Sashe 2
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ni dai ka daina cewa soyayyata zai kashe ka Modibbo, ko kana son in yi kuka ne?” ta tambaye shi cikin salon shagwa6a bayan ta fahimci ciwon nashi na so ne.
“A’a Babyna, don Allah kar ki yi kuka.”
Ya amsa da hanzari don babu abinda ya tsana a rayuwarshi irin kukan Aisha.
“Ka ci abinci kuwa yau?”
Ta tambaye shi bayan jikinta ya ba ta sam bai ci abinci ba.
“Ban ci abinci ba Babyna, rabona da abinci tun jiya da rana...”
“Kana son yunwa ta illata min kai ne Modibbo? Ni ma ba zan sake ci ba, ka ga sai yunwar ta illata mu tare...”
Ta fada cikin damuwa sannan ta sanya mishi kuka, amma na shagwaba, wanda babu ko digon hawaye a cikinsa.
“Oh my God! I’m sorry my wife.”
Ya fada cikin yanayin damuwa. Sannan ya fara rarrashin ta cikin tattausar murya tare da daukar mata alqawarin yanzun nan zai yi wanka ya fita zuwa gidan abinci don raya qundunsa.
“To, ni dai daga yanzu kada ka sake zama da yunwa...” Ta fada bayan ta tsaida kukan. Magana take tana tura baki kamar yana kallon ta.
“Na daina matata, amma sai idan kin yi min alqawarin ba za ki sake qin daukar wayata ba, ko kina so in bar aikina in dawo kusa da ke in zauna ne?”
“A’a!” ta amsa da sauri, duk da tana son ta ringa ganin shi a kusa da ita a kowane lokaci, amma tana son ya maida hankali a kan aikinshi da bincike a kan wadanda suka kashe ‘yar’uwarta Sadiya.
“Idan na kira ba ki dauka ba wallahi ciwo nake ji a zuciyata, don Allah matata ki daina wahalar da ni ta hanyar rashin jin sassanyar muryarki kin ji?”
Ya roqe ta da salon magana irin ta qaramin yaron da bai da qarfi ko dabara sai abinda mahaifiyarshi ta sanar da shi.
“To na ji, kuma na daina mijina. Daga yau ba zan sake qin daukar wayarka ba, matuqar ina kusa da wayar, kuma ban yi barci ba. Ka yi haquri da qona zuciyarka da na yi ta hanyar rashin jin muryata ka ji mijina?”
Ta amsa da irin salon muryar da ya yi amfani da ita wurin isar da rokon shi.
“Yauwa matata, shi ya sa a kowane daqiqa na agogo son ki qara ninkawa yake a zuciyata. Ai ke ba kya laifi a gurin mijinki, kuma har abada ba na tunanin za ki yi min laifin da zai sa in yi fushi da ke. Idan ma za ki yi ko da zuwa gaba ne na yafe miki, duniya da lahira.”
Ya fadi hakan cikin nishadi. A muryarshi ta fahimci abinda yake fada har a zuciyarshi iya gaskiyar kenan!
“Na gode mijina! Shi ya sa nake tsananin son ka! Allah ya bar min kai mijina.”
“Zuciyata domin ke aka halicce ta matata, ba na tunanin a duniya za a sami namijin da yake yi wa masoyiyarsa ko da kwatankwacin son da nake yi miki ne. wallahi ina tsananin son ki har ban san yadda zan kwatanta miki rin tsananon son da nake miki ki fahimce ni ba matata. Da zan iya bude zuciyata in nuna miki irin son da nake miki da na yi hakan matata.... ina sonki Aisha, wallahi ina tsananin sonki. zan iya bada rayuwata don in ceci taki rayuwar Aisha... ina sonki, don Allah kiyi haquri dani ki soni ko da kashi daya bisa dari na irin son da nake miki ne matata...”
Ya qarasa maganar yana jan ajiyar zuciya sauri sauri, da hanzari ya sanya hannunshi na dama ya dafe saitin zuciyarshi don ji yake son Aisha yana qoqarin fasa qirjinshi ya fito.
“Nima ina sonka Abdul, kawai dai bansan yanda zanyi in nuna maka irin son da nake maka bane, amma insha Allahu inai maka tanadin rayuwa da farin ciki mai dorewa har qarshen rayuwar mu idan mu ka yi aure, ka daina barin soyayyata tana wahalar da kai mijina. Bazan yafewa kaina ba matuqar son da kake min ya cigaba da wahalar da kai mijina...”
Ta fada bayan tayi kokarin daidaita natsuwarta daga duniya nishadin da kalaman Abdul suka cilla ta.
“Baki da laifi ko kadan matata, soyayyarki a zuciyata wani al’amari ne da Ubangiji kadai yasan dalilin da ya jarbceni dashi. ki daina zargin kanki akan yanda sonki ya zama jinin jikina, wallahi baki da laifi ko kadan.”
Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi bayan idona ya fada kan agogon dakin da ya nuna qarfe bakwai da minti ashirin na dare, har an kira sallar magariba an idar daf da kiran sallar isha’i. Awa daya da minti ishirin kenan muna magana a waya da Abdul.
“Lala lala.... mijina kaga yanda lokaci yaja kuwa ba tare da mun ankara ba?”
Sai a lokacin ya watsa idanunshi da suka canza launi daga farare zuwa ja kadan da kore kore, Cike tsananin shauqin soyayya da kwantar da murya mai cike da buqatar muradin abinda zuciyar shi take so a kusa da shi yace,
“Na gani matata! ke ce kika sa na manta da kowa da komai...”
“Ni dai babu ruwa na mijina, yanzu dai kaje kai wanka da alwala kayi sallah, bayan haka kuma sai ka je ka ci abinci. Ni ma yanzu zan je na yi sallah.”
“Umarnin ki abin bi ne a gareni matata! Amma ina roqon addu’a a sujjadarki ta qarshe, kin san addu’ar mace ga miji kar6a66iya ce a gurin Allah.”
“Ai dole in yi maka addu’a mijina, a kowace sallah tawa addu’arka ta musamman ce.”
“Na gode matata! Amma kin san akan abinda nake so ki yin addu’a?”
“A’a, sai ka faxa mijina...”
Ta amsa da zaquwa don jin ko mene ne buqatar tashi.
“Ki yi min addu’ar Allah ya bani sa’ar kama wadanda suka kashe Sadiya cikin satin nan don samun damar mallakar Aisha a matsayin matar aurena a sati na gaba da za mu shiga"
Sai da dariya ta qwace mata ba tare da ta shirya wa hakan ba. Cikin dariyar ta ce
“Komai tsawon lokaci za ka samu nasara in Allah ya yarda mijina.”
“Dariya kike min ko?”
Ya tambaye ta bayan ya yi qwafa.
Dariyar ce ta ci gaba da jan ta don haka cikin dariyar ta sake fadin
“A’a, ni ba dariya nake maka ba, a kan me zan yi maka dariya?”
“Za ki yabawa aya zaqinta duk lokacin da ki ka zo hannu yarinya tun yanzu gara ki bi ni a hankali”
“Oho dai, ai Mummy na ba za ta bar ka ka ci zalin ‘yarta ba.”
Ta fada bayan ta tsaida dariyar, sannan ta murguda baki kamar yana kallon ta.
“Lokacin da zan ci zalin naki ai Mummynki tana can ba ta da masaniya a kan komai.”
“Bye-bye mijina, ana kiran sallar isha’i...”
Tana gama fadin haka ta katse wayar don jin da tayi hirar tasu ta qi qarewa. Bandaki ta shiga ta dauro alwala don ba da farali. Bata qi gabatar da addu’ar da Abdul ya roqa a gare ta ba. Domin ita kanta za ta so a ce igiyar auratayya ta shiga tsakaninsu a nan kusa don samun damar mallakar junansu har abada a matsayin miji da mata.
Suna zaune da Mummy da Daddy (mijin Mummy) a kan dining table suna cin abinci, duk hankalinsu yana kan ta. Suna tarairayar ta don ta saki jiki ta ci abinci sosai. Daddy da kanshi ya zuba mata abinci mai yawa a filet ya miqo mata tare da zuba mata juice a kofi yana fadin
“Baby, ki yi sauri ki cinye in qara miki, so nake yi ki yi girma sosai kin ji yarinyata?”
Dariya ta qyalqyale da ita sannan ta ja abincin kusa da ita ta fara tsakura tana kallon idanunshi ta ce
“Daddy idan na cinye wannan abincin ai sai a zo a gan ni. Zan dai dage in ci ko da daya bisa hudu na abincin da ka zuba min. A hakan ma wai don Mummyna ta iya sarrafa girki yayi dadi kamar zai tsinke kunne ne"
Ta qarasa maganar tana kallon idanun Mummynta da tunda suka fara caftar tana kallon ta da murmushi a fuskarta.
“Daddyn Baby ka ji ‘yarka tana tsokana ta ko?”
Ta fada bayan ta mai da idanunta a kanshi, a muryarta dauke da salon shagwava.
“Ai gaskiya Baby ta fada Mummyn Baby, ke din ba dama ce in dai gurin sarrafa kowane kalar abinci ya ba da ma’ana ne.” YA fada yana dariya.
“Ka dai goyi bayan diyarka kenan ko?”
ta sake jefa masa tambayar tana dariya.
“Eh mana, ai gaskiya diyar tawa ta fada.”
“Kin ji dai Mummy, Daddy ma ya san kin cancani a ba ki award ta kowane 6angare, musamman ma a gurin hada abinci.
Hira suke gudanarwa cikin nishadi da fahimtar juna har suka gama cin abincin, ita ce ta kwashe kulolin abincin da filet da komai da suka yi amfani da su zuwa kicin.
Kan kujerun falo suka koma da zama suna hira jefi-jefi tare da kallon T.V.
“Gobe idan Allah ya kai mu za mu shiga kasuwa ni da Baby don za6a mata kayayyaki irin namu na gida (atamfa, leshi, shadda, materials) daga can sai mu wuce gurin tela mu ba da dinki. Idan lokaci bai qure ba za mu biya gaida Ardo.” Mummy ce take yi wa Daddy wannan bayanin.