Sashe 6
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
“Ke muguwa,,,,”
Cikin tsawa mai qarfi ta ji muryar ‘Arne na kan tudu’ ya yi amsa kuwwa a cikin dakin yana qwala mata kira.
A tsorace ta miqe daga kwanciyar da tayi tana waige-waige, amma ba ta gan shi ba kuma komai na dakin yana nan a inda yake. Cikin sakan biyar muryar Arne na kan tudu ta ci gaba da karade lungu da saqo na cikin dakin, da qaraji yake qwala mara kiran amma ba ta gan shi ba.
Da sauri ta dira daga kan gadon, ba ta tsaya neman zani don rufe tsiraicinta da rigar barcin ta bayyana ba ta nufi qofar dakin da gudu a tsananin tsorace, niyyarta ficewa daga dakin.
Duk yadda ta so bude qofar dakin ya qi buduwa, murda key din dakin take don budewa amma kamar tana sake datse qofar, kuma har a wannan lokacin Arne na kan tudu bai daina qwala mata kira cikin tsawa ba.
A rud'e ta zame ta zauna a qasa jikin qofar sharaf sannan ta sanya ‘yan yatsunta duk biyu ta toshe kunnuwanta gami da rintse idanunta da qarfi, duk da ba wani abu take gani ba.
Turirin zafi mai tsanani hade da tsamin barasa da hamamin warin da yake doso ta ne ya sa ta bude idanunta don gani ko me yake kusanto ta. Yana zaune a kan dan dutse mai tudu shi ba a sama ba kuma shi ba a qasa ba. Sanye da da dan yaloluwar riga wace take bayyana rama da qasusuwan jikinshi. Duk jikinshi hayaqi yake fitarwa mai hade da tururin zafin wuta. Idanun shi sun yi jawur fiye da yadda ta saba ganinshi. Da hannunshi mai dauke da rudu-rudun jijiyoyi yake watso mata daquwa sannan ya varke da wata mahaukaciyar dariya, lokaci guda ya turvune fuska gami da fashewa da kukan gyare. Saida ya tsagaita sannan ya fara magana
“Keh muguwa! Kin bamu aikin da ya fi qarfinmu! Kin sa na tura dan tsumuri inda za a yi sanadin hallaka shi, to ya dawo da alwaqarin ba zai mutu shi kadai ba, don haka ya dau fansarshi a kaina ta hanyar watsa min tokar da za ta yi ajalina. Don haka ni ma ba zan mutu ni kadai ba sai tare da ke baqar muguwa.”
Toka mai tsananin zafi ya watsa mata tun daga kanta har zuwa sassan jikinta. Saukar tokar a jikinta da wani azababben zafi da ta ji yana ratsa qwaqwalwarta ya sa ta yanka ihu mai tsanani yayin da shi kuma Arne na kan tudu ya bace vat! yana ci gaba da rera kukan gyare da babu dadin saurare ko kadan.
Kamar yadda jikin Arne na kan tudu yake fitar da hayaqi da wari da hamami cikin minti biyu ita ma jikinta ya fara fitar da haka. Azabar da take ji a jikinta kamar ana zuba mata garwashin wuta ya sa ta ringa yanka ihu tana yage dan yalolon rigar jikinta tana jefarwa.
Daga can wajen qofar dakin ‘yanmatan gidan suke dukan qofar suna qwala ihun kiran
“Hajiya lafiya!?”
Ina! Hajiya Danasha ta yi nisa sam ba ta san suna yi ba, ihu kawai take yi tana birgima a qasan dakin saboda azaba. A hakan ta ci gaba da kasancewa har qarfe biyu da rabi na dare, sannan rai ya yi halinsa.
‘Yanmatan gidan sam ba su da masaniyyar Hajiya ta cika, koda suka daina jin ihunta sai suka yi tunanin barci ne ya dauke ta, sai washe gari suka nemo maza aka karya qofar dakin, nan aka tsinci gawarta tsirara haihuwar uwarta, kuma jikinta da fuskarta baqi qirin alamun qona ta aka yi. Ta kumbura suntum sai wari gawar da dakin suke yi.
Duk tsananin shaquwarta da ‘yanmatan gidan da irin kashe musu maqudan kudaden da take yi kasa zama a dakin da gawar take suka yi, sai wani sashi na daban suka koma da zama a cikin gidan, suka nemo lambobin qawayenta da suka sani, suka kira suna sanar da su abinda ya faru.
Minti talatin zuwa awa daya gidan ya cika da manyan mata qawayen danasha. Amma ganin irin mutuwar da ta yi da yanayin da gawartata take ciki daya bayan daya suka ringa sulalewa suna barin gidan. An rasa mazan da za su yi jana’izar ta. Kuka kawai Hajiya Mariya take tana qyamar harkarsu ta ‘yan neman jinsi, a zuciyarta take tunanin
“Ashe duk amintakar da suke yi da junansu ta fatar baki ce? Yau ga shi Hajiya Danasha da ta kasance jigon kafuwar qungiyarsu ta rasa masu tsayawa a kan gawarta? Me ake da irin wannan qazanta kuma wulaqanctacciyar rayuwa?”
Sai da aka kira sallar Azahar a masallacin dake unguwar da gidan Hajiyar yake sannan Mariya taje da kukanta ta samu limamin masallacin ta yi masa bayanin duk halin da ake ciki. Da liman da Ladan da daidaikun mutane da ba su wuce takwas ba suka sallaci Hajiya Danasha zuwa makwancinta na gaskiya.