← Book details A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 27

Sashe 14

A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A lokacin tana tare da Hidaya tana ba ta labarin duk abinda ya faru cikin farin ciki da murna.
“Yanzu dai kina nufin kin haqura da karatunki kenan gaba daya?”
Hidaya ta tambaye ta da mamakin wauta da rashin hankali irin na qawar tata.
“Qwarai kuwa! Ke kin ga laifina?”
Yasmin ta amsa mata kai tsaye ba tare da shakkar komai ba a cikin zuciyarta.
“Hmmm! Ai ni na rasa ma abinda zan ce. Kawai dai sai in yi miki fatan Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi.”
“Amin qawata, yanzu kika yi magana...”
Waqa mai taken
“A so da kaunar juna zan so a ce ka tausaya min, komai wuya da dadi ni da kai a ce ba za mu rabe ba, a so da qauna da amana zuciya tana son rarrashi... Kawalwalniyar soyayya ta shige min ruhuina...!” shi ne ringing din da ta saka a lambar Abdul. Jin sautin waqar yana tashi ya sa ta lalubo wayar tata tare da sake qawata fuskarta da fara’a.
“Kin ga dan halak ya kira ni. Kamar yana da masaniyar maganarshi muke yi.”
Ta fadi hakan tana kallon Hidaya, sannan ta latsa madannin amsa kira.
Hidaya dai ba baki sai kunne, domin al’amarin qawar tata yana kwance mata kai a duk sa’adda suka had'u. Sai a yau ta sake tabbatar da rashin hankalin Yasmin. Don haka ta yi tagumi tana kallon yadda Yasmin take magana a wayar tana kashe ido kamar Abdul yana gabanta.
“mijina barka da asuba, ina fatan ka wayi gari zuciyarka cike da soyayyar qanwarka kuma matarka nan da kwanaki shida kamar yadda na tashi, zuciyata cike da soyayyarka da dokin ganin ka.”
Sai da ya numfasa a zuciyarshi jin yadda ta iya jero wadannan dogayen kalmomin ba comma, balle fullstop, a tunaninta wai hakan zai burge shi.
Bai amsa tambayar da ta yi masa ba ya ce,
“Kin tashi lafiya?”
Murmushi ta yi kamar yana kallon ta, domin a daren jiya ta gano abinda ke saurin karyar mishi da zuciya, don haka ta amsa masa da cewa
“Na tashi lafiya qalau mijina, ina fatan kai ma hakan?”
“Alhamdu lillahi. Na tashi lafiya har ga ni a ofis na fara aikin da yake gabana.”
“Allah ya taimaka mijina, don Allah ka kular min da kanka.”
Ta fadi hakan a marairaice cikin salon kwantar da kai hade da roqon alfarma.
“Kar ki damu, na gode da kulawarki.”
Ya amsa cikin jin dad'i.
“Aikina ne in kula da kai mijina, balle ma wannan ba komai ba ne a cikin kula da qauna da soyayya da tarairayar da na tanadar maka idan mun yi aure... “
“Uhmmm! Na ce ba...”
Cikin sauri ya katse maganar da take yi jin tana neman bata masa lokaci bai tambaye ta dalilin da ya sa ya kira ta ba.
“Ina jin ka mijina!”
Ta amsa tare da qara maida hankali a kan wayar.
“Wai wane irin ciwuka ne a jikin Abba? su Daddy sun sani kuwa?”
“Dambe suka yi da wani abokinshi, su Daddy sun sani, domin jiya da safe ma Daddy da kanshi ya sake kai shi asibiti aka canza masa wasu magunguna, domin wadanda yake sha sam ba su karbe shi ba.”
“Dambe?”
Ya tambaye ta yana qara jinjina al’amarin a can qasan zuciyarshi.
“Qwarai kuwa, domin yaron da suka yi fadan da shi har yanzu yana kwance a asibiti.”
Ta sake tabbatar masa da hakan don qara gamsar da shi.
“Amma babu wani matakin da daddy ya dauka a kai?”
“A'a! Ya so ya dauki mataki a kan shi wancan yaron da iyayen yaron, sai Yaya Abban ya hana su, a lokacin ne ma ya sanar musu da cewa shi wancan abokin fadan nashi yana can kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.”
Cikin kokwanto a kan maganar tata ya sake tambayar ta da cewa,
“Su Daddy sun je asibitin sun ga shi wancan abokin fadan nasa ne?”
"A’a, shi ne dai ya fada musu hakan.”
“Ok.. toh na gode, bari in bar ki ki huta sai mun yi waya zuwa an jima...”
Cikin salon shagwaba da marairaita ta ce
“Yaya gaskiya ban gaji da jin muryarka ba...”
“Yi haquri yanzu ina tsaka da aiki, za mu yi magana an jima.”
Bai saurari abinda za ta sake fadi ba ya katse wayar yana jinjina al’amarin ciwon Abba a zuciyarshi.
“Yaya ka yi alqawari?”
Ta tambaye shi ba ta da masaniyar ya katse kiran. Fahimtar da ta yi ita kadai take magana ya sa ta yi sanyi riqe da waya a kunnenta, amma ganin Hidaya na kallon ta ya sa ta wayance ta hanyar cewa,
“Ok, bye bye. I love u.”
Tare da sumbatar wayar.
Chapter 14 · 0% Book details