Sashe 16
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ta ji ta sake cewa, “Yaya yanzu za mu shiga kasuwa, maganar ankon mu ne na ce bari in kira in yi maka tuni.” Dariya ta yi sannan cikin dan shagwaba irin wanda ake yi wa Yayan da aka shaqu da shi ta ce, "Kai Yaya, ai kai ma ka san dole ne a bikin babban Yaya mu yi shiga ta kece raini...” Shiru ta yi tana saurare daga bisani ta ce “Ammi ta ce babu ruwanta mu neme ka, shi kuma Daddy ya ce idan ya dawo da yamma zai neme mu.” Saurarawa ta sake yi, sannan ta ce, “Eh! Akwai shirye-shiryen da za mu yi namu na qannen Ango da Amarya, amma dai ba mu gama yanke shawara ba, zuwa dare ko gobe da safe zan kira ka.” Kallon ta kawai Aisha take yi, a zuciyartta tana dar-dar kada surutu ya sa ta yi wa Abdul maganarta, domin ta riga da ta nuna musu sam ba ta san shi ba. “A’a, yanzu dai anko za mu fara siyowa mu ba da dinki tun da wuri. Ka san telolin sai a hankali" Ta fada tana sosa kai. Ganin ta miqa wa Mummy wayar ya sa Aisha ta yi tunanin cewa ya yi a ba ta wayar. Sun dauki tsawon mintuna da za su kai goma suna magana da Abdul din, ba ta fahimtar abinda take cewa domin dai tana amganar ne cikin nutsuwa da hangen nesa, amma ta fahimci ya tambaye ta game da ita. Domin ta ji tana cewa, “A’a, sam ba ta tada hankalinta ba, tun jiya da aka yi maganar ban ga ta nuna bacin ranta ba.” Sai kuma ta ci gaba da cewa amsawa da “Eh ko a’a” Wani lokacin kuma ta amsa mishi da harshen fillanci. Daga qarshen maganar da suka yi ne ta fara fahimta, domin ta ji tana cewa “Eh, su biyar ne a nan. Ka san su Hafsat sa’annin Yasmin ne, dole cikin qawayen Amarya za su shiga. Su kuma nasu tsarin daban ne" Sai da ta saurara ya gama magana sannan ta ce “Dubu dari da hamsin ai ya yi musu yawa Abdul, ka san akwai hidima a gabanka, kuma daga nan gida ma za a qara musu wasu kudaden.” Dariya ta yi, sannan ta ce “A’a, ni kada ka janyo min rigima, tana ganin sa’anninta suna yin anko amma ita in ce ta jira yi zuwanka?” Shiru ta yi tana saurarenshi tsawon lokaci, sannan ta ce “Sai dai ka yi haquri, fita ai ya zama dole daga yau har bayan biki” Tana gama fadin haka ta katse wayar, ta miqa wa Zainab tana murmushi ta ce “Ya ce in ba ku dubu dari da hamsin.” Tsallen murna suka fara yi yayin da Aisha ta bi su da kallo daya bayan daya tana murmushi. “Uhm, Babyna kin yi wankan kuwa?” Mummy ta jefo wa Aisha tambayar bayan ta tsare ta da idanunta. Sosa qeya ta fara yi domin ta san kwanan zancen. Cikin muryar shagwava ta ce “Mummy tunda na shiga daki Zainab ta kira wayata ta ishe ni da surutu shi ya sa ban samu na yi ba har suka iso.” “Ba ruwana wallahi Aunty, saurayi ne ta tsaya hira da shi ko da muka shiga dakin fiye da minti ashirin ko kallonmu ba ta yi ba, sai ni ce ma da na gaji da jiran ta na amshe wayar na katse bayan na yi masa tsiyar ya qyale ta su gaisa da ‘yan’uwanta.” Da sauri ta fadi haka don kare kanta tana kallon Aisha cikin tsokana. Harara Aisha ta watsa mata, tare da qwafa mai isar da saqon zan kama ki ne. Wani irin zabura Mu’azzam ya yi, wanda ya sa kowa mamaki, bai damu da irin kallon tuhumar da kowa na falon ke mishi ba ya watso idanunshi kan Aisha ya ce, “Wane irin saurayi kuma? Kina nufin har kin iya zance da wani a waya?” Harara ta watsa masa tare da murguda baki, duk a lokaci daya, sannan cikin masifa ta zabura kanshi tana fadin, “Oho, ina ruwanka?” Dariya ya yi ganin yadda ta maida masa da maganar ya ce “Allah ya huci zuciyarki, maida wuqar ba ni na kar zomon ba.” “Kanka ake ji de" Ta sake fada cikin masifa. Sannan ta maida ido kan Mummynta sai a wannan lokacin ta fahimci tun dazu idanunsu yana kan ta. Kunya ce ta kama ta don haka ta yi qasa da kai tana dariyar rashin gaskiya. “Babyna masifa ko? Da har ina tunanin za a ringa cin zalinki ashe kar ki ke kallon mutane? To maza ki je ki yi wanka za ku shiga kasuwa yanzu.” Sun sum ta miqe ta nufi hanyar dakinta don cika umarnin Mominta. Tana jin su Zainab suna yi mata dariya amma ko waigowa ba ta sake yi ba. Bayan fitowarta wanka ne kiran Abdul ya shigo wayarta, yana daf da tsinkewa ta dauka tana yamutsa fuska kamar yana kallon ta. “Matata...!!" Ya kira ta da sunan da ya fi so ya kira ta a karo na uku. Ciki-ciki ta amsa, domin ta fahimci saqon da ya ba Mummy ne ta ce sai dai ya yi haquri yake neman jaddada mata bakinshi da nata. “Matata wai don kawai na ce wa Mummy kada ta bari ki shiga kasuwa sai na zo shi ne ta ce in yi haquri, don Allah na yi laifi kenan? “A’a, ai kai ba ka laifi.” Ta amsa masa cikin gatse. “Yauwa matata. Shi ya sa a kowane bugun daqiqa na agogo nake qara son ki. Ki bari idan na zo sai mu shiga kasuwar tare kin ji ko?” “saboda me?” Ta tambaye shi cikin tsiwa tana yamutsa baki. “Saboda kada wasu mazan su kalle min ke.” “Wadannan dokokin ai ba da ni suka dace ba Modibbo, ka fi ni sanin a inda suka dace. Don haka fita daga yau har bayan bikinka sai inda mai ya qare.” “Daga magana sai cibi ya zama qari?” Ya tambaye ta cikin dariya, domin ya fahimci zallar madarar kishi ne ke cin zuciyarta. Don haka ya maida abin wasa. “Oho maka dai" “Allah ya huci zuciyar matata, ba na son kina vata ranki a kan abinda bai kai ya kawo ba.” Ya fadi hakan cikin rarrashi da salon kwantar da hankalin wacce ake so. Ajiyar zuciya ta sauke wani sanyi yana kwarara a zuciyarta ta ce “Abdul wallahi ina son ka.” “Na sani matata, amma wallahi ina miki so fiye da wanda ki ke min. Ki yi haquri, haka Allah ya qaddara sai na fara auren wata matar kafin ke. Dacin da nake ji a zuciyata wallahi ya ninninka wanda kike ji a taki zuciyar. Ki yi haquri kin ji?” Zuciyarta fes da farin ciki ta ce ”Shi kenan na ji, yanzu dai su Zainab suna jira na a falo, bari in shirya mu shiga kasuwar.” Cikin qunci da qunar zuciya ya yi mata fatan shiga kasuwa da fita lafiya, kishin da yake ji na son Aisha a zuciyarshi sam yana baqin ciki wani namiji ya kalle masa ita. Kawai don dai yana tausar zuciyarta game da aurenshi da Yasmin ne shi ya sa yake bin ta a hankali, yana hadiye kishinshi a kan ta.