Sashe 25
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Qwanqwasa qofar falon da aka yi da qarfi ya sa Aisha ta zabura za ta shige dakinta ta kulle kamar yadda ta tsira a ‘yan kwanakin nan. Duk baqin da za a yi masu zuwa ganin amaryar Abdul ba ta yarda su gan ta, sai dai ta kulle kanta a daki ba ta sake fitowa har sai ta tabbatar sun tafi.
Hannunta Mummy ta danqe sannan ta yi mata alamar kada ta tashi da idanuwanta. Yayin da daddy ya je ya bude qofar tare da ba da izinin shigowa ciki.
Idanun Aisha suna qasa, sallamarshi da ta jiyo ya sa ta dago da sauri tana kallon shi. A zuciyarta kuma mamaki take yi.
“Lafiya a daren nan!?”
Da mamakin su ma suke kallon shi sai Mummy ce ta yi qarfin halin tambayar sa.
“Abdul lafiya kuwa a daren nan?”
Sai da ya sami guri ya zauna, sannan ya dan yi murmushin da da gani bai kai ciki ba ya ce
“Lafiya qalau.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauke, sannan ya yi dariya ya ce
“Wallahi ka kada min hanjin ciki, yanzu fa tara da rabi na dare. Wane abu ne zai fito da danyen ango waje idan ba qwaqqwaran dalili ba.”
“Hmmm! Daddy kenan! Ni wallahi a da da ba ni da auren ma na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa, kana ganin yadda kullum nake ramewa kamar wanda ake d'iba ana miya?”
Ya fadi hakan yana qoqarin lalubo idanunta don ta san da ita yake yi. Su ma da yake ba yara ba ne duk sun fahimci inda maganganun nasa suka sa ba. ita kam ko kallo bai ishe ta ba, sai ma tsaki da ta yi qasa-qasa.
“Haba Abdul, kada ka ba ni kunya mana, kamar ba jarumin dan sandan nan da na sani ba?”
In ji Mummy kenan tana xan murmushi.
“Hmmm! Allah dai ya yi mana magani… daman Ardo ke son ganin Aisha, shi ne ya umarce ni in zo in tafi da ita.”
Sai a yanzu Aisha ta daga kanta tana kallon shi cikin tuhuma, a zuciyara addu’a take Allah ya sa dai ba qarar ta ya kai ba.
“Toh fa! A wannan daren yake son ganin ta?” Daddy ya tambaya yana mamaki.
“Qwarai kuwa, domin cewa ya yi qafata qafarta.” Ya amsa da tabbacin idanunshi suna cikin nata.
“Allah ya sa dai ba laifi ta yi ba?”
Mummy ta tambaye shi, fuskarta na bayyana damuwa.
“Ni ina zan sani? Idan ta je can ta ji.”
Ya amsa kai tsaye yana daga kafada.
Kiran Ardo da ya shiga wayar Daddy yana sake tabbatar da son ganin ta yanzu ya sa suka yanke duk wasu tambayoyi nasu. Mummy ce ta dauko ma ta hijabi sannan suka yi matan fatan dawowa lafiya su kuma suka kama hanya.
“Qara ta ka kai kenan?”
Ta tambaye shi cikin masifa, domin duk hange da tunaninta ta kasa gano dalilin kiran da Ardo ya yi mata.
“Me kike ci na baka na zuba? Idan mun je ai za ki ji dalilin kiran.”
Ya amsa yana qara maida hankalinshi a kan titi.
“Idan ma qara ta ka kai, to wallahi ka sani babu wanda qullunshi zai qara ruwa sai kai. Domin duk abinda aka yi min a kanka zan rama.”
Bai ce komai ba, domin shi kansa bai san dalilin kiran da Ardon yake yi mata ba, har ya kwanta a gidanshi Ardon ya kira shi wai ya je yanzu ya dauko ta su taho tare.
Kai tsaye falon ganawa da bakin waje suka nufa, domin sunga takalma a qofar falon. Sallama suka yi a tare.
Daga can ciki aka yi musu umarnin shiga. Wa za ta gani? Aunty Hassana da Aunty Hussaina zaune a kan darduma sun yi shiga irin ta Larabawa. Da sassarfa Aisha ta qarasa ta rungume su tana murnar ganin su. Abdul can gefe ya raka6e yana gaida su cikin jin kunya da nutsuwa.
“Amaryar Abdul-Ahad.”
Aunty Hassana ce ta fadi hakan, tana murmushi.
Nan take Aisha ta yi rau-rau da ido za ta yi kuka.
Cikin tsawa Aunty Hussaina ta ce
“Mene ne haka? Duk kin bi kin wani tashi hankalinki kamar ba mai ilimi ba? idan kuma ba kya son Abdul ne ai sai mu sa shi ya sauwaqe miki.”
Ta tambayi Aisha tana kallon ta tare da zare mata anu.
“Hussaina ki yi mata a hankali mana”
Sannan ta mai da kai ga Aisha,
“Kin ga Aisha ba dad'ewa za mu yi ba, yanzu za mu tafi. Abinda ya kawomu shi ne domin mu fahimtar dake abinda ba ki sani ba. kin ga da saninmu aka daura aurenki da Abdul, da ba mu amince ba tun kafin a daura za mu zo mu hana daura auren. Kuma ki daina ganin laifin Abdul, ba shi da laifi ko kadan, haka ma Ardo. Tun farko Allah ya qaddari ranar Asabar za ki zamo mata ga Abdul, domin sai da suka nemi zabin Allah a kan daura auren ko barinshi. Sannan suka daura. Bincike a kan wadanda suka kashe Sadiya kuma yana daf da cimma nasara, ke dai kawai ki taya shi da addu’a, ki kwantar da hankalinki. Komai kika gani ya samu bawa, muqaddari ne daga Allah. Ba na so in sake jin kin yi wa mijinki rashin kunya. Ki zauna da kishiyarki lafiya”
Tana gamawa Hussaina ta dora da cewa,
“Kuma batun ki zauna a gida har sai bayan ya gama binciken sannan ki tare a dakinki mun soke shi, duk ranar da zai bar garin nan ku tafi tare da mijinki, domin zai fi jin dadin gudanar da aikinshi idan kina kusa da shi. Ke dai ba jahila ba ce, daidai gwargwado kina da iliminki, ki bi duk hanyar da kika san za ki qara soyayyarki a zuciyar mijinki kin ji ko?”
Kai kawai Aisha ta daga alamar ta ji a kunyace.
“Abdul ka yi haquri da Aisha, ka yi juriya a kan duk wani hali da za ta nuna maka domin yarinya ce, amanarta muka danqa maka. Muna taya ka addu’ar Allah ya ba ka ikon riqe amanar da muka danqa maka.”
“Amin summa amin.”
Ko kunya bai ji ba ya amsa da hakan.
“Shiga cikin gida ka yi mana sallama da Ardo za mu wuce.”
Yana fita suka ci gaba da janyo hankalinta da nasiha mai ratsa jiki, sannan suka ba ta wani farin ruwa a gora suka ce ta kai wa Mummy ta shanye a lokaci daya, ta ci gaba da addu’a in Allah ya yarda za ta sami haihuwa.
A gabansu Ardo ya danqa mata sadakinta naira dubu talatin, kunya ta kama ta shi kuma ya dage lallai sai ta amsa, domin haqqinta ne. Daman a gobe yake shirin aikawa a kira ta ya yi mata nasiha, sannan ya damqa mata. Su suka sanya baki ta kar6a sannan su ka yi mata sallama suka tafi.
Taqaitacciyar nasiha Ardo ya sake yi musu, sannan ya umarci Abdul ya maida ta gida daga can shi ma wushe nashi gidan.
Suna mota a hanyar komawa gida kowa da saqe-saqen da yake yi a zuciyarshi.
“Matata don Allah ki yi haquri, ki daina sha re ni haka nan.
Wallahi ni kadai na san wahalar da nake sha, ko isasshen abinci ba na iya ci.”
Ya fada ma Aisha bayan ya kama hannunta da hannu daya, yana tuqi da daya hannun.
“Na haqura, ni ma don Allah ka yafe min duk abinda na yi maka.”
“Kada ki damu, tun kafin ki yi min laifi na yafe miki ko kin manta da hakan? Allah na gode maka da ka fahimtar da matata abinda ba ta sani ba.”
Ba su isa gida ba sai qarfe goma sha daya da minti goma na dare, bai jima ba ta kora shi zuwa gida duk da bai so tafiya ba.
*** *** ***
Suna zaune a falon Abdul ranar Litinin da misalin qarfe shida na yamma, baqin da suka kawo Amare daga Yola duk sun tafi da misalin qarfe biyu na ranar. Tana cikin matsanancin farin cikin da fuskarta ta kasa 6oyewa. Har da Mummynta a cikin wadanda suka yi mata rakiya gidan miji, sun hada su da Yasmin sun yi masu nasiha mai ratsa zuciya da sassan jiki, sai fatan Allah ya ba su zaman lafiya.