba su gama haduwa ba, amma mafi yawancin dangin sun hallara, idanu sun yi yawa a kan Aisha, don haka ta takure a kusa da Mummynta, hannunta na dama yana cikin na ta, tana matsawa a hankali.
Mummyn Yasmin ce ta kasa haquri sai da ta jefa wa Mummyn Aisha magana cikin shagu6e,
“Aishatu ashe kin ta6a haihuwa ba mu da labari?”
Da yake Mummy mace ce mai gaskiya da rashin barin ko ta kwana take ta ba ta amsa kai tsaye ta ce,
“Qwarai kuwa ga zahiri! tunda kin gan ni da ‘ya?”
Dariya ta yi cikin kunya da son basarwa ta ce
“Allah ya ba ki haquri, daga tambaya sai cibi ya zama qari?”
Ita ma Mummyn Aisha dariya ta yi, sannan ta ce “Wannan salon hausar ke kika santa Aunty Maryam, abinda na sani kawai shi ne kin yi tambaya kuma na ba ki amsa.”
Babu wanda ya sake tankawa a tsakaninsu, sai ‘yanmatan daga cikin dangin ne suka fara magana cikin mamaki suna fadin
“Laaaa! Aunty wannan kyakkyawar dama diyarki ce? Ya sunanta?”
Da fara’arta a fuska ta amsa musu da cewa
“Sunanta Aisha, kuma ‘yata ce duniya da lahira. Duk mai neman qarin bayani ko kuma tambaya a kanta ya jira shigowar Ardo.”
Da wannan maganar ta rufe bakin duk mai niyyar yin magana a kan Aisha.
Chapter 8 · 0% Book details