Sashe 20
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"‘Yar wulaqanci… ke Smally! Yau dai na ga duk abinda kike 6oye min.”
Abinda Zee ta fara ce mata kenan bayan haduwarta da su a tsakar gidan suna zaune a kan fararen kujerun da aka gudanar da saka lallen amarya.
“Oh, su cakwaikwaiwa ashe a na nan? Ai na zaci kun dad'e da komawa gida. Yanzu kun kai Legas a barci”
Dariya suka kwashe da ita har ita ma ta taya su darawa.
Maryam ce ta amsa mata da cewa
“Mun kira wayarki har babu iyaka amma da yake tsuntsun soyayya yana kanki ba ki san muna yi ba, don haka muka tambayi Mummynki ko za ki dawo gidan nan, tabbatar mana da za ki dawo ta yi ya sa muka ce komai dare sai mun jira ki kin dawo domin mu sha labari"
“Ai ko kun taka zero, domin babu wani labari da za ku samu daga gare ni, sai ku ne ma da nake jira ku ba ni labarin abinda aka yi ba na nan.”
“Kin isa ma kice ba za ki ba mu labari ba? ai yau na yi takaicin ina ma zan iya zama quda in je in maqale don ganin yadda Smally take rikita bawan Allah”
“Saboda tsabar tsegumi kike fatan zama quda?” Aisha ta tambaye ta tana dariya.
“Ai ba ita kadai ba har da mu gaba daya.”
In ji Ilham tana dariya.
“Ai kuwa da hakan ya kasance da kun bata wasan, domin ina ganin qudaje har hudu a falonmu zan nemo sheltox in fesa musu duk su mace, kun ga gulma ta yi kyau kenan ko?”
Dariya suka sake kwashewa da ita gaba dayansu. Sannan ta zame zuwa cikin dakunan matan gidan don duba inda Mummy take a zaune.
Ba su dad'e ba Daddynta ya iso suka wuce zuwa gida tare da Zee, domin ta maqale dole sai ta ba ta labari shi ya sa ta yi wa Ammi (mahaifiyarsu) kamar yadda ta ji suna kiran ta waya ta sanar da ita a gidansu Aisha za ta kwana.
“Ashe kin san yaya Abdul, amma shi ne kika bar ni ina ta haukan cewa idan ya zo zan hada ki da shi?” Tambayar da ta fara jefa wa Aisha kenan bayan sun yi daidai a kan katifa duk suna sanye da kayan barci.
“Wa ya ce miki na san shi Zee?”
Harara cikin wasa ta watsa mata tana murmushi, sannan ta amsa da cewa
“Ina ganin lokacin da kuka bar gidan Ardo tare da shi dazu, kuma sai a lokacin na fahimci dalilin da ya sa Yasmin take matuqar jin haushin ki.”
Akwai qauna da shaquwa mai qarfi tsakanin Aisha da Zainab, don haka ba ta boye mata komai ba game da soyayyarta da Abdul yayanta, amma ta boye mata duk rikita-rikitan dake cikin soyayyar tasu da kuma aihinin yadda aka yi ta hadu da Abdul.
Tagumi ta yi hannu bibbiyu ta ce
“Allah sarki Yaya Mu’azzam, ashe bai da rabon aurenki, duk da bai fada min ba na fahimci yana tsananin son ki.”
Dariya kawai ta yi ba ta ce komai ba.
“To amma ta ya aka yi Yasmin ta san Yaya Abdul yana son ki?”
Ta tambayi Aisha da mamaki.
“Akwai ranar da ta ta6a ganina a gidanshi na Kaduna tun kafin in dawo nan gida Yola”
Ta amsa mata a taqaice.
“Au, dama kin yi zaman Kaduna?”
“Qwarai kuwa.”
“Amma wallahi na ji dad'i da ya kasance za ki auri yaya Abdul, daman can duk ‘yanmatan family ba a so hadin Yasmin da Abdul ba, saboda baqin halinta da girman kanta.”
“Hmm! matar mutum ai kabarinsa.”
Ta fadi hakan don ba ta so hirar tasu ta yi tsawo har ya kasance sun ci naman Yasmin.
“Qwarai kuwa Aunty Smaily.”
Harara Aisha ta watsa mata, sannan tace,
“Tun lokacin da na so ki kira ni da Aunty ba ki kira ni ba sai yanzu? Wannan shi ne daga baya
(wai an yi sadaka da bazawara).”
Dariya ta yi ta ce
“Ai yanzu ya zama dole in ce miki Aunty, idan ba haka ba Yaya Abdul ya yi quli-qulin kubura da ni”
“Can dai ta matse miki. Ni kin ga kwanciyata.” Tana gama fadin haka ta juya mata baya ta daga hannuwa sama tana karanta addu’ar barci.
“Mu kwana lafiya.”
Ta amsa mata bayan ta fahimci ta gama addu’a.
Qarfe goma sha biyu da rabi na dare kiran Abdul ya yi mata ya tada ta daga barci, murya qasa-qasa irin ta wacce ta fara barci ta amsa wayar tana fadin
“Hello!”
“Matata kin yi barci ko? Yi haquri na tashe ki daga barci.”
“Me kake yi har yanzu ba ka yi barci ba mijina?”
“Ina tare da Ardo ne, kasa haquri na yi da rashin jin tattausar muryarki a daren nan. Shi ya sa na kira don in ce miki ina son ki”
“A gaban Ardon kake wannan maganar?”
Dariya yayi qasa-qasa, har yanzu ba ta ji jarumtaka kamar yadda yake da a muryarshi ba, da alamun har yanzu a cikin damuwa ya ke.
“Ardo zai hana ni magana da iyalina ne?”
“Mijina kamar akwai abinda kake 6oye min ko?”
Ajiyar zuciya ya sauke kamar ba zai amsa tambayar ta ba, sai can kuma ya ce
“Me ya sa kika fadi hakan matata?”
“Kawai dai a jikina ne na ji hakan. Kuma ko don irin soyayyar da nake maka ai ya cancani in fahimci idan kana cikin damuwa ko kana cikin farin ciki. Sai dai kuma idan kai a gurinka ban kai matsayin da za ka fada min damuwarka ba..”
“Oh my God! Wallahi ba haka ba ne, kin san dai ba na son in tayar miki da hankali ne. damuwata mai sauqi ne idan ke kina cikin farin ciki.”
“Ta ya kake tunanin hankalina zai kwanta idan har wanda nake so zai kasance cikin damuwa?”
“To yanzu dai ki kwantar da hankalinki ki kwanta ki yi barci, gobe idan na zo sai mu yi maganar.”
Ajiyar zuciya ta sauke cikin damuwa, amma ta kasa cewa komai.
“Mene ne kuma matata?”
Ya tambaya hankalinsa a tashe.
“Kana so in daina walwala in shiga cikin damuwa ko Abdul?”
Ta tambaye shi muryarta na rawa-rawa, tana shirin fashewa da kuka.
“A’a, a’a. Wallahi ba na son damuwarki matata, hasali ma tsoron halin da za ki iya kasancewa a ciki ne ya sa nake 6oye miki damuwata.”
“Na yi maka alqawarin ba zan damu ba, yanzu dai ka fada min taka damuwar.”
“Mu bari zuwa gobe Aisha don allah, kin ga yanzu ina tare da Ardo ne.”
“Allah ya kai mu goben…”
Dif cajin wayarta ya dauke gaba daya, kuma abin cajin yana falo, don haka ta haqura ta kwanta tana saqe-saqe a cikin zuciyarta har barci ya dauke ta.
Qarfe goma na safiyar washe gari ya iso gidansu cikin rakiyar abokansa guda biyu, don haka ba su samu wani isasshen lokaci na tattaunawa ba. sun yaba qwarai da breakfast din da ta shirya musu, tare da taimakon Zainab. Abinda ya ba ta dariya shi ne yadda Abdul yake ta wani kakkare ta a lokacin da take gaisawa da abokan nashi a falon baqin gidansu. Hatta Zainab sai da ta yi mata tsiya a kan hakan.
Dariya ta yi sannan ta kashe surutun bakinta da cewa
“Ina laifin mutum don ya yi kishi a kan iyalinshi?”
Qarfe hudu na yammacin ranar Juma’a ne aka shirya za a yi
“Fulani Day"
maza da matan da za su halarci gurin duk shigar kayan fulani za a yi. Haka ma Amarya da Ango. Irin kayan da za su sa kenan.
Hudu da kwata sun gama shiryawa tsaf domin babu African time, ita ma Aisha ta yi kyau sosai cikin kayan fulanin tamkar Bafulatana ta gaske.
“Wallahi Smally jikinki yana da kyau, duk kayan da kika sanya sai ya amshe ki tamkar da su aka halicce ki.” In ji Zainab kenan kuma da iyakar gaskiyarta take wannan maganar.
“Na gode…”
Abinda Aisha ta ce kenan ta fice daga dakin zuwa falo domin ta san tunda ta tanka su Maryam ma sai sun tanka.
An shirya komai na gurin gudanar da taron Fulani Day cikin tsari, domin hatta mutanen da za su halarci gurin a qididdige suke. Kati ne aka raba ga duk wadanda aka gayyata zuwa gurin. ‘Yansanda ne guda uku a qofar shiga gurin, dole sai ka ba da kati sannan za ka wuce zuwa ciki. Mu’azzam shi ma ya samar musu nasu katin, don haka suna zuwa ciki suka wuce kai tsaye.
Isarsu da kusan minti goma Amarya da Ango suka isa gurin cikin shiga ta alfarma ta kayan saqin Fulani, gashin kantin da yake kan Amarya ya sha dutsawu, da kayayyakin kwalliya irin na Fulani. Ta yi kyau babu laifi, domin amarya ce duk muninta kuwa ranar aurenta sai ta yi kyau.
Abdul ya yi kyau sosai cikin kayan domin tun farko shi mai kyau ne, duk hangen Aisha ba ta ga namijin da kayan suka kar6e shi irin mijinta Abdul ba.
"So hana ganin muni" Inji fareedah