← Book details A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai da ya bari mai gadi ya bude qofar ya shiga da motar ciki sannan ya bi ta dan qaramin qofar gidan ya shiga ciki ya tsaya can kusa da fulawoyin gidan, gurin da idan wanda ya fito daga motar bai yi waige ba ba zai iya ganin shi ba, amma daga inda yake tsaye yana iya ganin komai da yake faruwa a gurin motar Abban.
Sai da maigadin ya maida qofar get din ya kulle hade da sanya kwad'o ya datse, gurin motar Abba ya nufa da gudu ya bude qofar direba.
A buge ya fito da Abba domin kasa tsayawa da qafafunshi ya yi sai da taimakon maigadin, fiye da rabin jikin Abban yana jingine da jikin maigadin. Sai da suka shige cikin dakin Abba sannan Abdul ya fito daga maboyarsa ya bi bayansu har zuwa jikin tafkeken windon da ke jikin falon Abban. Da yake dare ne kuma haske ne tar a cikin falon, don haka yana ji kuma yana ganin duk abinda yake faruwa.

Tun daga tsakiyar falon Abba ya fara kwara amai don haka maigadin ya tsugunar da shi a qasa yana jera masa sannu, har sai da ya tabbatar Abba ya gama aman. Zagi Abba ya fara surfa masa cikin maye da buguwa amma hakan bai sa maigadin ya fasa aiwatar da abinda yake yi ba.
Kayan jikin Abban ya cire T.shirt da wandon jeans, ya bar shi da singileti fara kar da gajeren wando. Bai gaji ba ya sake tarairayar Abban har zuwa cikin dakin barcinsa ya kwantar da shi a gado, ya janyo babban bargo ya rufa mishi. Sannan ya kashe wuta mai haske ya kunna mara haske sosai. Falon ya dawo ya tattare hannun rigarshi, abinda ya fara yi shi ne lalube aljihun wandon da ya cire a jikin Abban ya kwashe duk kudaden ciki ya zuba a nashi aljihun, a gefe ya ajiye kayan, sannan ya nufi bandaki ya dauko tsintsiya da ruwa a bokiti ya kwashe aman tas ya goge gurin.
Turaren ya dauko ya feshe falon gaba daya don dakushe qarfin warin giyar da ya mamaye falon. Yadda maigadin yake kwashe aman hankalinshi kwance kuma ba tare da qyanqyamin ba shi ya tabbatar wa Abdul ba yau ne karo na farko da maigadin ya fara irin wannan aikin ba.

Agogon wayarsa ya kalla, qarfe daya da minti goma sha biyu na dare. Fitowa ya yi daga inda yake tsaye, ya nufi qofar falon Abba kai tsaye, A daidai lokacin kuma maigadin ya gama komai har ya kwaso kayan jikin Abba da ya cire ya nufo waje don ficewa daga falon.
Cak ya ja ya tsaya jikinshi na karkarwa lokacin da ya hada idanu da Abdul-Ahad. Murmushi Abdul ya jefa mishi, sannan ya yi saurin cewa,
“Inusa har yanzu ba ka kwanta ba?”
Sosa qeya ya yi cikin alamun rashin gaskiya qarara, murya na rawa ya ce
“Ina barci ga wanda yake aikin gadin wasu ranka ya dad'e? Alhaji Abba ne ya dawo gida baya jin dad'i don haka na taimaka masa har ya samu barci.
A yanzu ne nake shirin komawa bakin get don ci gaba da aikina.”
Dariya Abdul yayi kawai, don qara kwantar wa da maigadin hankali, ya ce,
“Ni ma tun dazu da muka yi sallama da Yasmin ta shiga cikin gida ban samu tafiya ba, ka san al’amarin qarfen nasara ba tabbas! Ganin dawowar Abba ya sa na yanke shawarar kwana a nan in ya so gobe sai in wuce da safe. Ka je ka ci gaba da aikinka ni zan kwana tare da Abban. Allah dai ya biya ka Inusa irin wannan dawainiya da kake da mu.”
Farin ciki ne ya mamaye tsoron da ya cika zuciyar Inusa maigadi. Kai tsaye ya amsa addu’ar Abdul cikin farin ciki da cewa
“Amin ranka ya dad'e, ku ma Allah ya saka muku da alkhairi, domin ba don ku ba da yanzu ina garari a gari cikin marasa aikin yi. Bari in koma bakin aikina, mu kwana lafiya ranka ya dad'e”
Yana gama fadin haka ya kama hanyar ficewa daga falon cikin sauri.
Idanu Abdul ya raka shi da shi, a zuciyarshi yake dariyar yadda maigadin ya shiga rudani daga ganin shi. Kai tsaye bedroom din Abba ya wuce don ganin halin da yake ciki. Yana kwance dai-dai a kan makeken gadon da ya mamaye fiye da rabin dakin. Barci yake cikin kwanciyar hankali, harta bargon da maigadin ya lulluba mishi ya yaye shi can gefe daya.
Da wayar hannunshi yake haska cuwukan da ya gani kwance a jikin Abba a gurare daban-daban. Mamaki ne ya kama shi, da ganin ciwukan dai ba a daren wannan ranar aka ji su ba. Amma kuma ba a dade da jin ciwukan ba domin danye ne sharaf, wani irin ruwa-ruwa suke fitarwa musamman na wuyanshi wanda nuna alamun yakushi ne sanadinsu, domin sun yi layi-layi alamun yatsu. Wutar lantarki mai haske ya kunna domin ya qara karantar ciwukan da kyau. Duk da cewa an kunna wutar bai sa Abba ya motsa ba, domin barcin da yake yi da taimakon ababen gusar da hankalin da ya sha ne.
Kanshi ne ya kara daurewa, domin sai a yanzu ya gama fahimtar ciwukan duk kusan sanadin samuwarsu daya ne. kallo daya za a yi ma duk wani ciwo da yake jikin Abba a fahimci yakushi ne.
“Da waye Abba ya yi dambe aka yakushe mishi sassan jiki haka?”
Abdul ya tambayi kanshi da kanshi duk da yana da tabbacin amsar bazaiyi wuyar samu a gareshi ba. Tsawon mintuna goma sha biyar yana tsaye a kan Abba yana qare masa kallo, daga bisani kuma sayya kashe wutar dakin ya barshi a duhu a yanda ya tarar da shi da farko, kai tsaye ya fice daga falon ya nufi gurin maigadi, a zuciyarshi yake addu’ar Allah ya sa ya samu qarin bayani daga gurinshi.
Yana kishingide a kan benci a dakin da yake kwana amma ba barci yake yi ba. Motsin da ya jiyo ana taba qofar dakinshi ya sa ya fito da sauri da adda a hannunshi, yana muzurai.
Ganin Abdul a tsaye kyam ya sa jikinshi ya yi sanyi, sai daga bisani ya yi qarfin halin fadin
“Ranka ya dad'e lafiya kuwa? Ko wani abu kake nema?”
Chapter 12 · 0% Book details