Sashe 11
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ni kaina na fahimci tsananin soyayyarshi gare ta Maman Baby, ki daina damun kanki, kin ji yarinyata? Dama can Allah bai qaddara ke ce matar farko a gurin Abdul-Ahad ba.”
Da haka suka shawo kanta ta yi watsi da duk wata damuwa daga zuciyarta.
Kiran Ardo da ya shigo cikin wayarta shi ya sa ta qarasa wartsakewa gaba daya har ta samu qwarin gwiwar ci gaba da linka son Abdul-Ahad a cikin zuciyarta.
“Ina fatan ba ki dauki maganar auren Abdul da Yasmin kin sanya ta a zuciyarki har ta zame miki abin damuwa ba Aisha?”
tambayar da Ardo ya fara yi mata kenan bayan sun gaisa, ya yi mata ban gajiyar taron gabatar da ita ga zuriyarsu.
A kunya ce ta amsa masa da cewa
“A’a.”
“Ki kwantar da hankalinki Aisha, a sati mai zuwa idan Allah ya kai mu za a daura auren Yasmin da Modibbo, amma hakan ba shi ne zai hana maganar aurenki da shi ya tabbata ba. Ko a yau idan Abdul ya gama binciken wadanda suka hallaka ‘yar’uwarki Sadiya ya miqa su suka fuskanci hukunci zan daura aurenki da shi. Tun fil azal Allah bai qaddari ke kadai za ki zauna da Modibbo ba, don haka ki kwantar da hankalinki, kuma kada ki nuna wa Abdul komai da ya danganci kishi da 6acin ranki, hakan shi ne zaisa ya cigaba da gudanar da binciken da yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.”
Da haka suka yi sallama da Ardo bayan ta yi masa godiya tare da alqawarin in Allah ya yarda ba za ta sa6a wa umarninsa ba.
*** *** ***
Yana zaune a cikin motarshi a qofar get din gidan, baqin cikin da ta qunsawar zuciyarshi ita da mahaifanta ya sa sam bai yi niyyar shiga da motar ko harabar gidan ba. Duk da agogon motar ya nuna masa qrfe goma da kwata na dare, hakan bai sa ya fasa kiran lambarta ba. Umarni ya ba ta a kan cewa ta fito qofar gidan yana jiran ta.
Da murna take canja kayan barcin jikinta zuwa riga da siket na atamfa, wanda ya kama jikinta sosai, duk yadda ta so ta saka jarumta a ranta hakan ya qi yiwuwa, qirjinta na bugawa kadan-kadan, amma fa ko kusa ba ta nadamar abinda ta aikata a can Yola a gaban zuri’arsu. Wanda iyayenta suka kira rashin kunaya, kuma wai a fadarsu za ta yi nadama a can gaba, musamman alqawarin da ta dauka na daina karatun da ta dauki tsawon shekaru biyu da watanni shida tana yi a jami’a, wata uku suka rage mata amma ta za6i watsar da karatun a kan soyayyar wanda bai damu da ita ba.
Qwanqwasa qofar motar ta yi bayan ta ja qofar domin budewa, ta ji a kulle take daga ciki. Sai da ta gyara zamanta a kan kujerar mai zaman banza ta kusa da direba sannan ta kashe murya cike da yanga ta ce
"Yaya Abdul barkanmu da dare.”
Harara ya watsa mata, sannan ya ci gaba da kallon ta qasa da sama. Haushinta matsananci yake ji a zuciyarshi, domin ya san ba don Allah da Annabi ta roqi a kusanto da daurin aurensu ba. Ko ma mene ne dalilinta ita ta sani, amma yana da tabbacin dalilin nata ba ya rasa nasaba da ganin Aisha a cikin zuri’arsu.
“Sai na ji kin buqaci a kusanto da daurin aurenmu saboda kina da matsanancin sha’awa ko?”
Tambayar da ya jefa mata kenan yana kallon qwayar idanunta don jin shi ma rashin kunya za ta yi masa?
Sai da ta gama tattaro dan ragowar yawun da ya rage mata, sannan ta yi qarfin halin cewa,
“Ko me na yi ka fi kowa sanin dalilin da ya sa na aikata shi Yaya Abdul, kuma ba don buqatar kaina na nemi a kusanto da daurin aurenmu ba, don buqatar kanka ne da kuma guje maka fada wa halaka.”
Shiru ya yi yana qoqarin danne zafin da zuciyarshi take dad'a dauka a kan Yasmin, a yadda yake jin ranshi zai iya yi mata dukan kawo wuqa ya bar ta kwance a wurin.
“Qarya kike yi Yasmin, ba ki isa ki raina min hankali ba, amma ina tabbatar miki za ki yi dana sani a can gaba. Kuma wannan auren da za a daura mana nan da kwana shidda ba shi zai sa in fasa auren Aisha ba, duk haukanki zakiyi ki gama, shashasha.”
Qus ta yi har ya gama zazzage mata duk ruwan bala’in da ya qunso a cikinshi, domin ta san kadan daga aikinshi ne ya tsittsinka mata mari idan ta nemi yi masa rashin kunya. Don haka ta ja baki ta yi gum, sai hawaye da yake tsiyaya a idanunta.
Kukan da ya ga tana yi shi ne ya dan sanyaya masa jiki, don haka ya kau da kanshi gefe ya ce
“Kin san dai daga gobe har zuwa juma’a ina cikin aiki, zai yi wuya ki sake gani na a cikin wadannan kwanakin. Duk abinda kike buqata na shirye-shirye ki kira ni a waya zan aiko miki da shi. Ranar Juma’a zan wuce Yola da yamma, sai mun hadu a can.”
Ba ta ce komai ba kuma ba ta daina kukan da take yi ba, sai ma qara armashi kukan nata tayi ta hanyar hadawa da shesshekar kuka da wani irin salo wanda dole ya sanyayar da jikin wanda aka yi domin shi.
Ta yi nasarara tabbas, domin gaba daya ya dawo da hankalinsa kan ta. Cikin kulawa ya ce
“Wai mene ne kuma? A tunanina murna ya kamata ki yi tunda burinki yana daf da cika?”
Fuskarta jage-jage ta dago idanunta ta zuba a kanshi, murya na rawa ta ce
“Ya za a yi in yi murna bayan Allah ya dora min son wanda sam ko daidai da qwayar zarra ba ya so na? Duk wani kuskure da kake ganin na aikata son ka shi yake tunzura ni gurin aikatawa. Me ya sa ba za ka ji tausayi na ba Yaya Abdul? Ina son ka son da har ban san iyakarshi ba, amma kar ka manta ba ni na dora wa kaina wannan jarabtar ba, Ubangiji da ya dora min shi ya san yadda zai yi da ni.
Duk da ka qi yi min uziri a kan kura-kuran da na aikata, hakan ba zai hana in durqusa har qasa in ba ka haquri ba. Don Allah ka yafe min Yaya Abdul.”
Take ta zame daga kan kujerar zuwa qasa ta daga hannayenta biyu sama alamun roqo tana ci gaba da jan majina da tsananta zubar da hawaye.
Ta yi matuqar ba shi tausayi. Nan take ya fara tunanin idan shi ne Aisha take masa irin abinda yake yi wa Yasmin ya zai yi da ranshi? Don haka a take ya yi alqawarin daina ganin laifinta a kan duk wani abu da za ta aikata. Kamo hannunta ya yi ya zaunar da ita a kan kujera, cikin murya mai dauke da alamun rarrashi ya ce
“Ni ban ce ba na son ki ba Yasmin, ke din ce har yanzu ba ki fahimce ni ba. Amma komai ya wuce, kuma daga yau kada ki sake cewa ba na son ki.”
“Da gaske kana so na Yaya Abdul?”
Ta tambaye shi cikin murna da zumudi.
“Qwarai kuwa Yasmin, qila ma har fiye da yadda kike so na.”
“Allah na gode maka... Na gode maka ya Allah. Allah ka tabbatar da soyayyata ni kadai a zuciyar Yaya Abdul.”
Bai amsa wannan addu’ar tata a fili ba, da sauri ya amsa da
“Ba amin ba”
A zuciyarshi. Ganin yadda take murna sai ya ji sam ba ya son bata mata rai a wannan dare.
“Yanzu dai kin ga dare ya yi, zan tafi. Ina fatan kin ji duk abinda na fada miki.”
Marairaice fuska ta yi cikin salon shagwaba ta ce
“Yanzu ba zan sake ganin ka ba har sai mun je Yola ranar Juma’a?”
“Haquri za mu yi, kin san yanayin aikina, ba ni da wani ishasshen lokaci.”
“Amma dai Yaya Abdul hutu za ka dauka bayan bikinmu ko?”
Ta sake jefa masa wani qorafin.
Ya qosa ya koma gida, domin lokacin da ya saba kiran Aisha su yi hira har sai barci ya dauke ta har ya gota da minti ashirin.”
“Eh, in Allah ya yarda.”
Ya amsa mata a gajarce.
Ta lura da qosawarshi, da tsoron kada liqin da ta yi ya valle ya sa ta ce,
“Shi kenan mijina, ina son ka sosai, don Allah ka daina qin daukar wayata a duk lokacin da na kira ka. Kuma kai ma ka ringa kira na don Allah ka ji mijina?” Ta roqe shi a marairaice.
“Kada ki damu, na yi alqawarin kiranki idan na samu lokaci. Kuma zan ringa daukar wayarki matuqar kin kira a lokacin aiki bai yi min tsanani ba.”
Ya fadi haka yana murmushi, sukai sallama.
Farin ciki fal zuciyar ta yayin da shi kuma ba yabo ba fallasa sannan ya yi umarni a gare ta ta isar masa da gaisuwa gurin Baffanshi.
Har ta qule zuwa cikin gida bai tada motar ba, kuma bai daina kallon hanyar qofar get din gidan ba ta inda ta shiga. Minti biyar bayan shigar ta cikin gidan lokacin agogon motar ya nuna sha biyu na dare saura minti goma.
Motar aka danno da gudu kai tsaye aka nufi babbar qofar get din gidan, tun daga nesa ake danna hon ba qaqqautawa. Ita ta ja hankalinshi daga kan wayarshi da yake ta danna kiran lambar Aisha, amma sam ba ta dauka ba, hakan shi ya ba shi tabbacin ta yi barci. Bai gaza gane motar Abba ba ne take wannan mahaukacin gudu da hon din, kuma haske ne tar a qofar gidan.