← Book details A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 27

Sashe 15

A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda Aisha ta so ta cire damuwa daga zuciyarta hakan ya qi yiwuwa, domin tun jiya da aka yi maganar auren Abdul da Yasmin Abdul ya canza mata. Tunda ya kira ta a mota suna hanyar komawa gida ita da su Daddy ba ta daga ba, sai daga baya ya kira ta yana ba ta haquri tare da kalaman kwantar da hankali bai sake kiran wayarta ba. Ta yi matuqar qoqari gurin boye damuwarta, don kada ta tashi hankalin su Mommynta, kuma ta yi nasarar hakan. Ita ce ma ta taya ta aiki kamar yadda ta saba, suka kammala hada abin kari, amma ba ta ci komai ba sai ta yi wa Mummy qaryar tana azumi. Da mamaki suke kallon ta, abinka da wacce ba ta saba qaryar ba, nan take ta fara sosa kai tana neman shiga rudani. A hanzarce ta miqe ta nufi hanyar dakinta tana fadin “Mummy zan yi wanka.” Ba ta jira amsarta ba ta shige daki ta turo qorar. Wayarta ta dauko duk da ba ta yi tunanin samun miss calls ba. Miss calls din Zainab ta gani qanwar Abdul, har guda biyar tare da baquwar lambar da ba ta san ko ta waye ba. Sai a wannan lokacin ta fahimci Abdul ya kira lambar ta sha biyu na daren jiya. Tsaki ta ja sannan ta bi kiran da Zainab ta yi mata. “Ashe ma kina gida?” Abinda ta fara furtawa kenan bayan ta daga wayar daga can 6angaren. “Ashe ma kin mai da ni shanshani mai qafar yawo kenan?” Aisha ta mayar da tambayar tana dan dariya mai sauti. "A’a, ba haka ba ne, kawai dai tambayar ki na yi.” “Ina zan je da sanyin safiyar nan? Ina nan a gida, ya aka yi?” “Ga mu nan a hanyar zuwa gidanku ni da su Maryam, ki shirya kafin mu qaraso domin fita za mu yi" “Sannu Mummyna, sai kun iso.” Dariya mai qarfi ta kwashe da ita, daga bisani ta ce, “Da dai sannu Aunty Zainab ki ka ce sai in amsa, amma ban isa haihuwar kamarki ba” “Lallai ma yarinyar nan! Zan kama ki ne.” Aisha ta fada tare da jan qwafa mai qarfi. Tana magana da Zainab ta ga kiran Abdul ya shigo, don haka da gangan ta yi ta jan hirar tasu har sai da ta sanar da ita sun shigo layinsu, sannan ta haqura ta katse wayar, bayan ta yi mata fatan isowa lafiya. Kafin ta gama maida numfashi kiran nasa ya sake shigowa, sai da ta bari yana gab da tsinkewa sannan ta daga ta yi shiru ba ta ce komai ba. Shi ne ya gaji da shirun nata ya ce, “Assalamu alaikum ya Habibati...” Kamar ba za ta amsa ba amma sanin ladan da ke tattare da amsa sallama ya sa ta amsa da “Alaikas salam.” Sannan ta ja bakinta ta tsuke. “Afuwa dai matata, na san dai na yi laifi” Ya fada cikin marairaicewa. “Au, da gaske? Laifin me ka yi in taya ka ba da haquri?” Ta fada cikin gatse, domin ya qona mata zuciya tsakanin jiya da yau. "Allah ya huci zuciyarki, amma ai ko za a yi min hukunci ya kamata a ji uzurina tukuna.” “Ai na riga da na san uzurinka Abdul, don haka ba na buqatar ka ba ni haquri, domin ba ka yi min laifi ba.” “Mene ne uzurin nawa? Kada fa ki yi zaton abinda ba haka ba ne?” “Gurin matarka ka je domin ku yi tsare-tsaren abinda za ku gudanar da bikinku. Ko ba haka ba ne?” Shiru ya yi yana mamakin yadda ta fadi inda ya je da kuma wani daga cikin abinda suka tattauna tsakaninshi da Yasmin. “Ni dai kaina bisa wuyana matata, don Allah a kar6i tubana. Wallahi ba qaramin dauriya na yi ba da rashin jin muryarki a daren jiya.” A daidai wannan lokacin su Zainab suka turo qofar dakin tare da sallama, su hudu ne duk da Zainab. Ganinsu bai sa ta daina amsa wayar tashi ba, amma nan take ta yi saurin sauya salon maganarta yadda ba za su fahimci da wa take magana ba. “Au, haba! Da gaske?” “Haba matata, don Allah fa na ce.” “Wannan sunan kamar dai ba da ni ya dace ba. “Na ji kamar hayaniyar mutane sun shiga dakinki, mun yi baqi ne?” “Eh na yi baqi ne.” Ta amsa kai tsaye. “Su waye baqin naki matata, da har kike fadin ke kadai ki kai yi baqi?” “Ba ka sansu ba. ‘Yan’uwana ne.” “Yau dai kina gara ni da yawa matata, ko dan kalaman bakinki masu zaqi kin qi furta min. Ko kina so in yi miki kuka ne?” Sai da ta yi murmushin jin abinda ya fada, sannan ta amsa masa da cewa “Ni kuma sai in yi maka dariya...” Zainab ce ta matso da bakinta kusa da wayar ta ce "Malam don Allah ka bar mana ‘yar’uwa haka, tun dazu ka dame ta ko gaisawa da ita ka qi bari mu yi.” Tana gama fadin haka ta sanya hannu ta katse wayar tana dariya. Ita ma Aisha dariya take yi tana kallon ta ta ce, “Kin san da wa nake magana da har za ki fada masa haka?” “Ko ma dai waye ai kin gama ya gama, haba... tun dazu kina amsa waya kin kyale mu?” Ta fada tana dariya hade da watso mata harara cikin wasa. “Oh, su Smally kenan! Irin wannan kashe murya da yanga ai sai ki sa ya manta a inda ya ke.” "Maryam ce ta fadi haka bayan ta riqe ha6a tana mamakin Aisha. “Ai ni har na yi course, Allah dai ya nuna min lokacin da zan fara soyayya.” In ji Ilham tana kallon idanun Aisha. “Ni kam ai na rasa ta cewa, wai don Allah ko nauyin magana da saurayi ba ki jiba a waya?” Nuratu ta fadi hakan. Dariya Aisha ta qyalqyale da ita, domin maganganunsu sun sa ta dariya sosai. Ta rasa amsar da za ta ba su don haka ta ce, “Bari in kawo muku breakfast. Domin na san irin wannan sammako ko karyawa ba ku yi ba.” “Haba sai ka ce wasu ke? Shi ya sa cikinki yake a dame da gani an san ba kya cin abinci.” Zainab ce ta fadi hakan. “Sha dayan safe ne yanzu fa. Kina nufin ina latti gurin yin break kenan?” “Qwarai kuwa! Suka hada baki gurin fadin haka. “Mu je falo ku gaisa da Yaya Mu’azzam. Da fatan dai kin shiryawa fitar da za mu yi?” Zainab ta tambayi Aisha bayan ta miqe ta nufi qofar zuwa falo. “Ni kam babu inda zan je.” Ta amsa kai tsaye sannan ta miqe ta dauki siririn mayafi ta rufa a kan hular da ta boye asirin dogon gashin kanta. “Ai wallahi ba ki isa ba, fita dole.” Maryam ta amsa mata tana dariya. “Toh, ba sai ku ja ni ba, ku ji ni da yara za su yi min rashin kunya...” Gaba dayansu suka kwashe da dariya, ita kanta da ta fadi maganar sai daga baya ta ji dariya ta qwace mata, domin dukkansu sai dai su zo sa’annin juna a shekaru. Da haka suka sanya kai cikin falon tare da sallama a bakunansu. Yana zaune a dining suna hira da Mummy, da alamun dai breakfast yake yi, domin Aisha ta ga kofi a hannunshi. Idanunshi a cikin nata yana murmushi ya ce "Aunty ashe dai diyar taki tana magana? Sun yi kama da Zainab sosai, don haka ma ta yi tsammanin shima qanin Abdul ne, amma kallo daya ta yi masa ta fahimci bai wuce shekaru ashirin da daya zuwa da biyu ba. Dariya ta yi cikin tsokana ta ce, “Uhmm! Ya ma sunan? Mu’azzam ko?” “Point of correction! Yaya Mu’azzam dai ko qanwata? Domin ko Zainab na girme ta balle ke.” Cikin salon son girma yake wannan maganar. Sai da ta nemi gurin zama kusa da Mummynta ta zauna, sannan ta watsa idanunta a kanshi ta ce “Ai Zainab tana cikin qanne na na uku ne, ka ga kai kuma qanina na biyu kenan! Don haka ni ya kamata ka kira da Aunty Humaira.” “A haba dai, ke ma kin san na girme ki, domin da ganin idanunki ba ki haura fifteen years ba.” Ya katse ta yana dariya. “Sai ka ce wata kai? Da a gobe ne ma kake neman cika sha hudu a shekaru?” Tunda suka fara tafkawa su Zainab dariya suke kwasa, domin sun fahimci tsakanin Aisha da Mu’azzam qafar gaba ce da ta baya, wato kowa yana son girma. Don haka suka yi bakam suna sauraren wanda zai saki ya bar wa daya. “Lalala...tab! Amma yarinyar nan kin ga gadon barcina, Aunty ke ya kamata ki raba mana wannan gardamar. Wai tsakanin ni da Humaira wa ya girmi wani?” Dariya Mummy ta yi amma ta qi tankawa, ganin haka ya sa Aisha ta yi saurin cewa, “ka gani ko? Mummyna kara take maka amma tabbas ta san na girme ka.” “Hmmm! Haka dai kika ce, ji ya zama dole, amma yarda ba ta zama dole ba...” Sai da Aisha ta yi dariya ganin ya sare da wuri sannan ta ce “Ya ka sare tunda wuri haka qanina? Ka ga wannan jumlar maganar taka ta qarshe ta sa na qara tabbatar da cewa ni ke gaba da kai a shekaru, kawai dai ka yi tsawon qafa ne da har kake tunanin ka girme ni.” Dariya ya yi yana kallon dan tsukakken bakinta da har take kirarin ta girme shi, tabbas ya san ya girme ta, amma haka kawai yake a ranshi tana masa kwarjini ba zai iya jan musu mai tsawo tsakaninsu ba. Don haka ya ce, “Sakar miki kawai na yi qanwata, amma ke kanki kin san ni ke gaba da ke a shekaru nesa ma ba kusa ba.” Kiran wayar Zainab da aka yi ya sa Aisha ta yi shiru ba ta qara tanka masa ba, amma a fili take nuna ba ta yarda da abinda ya ce ba. Yadda Zainab take magana cikin girmamawa da ladabi Aisha ta fahimci da wanda take magana a wayar. Tunaninta bai qara tabbata ba sai da ta ji ta ce “Yaya Abdul muna gidan Aunty Aisha ne.” Shiru ta yi na dan lokaci, sai kuna
Chapter 15 · 0% Book details