Sashe 26
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Babban gida ne mai matuqar kyau da qayatuwa, Baffa Abubakar daya daga cikin ‘ya’yan Alhaji Bello qanin Ardo ya mallaka wa Abdul a garin Kaduna. Manyan flat uku ne a cikin gidan, daya na maigida Abdul, wanda shi ne a tsakiya, daya na Yasmin daya na Aisha. Sai B.Q, a can daga bayan gidan.
Duk da mahaifin Abdul ya yi mata komai na kayan daki, kamar yadda ya yi ga Yasmin, sai da Mummy ta sake danqaro mata wasu kayan dakin na alfarma. Duk da komai na bikin ya zo a qurarren lokaci, babu abinda ba a yi mata ba na bikin ‘yar gata. Mummy ita ce ta nemi su Rahama da su Safiya a waya ta sanar da su duk abinda ya faru, dukkansu a gidanta suka kwana, har da Baba Jummala suna hirar yaushe gamo. Sun qara kyau da washewa da alama babu wacce take cikin wata matsala.
Fatima ce kawai ba ta samu zuwa ba, don ita tana can Qasar Nijar gurin dangin mahaifiyarta. Amma kowane lokaci suna tare da ita a waya. Bayan su Mummy sun wuce ne suka sake shirya mata d'akuna, sannan suka yi mata sallama kan cewa sai an kwana biyu sa sake leqowa tunda suna gari daya.
“Ni dai ba zan zo ba sai kin gama cin amarci, domin yadda idanun Ango suke a tsattsaye da gani ba kunya zai yi ba…”
In ji Rahma kenan gwanar tsokana, tana gama fadin haka ta ruga da gudu tana qyalqyala dariya.
“Ai kin ci bashi Rahma, zan rama ne…”
Amsar da ta ba ta kenan ita ma dariyar take domin ta san gaskiya ta fada.
A cikin ‘yan kwanakin nan Abdul har tsoro yake ba ta, idan yana kallon ta ko qifta idanu baya yi. Shi ya sa tunda Mummy ta samu labarin umarnin su Aunty Hassana na wucewa da ita gidan miji ranar Lahadi, ya sa ta dauke ta daga gidan ta kai ta gidan babbar aminiyarta tun quruciya aunty Sa’adatu, a can aka nemo kwararriyar mai gyaran jikin amare ita ma ta tare a gidan dare da rana tana tare da ita tana tsuma ta da hadaddun magunguna da turarruka masu tsananin qamshi.
Ko Abdul sai a waya yake samun ta, duk iya nacinsa Mummy ta qi ba shi hasken inda take, bai gan ta ba sai safiyar ranar da za su taho Kaduna.
Ita kanta ganin irin kyan da ta qara komai na jikinta ya sake cika da tumbatsa abin har tsoro ya riqa ba ta. Abdul kuwa ranar da ya ga irin kyau da ta qara yi, duk da a gabansu Mummy ne sandarewa ya yi a tsaye ya kasa magana, har ya so ya ba ta kunya. Duk yadda ya so ya ke6e da ita ta qi yarda da hakan. Wannan kuma yana daya daga cikin shawarwarin Aunty Sa’a, da ta ce kar ta kuskura ya gama luguiguita ta tun a Yola ta ja mishi aji har sai an kai ta gidanshi sannan ya samu abinda yake so.
Yana zaune a kan kujera mazaunin mutum uku, Yasmin tana narke a gabanshi tana zuba masa salo yayin da gaba daya shi kuma hankalinshi yana kan Aisha. Duk yadda ya ke yi mata ishara da ido kan ta dawo gefenshi ta zauna ta qi, har sai da ya gaji ya ce
"Aisha kin ji dad'in zaman gurin nan kuwa? Ki dawo nan kusa mana?”
Murmushi ta watsa masa, sannan ta yi luu da idanunta cikin salon jan hankali ta ce
“Alhamdullahi, nan ma is okey.”
Harara Yasmin ta watsa mata, ita kam ba ta nuna ta damu ba, domin ta san hankalin Abdul yana kanta, don haka ba ta bar murmushi ya qaurace daga fuskarta ba.
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sannan ya yi gyaran murya ya fara da cewa
“Alhamdulillahi, dukkan godiya da yabo da jinjina su qara tabbata ga Allah (S.W.T) Tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W). Duk wata nasiha da nake tunanin zan yi muku babu wadda iyayenmu da kakanni ba su yi muku ba. Abinda zan qara shi ne, ku taimaka ku ba ni hadin kai domin samun zaman lafiya a tsakaninmu. Ku ji ku qi ji, ku gani ku qi gani. Sai kun kau da kai daga duk wani wanda zai zo don kawo zuga a tsakaninku. Zaman lafiyarku shi ne kwanciyar hankalina. Ba zan yarda qananan maganganu da kun ji – kun ji ba. duk wacce ta yi ba dai dai ba za ta fuskanci hukunci daidai da abinda ta aikata. Ni kuma a kullum addu’ata Ubangiji ya ba ni ikon yin adalci a tsakaninku.”
“Amin.”
Suka amsa gaba daya.
“Sai batun raba kwanaki, ya kuke ganin za ku raba kwana ta yadda babu wacce za ta cutu?”
Ya fadi haka yana raba idanu a tsakaninsu.
“Kwana bibbiyu za ka ringa yi a dakunanmu.”
In ji Yasmin kenan tana wani fiffisga.
“Aisha ya kika gani? Kwana biyun ya yi miki?”
Ya tambaye ta yana kallon ta.
Murmushi ta ci gaba da jifan shi da shi kamar ba za ta yi magana ba. cikin yanga ta ce
“Idan kwana biyun ya yi maka ni ma ya yi min. umarninka abin bi ne a gurina ranka ya dade.”
Sai da ya dan dara don jin dadin maganarta, sannan ya amsa da
“Ina ganin a barshi kwanaki biyun, Allah ya ba mu zaman lafiya.”
“Amin.”
Wannan karon Aisha ce kadai ta amsa.
“Sweetheart, ka san dai ni ma amarya ce dal a leda ko? Don haka sai ka fara yi min kwanakina bakwai tukun kafin ka koma daya dakin.”
Dif Abdul ya dauke wuta tun kafin ta aje numfashin maganarta. Ita kanta Aisha sai da ta ji babu dadi, domin ta gama tunanin yau a dakinta Abdul zai kwana. Amma sai ta share komai a fuskarta ba ta nuna rashin jin dadinta ba.
“A tunanina yau kwanakin Aisha sun soma? saboda yau kwanakinki tara a gidan nan Yasmin.” Qarfin hali ya yi ya furta hakan yana kallon ta hankalinshi a tashe.
“Dukda kwanakin nawa tara ai babu abinda ya shiga tsakaninmu, idan kuma ba rashin adalci za ka fara gwadawa tun yanzu ba.”
Ta fadi hakan tana murmushin mugunta, domin ta san ta gama cusguna musu.
Zai sake magana kenan Aisha ta yi saurin katse shi da cewa
"Ranka ya dad'e kamar ta fi ka gaskiya. Ina ganin wannan bai kai wani abun damuwa ba, kwana bakwai ai kamar gobe ne a gurin Ubangiji. Kada ka damu har ni ma ka jefa ni a cikin damuwa ka ji mijina?"
Da ido take mishi nuni da ya bar maganar hakan, don haka ba don ranshi ya so ba ya ce,
“Shi kenan! Allah ya qara had'a kanmu"
Addu’a ya yi musu mai tsayi, sannan ya umarci su je su gabatar da sallar magrib, shi zai wuce masallaci.
Aisha tana band'aki tana wanka bayan ta idar da sallar magrib da isha ta ji motsin shigowarshi cikin bedroom dinta. Kallon shi take gwanin ban tausayi, yana kwance d'ai-d'ai a kan gadonta, ya rungume filo tsam a qirji ya rufe ido.
“Mijina lafiya dai ko?”
Ta tambaye shi bayan ta zauna daf da shi a kan gadon.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bud'e idanunshi ya watso su a kanta. Mirginowa ya yi matashin kai da cinyarta ya danqe hannunta d'aya ya ce
“Matata gaskiya zan cutu idan har ban kwana a kusa da ke ba yau. Amma sai nake ganin ke kamar ba ki damu ba”
Idanunshi sun dan canja kala yayin da yake mata wannan maganar.
“To idan ma na damu ya zan yi? Ganin dai dole mu yi haquri har zuwa kwanaki bakwai shi ya sa na danne damuwar tawa. Kai ma don Allah ka kwantar da hankalinka, kwana bakwai ai kamar gobe ne idan muna da rai.”
Shiru ya yi na dan lokaci, sannan ya fara wasa da wasu sassan jikinta, cikin nutsuwa yake aiwatar da komai dan rage wa kansa damuwa. Dan