Sashe 13
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Bai ce da shi komai ba illa ra6ewa da ya yi gefe maigadin ya shiga dakin ya zauna a kan bencin. Biyo bayanshi ya yi sannan ya zauna a can nesa da shi, yana jiran abinda Abdul zai ce da shi.
“Malam ina fatan ban takura maka ba? Sam ba na jin barci shi ya sa na yanke shawarar zuwa gurinka don in taya ka hira.”
“Habawa ko da na ji! Ni fa na yi mamakin ganin ka a wannan lokacin bayan har na fitar da tsammanin ka yi nisa cikin barci.”
Maigadin ya fadi haka yana qara washe haqora tare da sakin jikinshi gaba daya.
“Ka san gobe ranar aiki ne, ko a gida ban cika sakin jiki in yi barci mai nisa a daren Lahadi ba, amma fa ina kai wa sha biyu na safe ban tashi ba ranar Asabar da Lahadi, so barcin da na yi a safiyar Lahadin yau shi ya sa a daren barcin ya qi kawo min farmaki.”
“Allah Sarki Ranka ya dad'e, ai kuna matuqar qoqari. Irin wannan aikin naku na ‘yansanda ba kowa ne zai iya shi ba, shi ya sa ladanku sai gurin Ubangiji.”
Sai da Abdul ya yi dariya sannan ya ce,
“Aikin namu ai duk kusan tafe yake da naku Malam Inusa. Bambancinmu da ku kadan ne, ka ga mu muna gadin rayuwar al’umma ne, yayin da ku kuma kuke gadin wasu daga cikin al’ummar. Ka duba, misali yadda duk mutane gidan nan a yanzu haka suna kwance suna barci, amma kai a lokacin barci kai kuma idanunka biyu kana gadinsu. Ka ga dole a jinjina muku, Ladanku ku ma sai gurin Allah. Don haka nake ganin ko miliyan nawa aka biya ku da shi ba a biya ku abinda ya dace da ku ba.”
Dariya maigadin ya qyalqyale da ita cikin matuqar jin dadin an yabi qoqarinshi, kuma ya san kadan daga cikin aikin Abdul ne ya sa a yi masa qarin albashi. Don haka ya sake kwantar da kai yana nunar wa Abdul irin qoqarin da yake yi a kan aikinshi na gida.
“Maganarka gaskiya ne Ranka ya dade, yanzu ka duba dai yadda Alhaji Abba ya dawo gidan nan a galabaice, idan ba da irinmu haziqan masu gadin ba ai sai ya shiga cikin wani hali ba tare da sanin iyalan gidan nan ba.”
An sosa wa Abdul inda yake yi masa qaiqayi, don haka ya sake yabon maigadin da cewa,
“Ni ma tuni na fahimci qoqarin da kake yi Inusa, kuma ya kamata a qara maka albashi, domin ka cancani fiye da dubu talatin a wata. Amma kai kana ganin wane irin ciwo ne a jikin Abba haka? Mutanen gidan nan sun ankara kuwa?”
Da matuqar mamaki a fuskar maigadin ya ce,
“Amma dai kun kwana biyu ba ku hadu da Alhaji Abba ba ko Ranka ya dade?”
Kai tsaye ya amsa masa da cewa,
“Qwarai kuwa, tun da na dawo Kaduna da aiki na bar gidan nan ban qara haduwa da shi ba sai yau.”
“Shi ya sa ba ka san da wadannan ciwukan a jikinshi ba, ina tunanin yau kimanin kwanaki tara kenan ko goma da ya dawo gida da wadannan ciwuka. Amma dai ban san ko da me ya ji su ba, ni dai na fi tunanin dambe suka yi da wani ya yayyanka shi. Abin daure kai game da ciwukan shi ne, a kullum yana sha da shafa magani a kansu, sam sun qi nuna ko alamun warkewa.
A dazu ma sai na ji ciwon har wari-wari suke yi suna fitar da wani irin ruwa. Ni addu’ar da nake yi ma Allah ya sa dai ba wani abu abokin fadan nashi ya yi masa ba.”
“Wani abu kamar me kenan?”
Abdul ya tambaye shi da mamaki a fuskarsa.
“Wani abu kamar asiri mana, ka san mutanenmu mafi yawancinsu babu tsoron Allah a zuciyarsu.
Dariya Abdul ya yi sannan ya ce,
“Ba na tunanin haka Inusa, wataqila dai magungunan da likitoci suke ba shi ba ya amfani da su daidai, kuma a kan lukutansu. Ko kuma lokacin warkewar ciwon ne har yanzu bai yi ba.”
“To Allah dai ya kawo sauqi, domin ko mutanen gidan hankalinsu tashe yake a kan ciwon nan, shi Abban ne ma dai na ga kamar bai damu ba.”
“Ciwo a jikinshi, amma a ce bai damu ba Inusa? Ai in da wanda ya damu a kan ciwukan bayan shi ne.”
Shiru Inusa ya yi yana tunani, daga bisani kuma ya ce,
“Ina da hujja a kan abinda na fada Ranka ya dade. Ka ga duk da wadannan ciwuka na jikinshi bai fasa fita a kowane dare kamar yadda ya saba ba. Ko yau da ya dawo gida a wannan lokacin sai da na yi mamaki sosai a zuciyata, domin lokacin dawowarshi shi ne qarfe daya da rabi zuwa biyu na kowane dare. Idan ka ga Alhaji Abba ya dawo da wuri, to kana cikin gidan ne.”
Ajiyar zuciya mai nauyi Abdul ya sauke, a ranshi yake Allah wadai da sakaci irin na Baffanshi da matarshi. Sun manta yanzu dan’adam ake kiwo ba dabba ba?
Kiran sallar farko da ya ji an yi daga masallaci can nesa da gidan ya sa ya mai da idanunsa kan agogon wayarshi. Qarfe hudu na asubahi. Miqewa tsaye ya yi sannan ya sa hannu a aljihun wandonshi ya zaro kudi masu dan yawa, a qiyasce za su kai dubu goma sha biyu. Inusa ya miqawa tare da fadin,
“Inusa ga wannan ka sai katin waya. Zan duba mota ta idan ta tashi zan tafi gida yanzu.”
Hannu biyu maigadin ya sa ya kar6i kudin yana godiya tare da yi wa iyayen Abdul addu’a.
Har ya sanya kanshi ya fice daga dakin sai kuma ya juyo yana kallon maigadin dake biye da shi a baya don bude mishi qofar gidan.
“Uhmm! Ba na buqatar iyalan gidan nan su san a nan na kwana, domin Baffa ba zai ji dadi ba idan na kwana a gidan nan na tafi ba tare da mun gaisa da su ba.”
“An gama ranka ya dade, matuqar ba kai ne ka fada musu ba ba za a tava jin haka daga bakina ba.”
Yana tafe a mota yana tunani tare da saqe-saqen maganganun da suka yi da maigadi a zuciyarsa, har ya isa gidanshi. Sai da ya gabatar da sallar asubahi sannan ya kwanta da nufin rintsawa zuwa qarfe bakwai na safe, awa daya daidai ya dauka gurin shiryawa don haka takwas da minti ashirin a ofis ta yi masa. Sai da ya nitsa bayan ya gama duba wasu fayil sannan ya dauko wayarshi a laluba lambar Yasmin.