← Book details A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Ya nake jin ana magana a kan mijina ne? Allah ya sa dai ba wata ce take neman yi min qwacen miji har gida ba.”
Yasmin ce ta yi wannan maganar tare da watsa idanunta a kan Aisha, tana mata kallon da ta rasa gane kanshi.
“Ok... ko shi ne Abdul din da na ji Yasmin tana fadin tana da buqata ta matsu a daura musu aure?” Aisha ta tambayi Zainab, sannan ta fakaici idanunsu ta watsa wa yasmin kallon
“Ki iya takunki”
“Qwarai kuwa shi ne Smally...”
Zainab ta amsa mata kai tsaye ba tare da shayi ko shakkar Yasmin ba.
Gaba daya ‘yanmatan haushin Yasmin suke ji, don gani take kamar ta fi kowa a cikinsu, musamman da Ardo ya zabe ta a matsayin mata ga Abdul.
“Oho dai, duk dan baqin ciki sai dai ya mutu, ni da Abdul mutu ka raba, takalmin kaza. Qwalelen kowacce mayya”
Yasmin ce ta fadi haka cikin harzuqa, tana maganar tana watsa harara dama da hagu.
“Haba ‘yar’uwa! Kar ki ba da mata mana, ina abin yake wai maye ya ci jariri? Ko kina nufin ba ki yarda da kanki da irin son da ya Yaya Abdul yake miki ba ne?” Hankalin Aisha kwance take maida mata da martani cikin hikima da wayau ba tare da ta bari sauran ‘yanmatan sun fahimci ‘yar tsamar dake tsakanin ta da Yasmin ba.
“Babu abinda wata ‘yar iska za ta gwada min sai iya karuwanci da bin bokaye don sato zuciyar Abdul, hadadden saurayi irin Abdul, idan ba tsoro ba ta fito fili mu gwada mana.”
“Zaman duniya ai iyawa ne ‘yar’uwa... kana koyon laifi ba don ka aikata shi ba sai don duk ranar da ka tsinci kanka a cikin masu aikata laifin ka san hanyar da za ka kare kanka. Ina ganin har yanzu ba ki gama karantar yadda ake cin ribar zaman duniyar ba. Idan kuwa hasashena gaskiya ne, kin ga kina da buqatar ki sauke duk wani girman kai ki zo ki zauna mu ‘yan’uwanki mu karantar da ke, idan kuma kika tsaya kallon ruwa, kina ji kina gani kwado zai yi miki qafa...”
Gaba daya ‘yanmatan dakin suka kaure da shewa suna fadin,
“Zancenki dutse Smally, kukan kurciya dai jawabi ne...”
Da ganin yadda suke maganar farin ciki ne fal a zuciyoyinsu. Domin yau Aisha ta goge musu bak'in cikin da Yasmin take k'unsa musu.
Har shiru ta yi na wasu ‘yan mintuna tana jinjina maganganun da Aisha ta ragargaza mata, cikin laluben hanyar da za ta bi ta rama abinda ta yi mata ta ce
“Idan ana maganar ‘yan’uwana a cikin zuri’ar gidan nan ai ba a sakawa da irinki karere.."
Karaf wannan maganar a kunnen Gwaggo Dije uwargidan Ardo, don daman duk cafter da suke yi suna zaune ne a cikin falonta.
Mari mai qarfi ta kai wa bakin Yasmin da sam idanunta sun rufe ba ta lura da shigowar gwaggon cikin dakin ba.
“Diyar da Ardo ya daga hannunta ya gabatar a zuri’ar gidan nan kike kira da karere? Ai son da ake yi wa wacce kike kira karere ya ninka wanda ake yi miki fitsararriya mara kunya. Ta fiki komai da komai, sakara kawai shashasha.”
Da sallama suka shigo cikin falon, sannan suka janye hannun Gwaggo zuwa kan kujera suka zaunar da ita.
“Yi haquri Gwaggo! Allah ya huci zuciyarki.” Mahaifiyar Abdul Hajiya Binta ita ce ta fara ba Gwaggo haquri cikin tausasan lafuzza.
Mummyn Aisha kuwa harara ta watsa wa Yasmin kamar za ta rufe ta da duka. Sannan ta mai da idanunta kan tsohuwar ta ce
“Ki yi haquri Gwaggo. A yanzu Yasmin ganin ta take daidai da kowa, tana ganin ta isa fadin duk abinda take so, kuma a duk lokacin da ta ga dama”
A zafafe ta d'ago kanta ta ce
“Ai sai ta ba da himma, amma ina mai tabbatar mata wannan hanyar da ta biyo ba mai 6ullewa ba ce. Abdul yana da damar auren mata uku bayan ita, don haka ta bi duniya a sannu.”
Haushin maganganun Gwaggo ya sa Yasmin ba ta gama sauraren fadan da suke mata ba balle har ta bada haquri, ta dafe bakinta da ya fara tasowa saboda marin da Gwaggo ta yi mata ta fice daga dakin tana guna-guni.
Sai da suka gama kwantar wa da tsohuwar nan hankali sannan Mummy ta umarce su da su tashi su yi sallah. Don Daddy ya ce idan ya dawo masallaci za su tafi gida.

Tana yafa mayafi bayan sun idar da sallah Gwaggo ta kalli Aisha da fara’a ta ce
“Aisha ba za ki tsaya ki ci abincin gidan kishiyoyin naki ba? Ko tsoro kike kada mu taru mu yi miki duka?”
Murmushi kawai ta yi don rashin abin cewa, saboda sam ba a taba yi mata irin wannan wasan na jika da kaka ba, sai bayan shigowarta cikin zuru’ar su Abdul.
Ammi mahaifiyar Abdul ce ta tare mata wasan da cewa,
“Haba dai Gwaggo, ai tausaya muku take kada ta tsaya Ardo ya kasa cin abincinku,, saboda kallon ta kawai ya isa ya kosar dashi. Kuma na tabbata idan tana gidan nan gaba dayanku Ardo zai daina shiga harkar ku sai tata.”
“Ai duk wannan kyan nata ko kusa ba ta kama qafata ba.” Ta fada tana dariya mai qarfi.
“Mun dai gano ki Gwaggo, kawai kishi ne ke damun ki, don kin gan ta sabon jini...”
Wannan karon Zainab ce ta amsa sannan ta janye hannun Aisha suka fice daga dakin suna dariya.
Kowane daki na gidan sai da suka shiga, Aisha tai musu sallama cikin karamci da jin dadi suke amsawa. Gaba d'ayansu tambayar ta suke kan yaushe za ta je ta yi musu kwana biyu? Matan yayyen Mummy maza da yayyinta mata duk tambayar Mummy suke da cewa
“Aishatu diyar taki ba ki ba da aronta ta yi wa mutane kwana biyu ne?”
Da dariya take amsa musu da cewa tana nan zuwa.
Aisha ta samu kyautukan kudi masu yawa daga mazan iyayen su Abdul har matan qannen Ardo maza kuwa suka yi ta mata wasan jika da kaka, sannan suka yi mata addu’a da fatan Allah ya yi mata albarka.
Su Zainab fadi suke
“Wayyo Smally, kamar kada mu rabu.”
Dariya ta qyalqale da ita, sannan ta ce,
“Rabuwa ai dole ne, duk mai son gani na ai ya san gidanmu.”
Musayar lambobin waya suka yi tsakaninta da matasa maza da matan gidan, sannan suka rabu a cikin farin ciki da qaunar juna.
Yasmin dai har Aisha ta bar gidan ba ta sake ganin qeyarta ko na mahaifanta ba.
Suna shiga mota a karo na barkatai ta sake jiyo vibration din wayarta a cikin jakarta. Da tsaki ta janyo jakar ta ciro wayar, duk idanun Mummy suna kanta. Abdul ne, daman ta san sai shi din.
‘Xan anace.”
Ta fada a zuciyarta, gaba d'aya haushi da takaicinshi ya cika mata zuciya, gani take kamar shi ne Yasmin da take neman zame mata qarfen qafa a rayuwa.
“Baby yau kuma mijin naki kike kira dan anace?”
Dady yai murmushi, yana jan motar yayin da ita kuma tana zaune a sit din baya yana kallon fuskarta ta cikin madubi.
Haushi da kishi ya sa ta fashe da kuka don ji take wani abu ya tsaya mata a maqoqwaro ya hana ta hadiye miyan, idan ba kukan ta yi ba sam ba za ta sami sauqi a ranta ba.
Sun kusa isa gida don haka a cikinsu babu wanda ya tanka mata har suka isa. Maigadi ya bude musu get, Mummy ce ta kama hannun Aisha har zuwa falo ta zaunar da ita a kan kujera, Daddy kuma ya kulle motar bayan ya dauko mata jakarta da wayarta zuwa falo.
“Shalelen Daddy har yanzu kukan bai isa ba ne?” Daddy ne ya jefa mata tambayar bayan ya zauna a kan kujera idanunshi na kan ta yayin da ita kuma ta ci gaba da rera kuka mai ban tausayi.
“Baban baby ni ina ga kawai mu je mu yi wa Ardo bayani yanzu ba ta son Abdul, don haka a janye maganar aurensu in ya so sai Allah ya ba ta wani mijin saurayi, wanda ya fi Abdul-Ahad komai da komai.”
Mummy ce ta fadi hakan a fusace tana kallon fuskar Daddy tana jiran abinda zai ce.
Qirjin Aisha ya buga dam, ba shiri ta tsaida kukan nata kamar daukewar ruwan sama. Bakinta a ture ta kalli Mummy ta ce
“Ni dai ban ce ba na son shi ba...”
Dariya suka kwashe da ita gaba daya, ita kuma kunya mai tsanani ta kama ta, don haka ta boye fuskarta a tsakanin qafafun Mummy tana dan murmushi domin ta fahimci tsokanarta suke yi.
“Toh, idan kina son shi ai babu amfanin kukan ki Babyna, domin na tabbata Abdul ko mata uku zai aura ba zai ta6a juya miki baya ba. Kuma ba zai taba iya daina son ki ba. Domin da bakinshi ya tabbatar min an halicci zuciyarshi ne da soyayyar Aisha. Kin ga daina sonki yana nufin daina bugawar zuciyar Abdul-Ahad.”
Chapter 10 · 0% Book details