Sashe 21
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Minti goma shabiyar da isowar Amarya da Ango zuwa gurin ana tsaka da gudanar da taron, babban abokin Ango yana ba da tarihin ango cikin harshen turanci, wani kuma yana gefe yana fassara maganganun da harshen fulatanci. Hankalin Aisha ya yi nisa gurin sauraren yadda Abdul yake sha’awar aikin dan sanda tun yana yaro da yadda har burinshi ya cika na kasancewa dan sanda mai gaskiya da amana.
An fara gabatar da tarihin da yadda soyayyarshi da Yasmin ta kasance ne ta ji ringing din wayarta, abin mamaki shi ne, Abdul ne yake kiranta, kafin ta dauki wayar sai da ta kalli gurin zaman ango da Amaryarshi. Ba ya nan a mazauninshi sai Yasmin ita kadai tana juya idanu dama da hagu.
“Ki sauko ki same ni a gurin motoci, ina jiran ki.” Umarnin da ya ba ta kenan, da yake hall din da ake taron bene ne.
Tana sauka qasa ta ja ta tsaya, domin ba ta san ko a gurin wace mota yake tsaye ba. caraf ta ji an cafke hannunta an janye ta zuwa cikin mota. Ba ta tsorata ba domin ta san idan ba Abdul ba babu namijin da ya isa yayi mata haka.
“Matata ya kamata ki koma gida yanzu.”
Abinda ya fara fada kenan muryarshi a dan fusace.
Kallon shi ta yi na wani lokaci don karantar yanayin fuskarshi. Da alamun an 6ata masa rai, domin bai da walwala ko kadan.
“Saboda me zan tafi? Bayan yanzu aka fara gudanar da komai?”
“Dole za ki tafi yanzu Aisha, domin mafi yawancin samarin gurin idanunsu bai kai kan kowace yarinya ba sai ke. Minti ashirin da biyar zuwanmu gurin mutane shida sun yi min magana a kan in taimaka in shige musu gaba a kan ki. Ban san me zai faru ba idan kika tsaya har aka gama gudanar da komai.”
Ya amsa mata yana numfashi sama-sama.
“Haba!! sai ka ce ni kadai ce mace a gurin bayan duk ga qawayen Yasmin masu digiri?”
“To ke suka gani, kuma a kanki suke magana… kowanne da tsamin bakinshi Abdul na ga tauraruwa a cikin qannenka, don Allah ina kamu daga gare ka babban Yaya…. kunne na ba zai iya sauraren wadannan maganganun ba.”
“Da sauqi ai tunda gani ba dauka ba ne. duk maganganun da za su yi sai gani sai hange.”
“Ganin ma ba za su yi ba, dole ki tafi gida yanzu.” Cikin masifa ya amsa mata da hakan.
“Toh, waye zai kai ni gidan?”
Ta tambaye shi tana tura baki, ba don ranta ya so ba.
Shiru ya yi na dan lokaci, sannan ya ce
“Bari in shiga in turo Mu’azzam ya kai ki gidan”
Har ya bud'e qofa yana niyyar ficewa, ta janyo gefen rigarshi don haka ya dawo ya zauna yana kallon ta.
“Mene ne kuma?”
Ya tambaya cikin kulawa.
Kukan shagwava ta sanya masa wanda babu ko digon hawaye a cikinshi, hade da bubbuga qafa cikin wani irin salo mai saurin rikita zuciyar wanda ake abin domin shi.
Galala ya tsaya yana kallonta, kasa daurewa ya yi, sai da ya kamo hannunta daya yana murzawa a hankali, muryarshi a can qasan maqoshi yake tambayar ta da
“Mene ne Babyna? me kike so?”
“Ni dai babu inda za ka je saidai mu tafi tare....”
Ta fadi hakan cikin shesshekar kuka.
“I’m sorry matata, kin ga ba dad'ewa zan yi ba, kuma komai dare zan zo in same ki a gida”
“Ni dai… ni dai… ni dai a’a! bayan kai ma ina kallon yadda ‘yanmatan Amarya suke kallon ka suna hadiye miyau.”
Dariya mai dan sauti ya yi, sannan ya ce
“Kai matata, kishi ko?”
“Eh din.”
Ta amsa tana tura baki.
“To ai duk yadda mata za su kalle ni bai kai yadda maza suke kallon ki da son ki ba. ke fa zinariya ce a cikin mata, duk lafiyayyen namijin da ya kalle ki dole sai wani abu mai kama da so ya d'arsu a zuciyarshi. Shi ya sa har ba na qaunar in gan ki cikin taron jama'a. matuqar akwai maza a gurin"
Ba zato babu tsammani suka ga an bude qofar motar ta bngaren direba inda Abdul yake zaune. Wa za su gani? Yasmin ce tsaye ta dafe qugunta da hannaye bibbiyu, tana hura iska da bakinta, da alamun gaf take da fashewa.
Kallon-kallo suka yi a tsakaninsu kowa da abinda yake saqa a zuciyarshi.
“Da kyau tsohuwar kilaki, ashe har yanzu kina nan a kan mummunar sana’arki ta karuwanci? A tunanina kin shiryu tunda na gan ki a cikin zuri’armu? To wallahi ina tabbatar miki ke da Abdul sai gani sai hange, qwalelen kare da hantar kura. Kuma idan baki kama kanki ba saina tona miki asiri..."
Bata tanka mata ba kuma bata saki hannun Abdul ba. don ta qara cusa mata haushi ma sai ta ci gaba da murza hannunshi da yake cikin hannunta.
“Yasmin ki saurare ni mana, ki saurara ki ji bayanin da zan yi miki.”
Abdul ne ya ringa fadin haka bayan ya lura muggan kalamanta a kan Aisha sun qi qarewa. Inda Allah ya taimaka ma shi ne, gurin ba gilmawar mutane sosai. Sai tarin motocin da aka yi fakin dinsu a gurin.
“Ka bar ni in gama goge wannan riqaqqiyar karuwar Yaya Abdul, ba na ta taka, domin na san kai ba yin kanka ba ne, ka riga ka fada tarkon wannan annobar. To wallahi ba ki isa ba, Abdul ya yi miki nisan da ba za ki iya kamo shi ba, ‘yar iska tantiriya wacce ba ta da zuciya. Idan kin isa ki tanka kiga yadda zan yi qasa-qasa da ke a gurin nan!”
Sakin hannun Abdul Aisha ta yi domin an zo inda ya dace ta yi magana. Bude motar ta yi ta sauka ta zagaya har inda Yasmin take tsaye, ta ce mortar
“Anya kuwa kina kallon kanki a mudubi? Ke kin san ruwa ba tsaran kwando ba ne, don haka ni da Abdul dole ki saka ido a kan soyayyarmu, ba ki da yadda za ki yi da ni. Ina tabbatar miki da baqin cikina za ki mutu Yasmin. Ki adana mugayen kalamanki domin kin fara kai ni bango, ba don kowa nake daga miki qafa ba sai don Abdul, don haka idan kin isa ki sa shi ya daina so na.”
Tana gama fadin haka ta bar gurin ta ci gaba da tafiya a qasa ba tare da sanin inda ta dosa ba, tana jin Abdul yana qwala mata kira, amma sam ba ta saurare shi ba.
“Hankalinki ya kwanta, tunda kin tunzura ta ta tafi ko Yasmin? To amma fa kin yi a banza, domin kin san ba zan bar ta ta tafi gida ita kadai ba…”
Yana gama fada mata haka ya biyo Aisha da sassarfa har sai da ya cim mata.
“Aysha ki zo mu tafi in kai ki gidan?”
“Na hutar da kai, je ka ji da matarka.”
Ta fada ba tare da ta kalle shi ba.
“Don Allah fa na ce, ina za ki je a daren nan?” Dada
Ya tambaye ta hankalinshi a tashe.
“Na Allah ai ba sa qarewa, ba zan rasa mai taimaka min ba.”
Hannunshi ya sanya ya finciko hannunta da qarfi, taga-taga ta yi za ta fadi da hanzari ya yi mata masauki a qirjinshi, ya sanya hannunshi duk biyu ya rungume ta.
Ture shi ta yi ta qwace jikinta, sannan ta zame ta tsuguna a qasa ta saka masa kuka mai tsuma zuciya.
Bai saurare ta ba, illa kiran Mu’azzam da ya yi a wayarshi ya fito waje ya same shi. Mukullin motarshi ya amsa ya ja hannun Aisha tana kuka ya saka ta a ciki. Sannan ya yi masa umarnin ya kai ta gida.
Har suka isa gida ba ta tanka wa Mu’azzam ba, ba ta kuma daina kukan ba, sannan ba ta daina sauke ajiyar zuciya ba. tana ganin kiran Abdul yana shigowa wayarta, amma ta qi dauka, daga qarshe ma sai ta kashe wayar gaba daya don har a lokacin haushin sa take ji. Kuma ta yi alqawari a ranta ba za ta sake halartar duk wani taro da za a yi na bikinshi da Yasmin ba har a gama bikin.