← Book details A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 27

Sashe 1

A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A Dalilin
DA NAMIJI

3

NA
Fareeda Abdallah

Tana zaune daga ita sai dan kamfai a gaban dan tsamurmurin Bokan da ta kira shi da sunan
“Arne na Kan Tudu”
Ta sha matuqar wahala kafin ta samu isa gare shi, motarta a can bakin titi ta bar ta, sannan ta yi tafiyar tsawon awa biyu tana hawa kan tudun don isa gurin
"Arne na Kan Tudu”.
Ta zagaya guraren bokaye har biyar duk amsarsu iri daya take kasancewa da bokan da qawarta Mariya ta kai ta gurin shi.

Tana da tabbacin buqatarta za ta biya, tazo inda za a share mata hawaye. amma bokan yana da sharudda kafin a isa gurinsa. Shi yasa ba ta zuwa gare shi sai ta ga buqatarta ta sha gaban kowane boka da take harka da shi. Amma ta san da ta kawo mishi matsalarta yake magance mata. Babu wata buqata tata da ya gaza biya mata. kowane
Daya daga cikin sharuddanshi shi ne, sharuddanshi
“Za ki daina bin duk addinin da kike kai har na tsawon kwanaki uku kafin ki je gare shi.
Na biyu kuma tun daga gurin da kika ajiye abin hawanki za ki tube kayanki tsirara ba abinda za ki sanya a haka za ki fara hawa kan tudun da bokan yake zaune. Tafiya ce kuma ta tsawon awa biyu.
Daf da isa gurinshi za ki ga wani dan kamfai rataye a ganyayyaki sai ki dauka ki sanya, sannan ki qarasa gurinshi.

Kallon ta yake da manyan idanunshi jajaye masu firgita qaramin yaro, qaton kan da yake d'ore a d'an siririyar wuyarshi shi zaisa a yi tunanin a kowane lokaci kan zai iya rinjayar jikin. Ihu mai qarfi ya qwalla bayan ya gama kallon qwayar idonta. Busashhen hannunshi mai nuna alamun rashin jini ya buga a qasa yana babbaka dariya, nan take hoton kyakkyawar fuskar Aisha ya bayyana.
“Kin zo a kan wannan, kuma kin je gurin mugaye har biyar sannan kika zaiyarce ni, ko ba haka ba?”
Ya tambaye ta cikin tsawa da daga murya yana watsa manyan idanunshi a kanta.

“Haka yake mugu dan muguwa jikan mugu, tatta6a kunnen mugwaye. Wadancan sun kasa saboda rashin qwarewarsu a kan mugunta shi ya sa na zo gare ka shugaban mugwaye. don na san babu abinda zai gagare ka dan gidan mugu.”
Ta amsa cikin daga murya kamar yadda ya yi mata tambayar, tare da yi mishi kirarinshi. Duk wannan yana daga cikin qa’idojinshi.
Idanuwanta tsaye suke kyam a kan fuskar Aisha tana murmushin mugunta, don tana ganin lokaci kadan ya rage mabudi da mukullin rayuwar Aishan ya dawo hannunta. Ta sha alwashin maida Aishan kadarar da za ta samar mata da biliyoyin kudi, sannan daga qarshe ta lalata rayuwar yarinyar saboda wahalar da ta sha kafin ta samu biyan buqatarta a kanta.

Dariya ya qyalqyale da ita, sa6anin dariyar dazu da ya yi ta cikin babbar murya. Wannan karon dariyar siririya ce mara dad'in sauraro.in
“Tabbas za ki samu biyan buqata idan ba ki manta da qa’idojina ba"
Ya fadi hakan yana kallon ta, bayan ya katse dariyar tashi kamar an yi ruwa an dauke.

“Ban manta ba mugu dan muguwa, jikan mugu. Tatta6a kunnen mugwaye.... a kwana biyu....”
Ta daga yatsunta guda biyu tana kallon qwayar idanunshi.

“Yauwa muguwa, rayuwarki a mugunta za ta qare. matuqar kina tare da mugu a kwana biyu buqatarki za ta biya. Yarinyar da kanta za ta neme ki idan kika ga haka buqata ta biya. Sai ki kawowa mugu budurwar da zai sha jininta a matsayin ladan aikinki, amma wannan aikin naki yana da sharadi muguwa.”

“Na amince da duk wani sharadi matuqar zan sami biyan buqatata mugu dan gidan muguwa, jikan mugu, tattava kunnen mugwaye.”

“Kamar yadda wadancan mugayen suka sanar da ke yarinyar tana da shiri a jikinta, don haka idan ba mu samu damar shiga jikinta ba mugu zai dauki ladan aikinshi a jikinki, ta hanyar tsotse jinin jikinki gaba daya.”
Ba taji wani dar ko tsoron abinda mugu ya fada a matsayin sharadi aikinta ba, domin tana da tabbacin babu abinda zai gagare shi a kan al’amarin Aisha.
Da qwarin gwiwa da na zuciya ta baro gurin Mugu bayan ta ajiye masa dan kamfanshi a inda ta dauka. Ba ta damu da tsirarun motocin da suke wucewa suna kallon ta a lokacin da take tsaye tana maida kayan jikinta ba. Tana gama sanya kayanta ta ja motarta a guje ta bar gurin tana dariya da farin cikin nan da kwanaki biyu buqatarta za ta biya.
* * *
Kamar kowane lokaci, da sallama ta amsa wayar, fuskarta dauke da qayataccen murmushi kamar yana kallon ta. ba kamar yadda ta saba jin muryarshi ba, yau muryarshi a matuqar sanyaye take. Hankalinta a tashe take tambayarshi da cewa,
“Lafiya kake kuwa Abdul? Me yake damun ka?”
Sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan ya amsa mata da cewa
“Aunty wai don Allah ya kuke so in yi da raina ke da diyarki ne? Yau kwana daya da yini daya sam ta qi daukar wayata, rabon da in ji muryarta tun shekaran jiya da muka rabu da ita a gurin Ardo. Idan wani laifi na yi mata bai kamata ta hora ni da rashin jin tattausar muryarta ba. A da da ban samu Aisha ba soyayyarta mai sauqi ce a zuciyata, ina da jarumta da kwarjini da nake iya ci gaba da aikina, duk da son ta ne danqare a zuciyata, amma a yanzu da na same ta bai kamata a wahalar da ni ba. Wallahi ba ni da wani jarumta a kan Aisha, ina son ta son da ban san iyakarshi ba. Don Allah ku tausaya min kada son Aisha ya zama ajalina.”
Ya qarasa maganar yana shesshekar numfashi, da alamun gaf yake da ya saka kuka a kowane lokaci.

Tausayinsa ne mai tsanani ya rufe ta, har ga Allah ba ta da masaniyar Aisha ba ta daukar wayarsa. Tana cikin yin wannan zancen zucin ta hango fitowarta daga dakin da yake a matsayin nata, ta yi kwalliya da riga da siket na kayan turawa, kai tsaye gurinta ta nufo tana murmushi. Ba tare da ta amsa mishi ba ta katse wayar ta maida hankalinta gaba daya kanta tana maido mata da martanin murmushin da take mata.
Dan nesa da ita ta zauna tana jiran jin abinda zata ce, don ta lura bakinrta akwai abin cewa.
“Babyna zo nan.”
Ta umarce ta tare da nuna mata gefen ta a matsayin gurin zamanta. Kusa da ita ta dawo ta zauna amma maimakon ta zauna a kusa da inda take zaune a kujera sai ta zauna a qasa kusa da qafafuwanta. Tare da maida hankalinta gaba daya kanta.
“Babyna, me Abdul ya yi miki ba kya daukar wayarsa?"
Ta tambaye ta tare da qura mata ido don jin amsar da za ta ba ta. kunya ce matsananciya ta kawo mata ziyarar bazata, don haka ta sunkuyar da kai qasa tana matsa ‘yan yatsun qafarta.
“Mummy ni fa kunyarshi nake ji, idan na dauki wayar tashi me zan ce mishi?”
ta tambaye ta bayan ta yi jarumtar korar duk wata kunya da take neman hana ta sakewa da wacce ta dauke ta tamkar diyarta da ta haifa.
“Haba Babyna, wace irin kunya kuma? Ki saki jikinki ki nuna masa soyayya tsaftatacciya, kin manta yadda sirikin nawa ya ke da farin jinin ’yanmata ne? Kina son wata ta qwace shi daga gareki ne? Idan ya kira ki a waya ki dauka, ki amsa mishi da sanyin muryar da zai isar da saqon so a gare shi. Ki nuna mishin tsantsar son da kike mishi, ki dage ki qara dasa soyayyarki a kowane lungu da saqo na zuciyarshi. Yadda babu wata mace da za ta samu damar dasa mishi tarkon soyayyarta. Ki nuna mishi kulawa, da tarairaya, da qauna da soyayya yadda zai ci gaba da zama naki ke kadai. kinji Babyna?”
Sakin baki kawai ta yi tana kallon Mummy yadda ta zauna tana warware mata duk yadda za ta yi ta sake riqe Abdul gam a hannunta. Duk abinda take fada haddace shi take yi a cikin qwaqwalwarta, don haka ta gyada kai cikin gamsuwa da duk maganganunta bayan ta fahimci ta kai aya a maganarta.

“Yanzu ki tashi ki je ki kira shi, sannan ki ba shi haquri cikin marairaita da shagwa6a akan rashin daukar wayarshi da ba kya yi. Tare da alqawarin hakan ba zai sake faruwa ba.”
Umarnin da ta da ba ta kenan bayan ta gamsu da yadda ta fahimci darasin da ta yi mata. Ba ta yi sanya ba ko musu gurin aikata umarninta.

Missed calls 25 ta gani a wayar tata, daga lokacin da ta bar wayar a kan mirrow zuwa falo gurin mummy. Tana danna kiran lambarshi wani kiran na shigowa don haka ta gyara kwanciya a kan gado ta rungume filo a qirjinta, sannan ta danna ok don amsa kiran tare da fadin
"Hello....” cikin sanyin murya da salon jan hankalin wanda aka yi abin dominshi.
“Wash Allah, zuciyata....”
Amsar da ta samu kenan daga can bangaren. Sannan ya fara sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanu hade da dafe daidai saitin zuciyarshi da yake jin kamar son Aisha zai fasa ya fito fili kowa ya gani. Yanayin yadda yayi maganar da saukar ajiyar zuciyarshi da take jiyowa tangaran a kunnenta ya sa ta lunshe ido tana jin wani sanyi da nishadi yana kwarara duk wani sashe na jikinta.
Qara rungume filo ta yi tsam-tsam a qirjinta, abinda yake yawo a jikinta ya sa ta kasa amsawa daga bangarenta sai shi ne ya katse shirun nasu bayan sun dauki kusan minti biyar a haka ya ce
“Aisha zan mutu, wallahi ba ni da lafiya...”
A rude ta fara jan
“Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un.” Domin a yadda ya yi maganar tabbas ta fahimci bai da lafiyar. Cikin alamun muryar da ke gaf da fashewa da kuka ta ce.
“Me yake damun ka Abdul? Don Allah kar ka mutu ka bar ni...”

“Soyayyarki ce Aisha, son ki yana neman ya yi ajalina Babyna... ki tausaya min don Allah...”
Chapter 1 · 0% Book details