← Book details A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kuka suke gaba dayansu, a lokacin ne suka sanar da ita ba su da masaniya a kan rasuwar Sadiya. Danye rasuwar ta dawo ma Aisha don ganin yadda suke kokawa harda Baba Jummala, ta kasa nuna dauriya hawaye kawai take tana fadin
“Inna lillahi wa inna ilaihiraji’un!”

Nasihar Ardo da ta Mummy da kuma jin rasuwar Sadiya sune suka taru suka saukarwa da ‘yan’uwan Aisha sanyin jiki, suka sauka dokin qiyayyar DA NAMIJI.
Ko da Ardo ya nemi maida su gidajen mahaifansu babu wacce tayi musu, a take suka fara tuba ga Allah tare da daura niyyar yin sabuwar rayuwa a gaban iyayensu da fatan samun mazaje nagari, kamar yadda Aisha ta samu.
Fatima ce ta fara neman a maida ta dangin mahaifiyarta ne a can qasar Nijar, amma adireshin inda suke zaune ba zai samu ba sai ta hannun qanin mahaifinta. Ardo ne ya amsa mata da cewa hakan ba zai zama matsala ba za a mayar da ita can din in Allah ya yarda.
Ba su samu wata matsalaba daga mahaifa da dangin kowacce daga cikinsu, duk gidan da suka je a mutunce da karamci ake karbarsu. Iyayensu da danginsu sun yi nadama matuqa, kuma sun tabbatar masu da babu inda ba su shiga don neman ‘ya’yan nasu, Ardo shi yake qara janyo hankulansu a kan amanar 'ya'ya da Ubangiji ya danqa a hannun iyayensu.
Da kuka suka rabuwa sannan Aisha ta Damqa kyautar chek na Naira miliyan biyar ga kowacce daga cikinsu. Baba jummala ce ta qara mata zuwa Miliyan goma, kuma ita ta yi alqawarin riqon Siyama da Suhaila da ta dauko su daga gidan Marayu kamar ‘ya’yanta na cikinta. A gidan da ta mallaka mata na mahaifinta suke zaune.
Ardo yayi alqawarin duk wani abu da zai taso dangane da su Siyama idan ana neman danginsu a neme shi, zai tsaya musu kai da fata kamar yadda zai tsayawa jikokinshi.

Alh. Musa qanin mahaifin Fatima yayi matuqar nadama sosai, domin kuka ya ringa yi da idanunshi, sannan ya duqa har qasa yana neman afuwarta. Koda suka sanar da shi abinda ya kawo su na neman adireshin dangin mahaifin Fatima don mayar da ita can kuka ya sake sakawa yana roqon Ardo da Allah da Annabi a bar ta a hannun shi zuwa sati mai zuwa da kanshi zai kaita gurin dangin mahaifiyarta ta kwana biyu. Amma ba zai iya barin ta a can ba don yana son ya nuna mata gata a matsayinta na diyar dan uwanshi, wanda a da can bai nuna mata ba. A kallo daya za ka gane tsantsar nadamarshi da gaskiyar abinda yake fadi har zuciyarshi ne, don haka suka amince da barinta a nan bayan ita kanta Fatiman ta amince da hakan.
Ba su samu kammalawa da komai ba sai ranar Asabar da yamma, jirgin qarfe takwas na daren ranar za su bi zuwa Yola, don haka suka ci gaba da shirye-shiryen komawa gida.

Suna zaune a falon Abdul, Aisha da Mummynta, Ardo yana cikin daya daga dakunan Abdul yana wanka. Hira suke da Mummy akan yadda maida ‘yan’uwanta gidajensu ya kasance tsakanin jiya da yau, shigowar Abdul cikin falo shi ya katse mata maganar da take yi.
Kallon-kallo suka yi a tsakaninsu sa’annan ya maida idanunshi a kan Mummy ya ce
“Mummy ko za ki ba ni aron diyarki ta yi min rakiya zuwa cikin gari?”
Ya tambaya yana Sosa keya, yana kara satar kallon Ayshan.

“Anya zan iya ba ka aron diyata kuwa Abdul? Babyna ta gaji sosai tana buqatar hutu ka ga bai kamata ka tara mata gajiya ba.” Ta fada kai tsaye tana kallon cikin idanunshi.
“Haba Mummynmu! ai don Allah na ce.” Ya sake fadi cikin salon roqo da kwantar da kai.”
“Tun da ka matsa bari in tambaye ta idan za ta iya zuwa.” Ta fada, sannan ta dawo da idanunta kan Aisha ta ce
“Baby wai za ki iya yi mi shi rakiya?”
Maqe kafada ta yi alamun a’a. Tana tura baki ta ce
“Ni dai a’a Mummy, shi kawai so yake ya qara wahalar da ni.”
“Toh, ka ji Abdul. Baby ta gaji da yawa, ka yi haquri kawai.”
Tagumi ya yi ya rasa hanyar da zai bullo musu. Yadda yai tagumin yai qasa da idanu ya so ya dan ba ta tausayi, shigowar Ardo dakin da sallama da maganar da yayi ya sa Abdul sakin murmushin da bai yi niyya ba.
“Mutum da matarshi an tava hana shi iko da ita Aishatu?” (Yana nufin Momy, idan ba ku manta ba sunansu daya) diyarki fa an riga an ba Abdul aurenta, kuma ina daya daga cikin shaidun da suka shaida, sadaki ya rage ya biya, jama’a da dama su shaida ya dauke ta daga gabanki”
Sunkuyar da kai qasa Aisha ta yi cikin matsanancin jin kunya. Mummy kuwa murmushi ta yi ta ce,
“An gama Ardo tun da ka sa baki, kai kuma Abdul ka yi tuqi a hankali kuma ka dawo min da diyata a kan lokaci.”
Mayafi kawai ta dauka ta yafa a jikinta, don dama ta yi wanka ta yi kwalliya cikin riga da siket na tamfar da ya yi matuqar dacewa da fatar jikinta.
“Matata kin ga yadda kika yi matuqar kyau cikin wadannan kayan kuwa? Ban tava ganinki cikin kayan dinki irin namu ba, sai a jiya da yau. Shigarki daga doguwar riga sai kayan turawa.”
“Doguwar riga da qananan kaya sune shigar da aka raine ni da su. Ban tava sanya irin wadannan kayan ba sai da Mummy ta dinka min. Ashe dai sun yi min kyau?” Ta tambaye shi da mamaki a fuskarta.
“Au, ke ba ki ga ni ba?”
ya tambaye ta shi ma da mamakin a fuskarsa.
“A’a ni ban gani ba, kawai dai gani na yi sun yi min yadda duk wani kaya da na saka yake min.”
“Ki gode wa Allah matata, wallahi ban tava ganin yarinya mai kyanki ba, ko wani kalar kaya kika sa sai ya karvi jikinki, a kullum kamar qara miki kyau ake yi.”
“Alhamdulillahi! Allah ya sa dai ba don kyaun kake so ba, ka ga idan haka ne duk ranar da ka ga wacce ta fi ni kyau za ka daina so na"
Sauka daga kan titi ya yi sannan ya yi fakin din motar, ya kamo hannunta jikinshi a sanyaye ya ce
“Haba matata, ki daina batun zan daina son ki, ko kin manta don ke aka halicce zuciyar Abdul-Ahad? Daina son ki yana nufin ba na raye a duniya, domin ko hauka nake yi ba zan daina ambaton sunan Aisha da irin son da nake yi mata ba. Wallahi ina son ki, so na tsakani da Allah. Ki daina kokwanto ko shakka a kan irin son da nake yi miki kin ji matata?”
Tsakiyar qwayoyin idanunta ya zuba nashi idanun suna kallon juna cikin tsantsar so da qaunar juna. Ya riga da ya gama kashe mata jiki da tausasan kalamanshi, a muryarta zai gane tsantsar so da yarda da aminci da sakankancewa.
Ta ce, “To na ji, mu tafi dare ya fara yi.”
“Kin ji fa kika ce, matata? Ba ki ce kin yarda ba...”
“Na yarda mijina.”
Ta amsa mishi kai tsaye. Tada motar ya yi suka ci gaba da tafiya inda suka nufa. Ya ci gaba da cewa
"Ina son ki matata, ina ma a ce an kawo min ke a matsayin matar aure na ne?”
“Ai ni matar taka ce, ko ka manta abinda Ardo ya fada kafin mu fito daga gida?”
“Ban manta ba, amma ai kin ji ya ce ban biya sadaki ba, kuma dubban jama’a ba su shaida ba.”
“Ai ka kusa samun damar mallakar matarka in Allah ya yarda mijina.”
“Allah ya nuna mana lokacin.”
“Amin mijina.”
Ta amsa kai tsaye ba tare da jin kunya ko tsoro ba.

* * *
Yau kwanaki uku kena tana kwana da wayarta a bude, kuma kusa da kunnenta don tsammanin samun kiran wayar Aisha kamar yadda
“Arne na kan tudu”
ya alqawarta mata. Ganin kwanaki biyu sun shude ba ta samu wayar Aisha ba kuma ba ta ji wani motsi daga Arne na kan tudu ba, kamar yadda ya ce idan ba su samu nasarar shiga jikin Aishan ba to zai dauki ladan aiki a jikinta. Don haka ta yanke shawarar qara masa wasu kwanaki biyun su zama hudu kenan. Tana fatan samun nasara a muguwar buqatarta.
Duk ‘yan matan da suke debe mata kewa a wannan kwanaki ukun ta hana su shiga dakin barcinta. Babban burinta shi ne idan Aishan ta kira ta su yi hirar da zai rage mata qarfin sha’awar Aishan a zuciyarta.
Tana kwance ta yi daidai a kan gadon daga ita sai yaloluwar rigar barci mai bayyana surar jiki, idanunta a bude suke ta qurawa P.O.P da ya mamaye saman rufin dakin ido, tana tunanin qirar jikin da Aisha ke da shi. Lokaci zuwa lokaci tana sakarwa kanta murmushi sa’annan ta shafa tumbin cikinta cikin nishadi.
Dif wutar dakin ta dauke ba zato ba tsammani, tsaki mai qarfi ta ja sannan ta janyo wayarta da niyyar kiran daya daga cikin ‘yan matan gidan. Dawowar hasken dakin ya sa ta sakin ajiyar zuciya ta aje wayar a gefe ta ci gaba da tunanin da take yi.
Chapter 5 · 0% Book details