← Book details A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yana kwance a dakin da yake a matsayin nashi, bayan ya fito daga wanka misalin qarfe goma sha biyu na dare, ya kira wayar Aisha fiye da sau goma amma ba ta dauka ba, har zai yi addu’ar barci sai ya yi tunanin, idan ya yi barci ba tare da ya nemi Yasmin don jin ko tana da damuwa bai yi mata adalci ba. don haka ya latsa kiran lambar wayarta, ringing daya, a na biyu ta dauka. Jin yana jiranta a dakinshi ya sa ta dauki rigar barci ta sanya ta qara feshe jikinta da turaruka masu qamshi ta nufi dakinshi.
Da farko kuka ta saka masa sannan ta fara fadin maganganu a kan irin rashin adalcin da take ganin an yi mata.
Bai bari qorafin ya yi tsawo ba ya ja ta zuwa jikinshi ya rungume sannan ya zura harshenshi a cikin bakinta. Take ya kashe duk wani qorafi nata tuni ta ba da kai bori ya hau. Ta fara qoqarin mayar mishi da martanin irin wasannin da yake yi mata.
“Ashe dai abin ba a shekaru ba ne…” Bai san lokacin da zuciyarshi ta ayyana masa hakan ba, domin ji ya yi komai da komai na jikin Aisha ya ninka na jikin Yasmin girma da daukar hankali.
Duk yadda ta so su zarce da wasannin ya qi yarda da hakan, a qarshe ta haqura tana rungume a faffadan qirjinsa har barci mai nauyi ya kwashe ta. Shi ma da yake tattare yake da gajiya barcin ne ya yi awon gaba da shi. Zuciyarshi cike da tunani da soyayyar Aisha.
Qarfe hudu daidai ya farka, a hankali ya zame jikinsa daga na Yasmin, bandaki ya shiga ya yi wanka sannan ya dauro alwala. Nafiloli ya fara gabatarwa, ya yi addu’o’i masu tsawo a kan Allah ya ba shi ikon yin adalci a tsakanin matanshi, sannan ya yi addu’a mai tsawo a kan samun nasarar kama wadanda suka kashe Sadiya.
Zai fita masallaci don sallar asubahi ya tashe ta amma yana ficewa ta sake maida kai ta kwanta. Yana daga cikin matsaloli manya da Yasmin take fama da su rashin gabatar da Ibada akan lokaci (Allah ya shirya).
Bai fito daga masallaci ba sai qarfe bakwai da rabi na safe, yana komawa gidan ya gan ta dai dai a kan gado tana sharar barci, alamu sun gwada qarara ba ta yi sallah ba. Sake tashinta ya yi yana tsaye a kanta har ta sauka ta shiga bandaki sannan ya canja kayan jikinshi daga jallabiya zuwa shadda ya dauki mukullin motarshi ya wuce zuwa gidan Ardo bayan ya bar mata dan short note, inda ya tabbatar za ta iya gani idan ta fito bandakin.

* * *
Su Aisha suna zaune a falo ita da Daddy misalin qarfe tara na daren ranar Talata, sun gama cin abincin dare. Qoqarin suke su qara kwantar wa da Aisha hankali don haka duka kalaman nasu nasiha da rarrashi ya fi yawa. Tun da aka daura auren duk ta bi ta tsangwami kanta ta qi sakin jikinta, shi ne abinda yake daga hankalinsu.
Abdul kuwa har yau da ake kwanaki hudu da zamowarsu ma’'aurata ta qi ba shi hadin kan da yake buqata, balle har ya yi mata bayanin da za ta fahimce shi ta daina ganin laifinshi. Ta zame mishi kurma qarfi da yaji, zai zo ya zauna bayan gaisuwa ba ta qara yarda wata magana ta shga sakanin ta da shi. Duk surutun da zai yi ba ta um bare um-um. Sai dai idan ta gaji ya fice zuciyarshi cike da damuwa, shiyasa maimakon a gan shi ya yi qiba ya yi kyau, a matsayinshi na ango, sai dan wuya yake yi.
Hatta Yasmin ta rasa gane kanshi, tun ranar daurin aure da ‘yan wasanni suka shiga tsakaninta da shi ba ta sake samun ko makamancin haka ba. ta yi kuka ta yi rarrashin ta yi masifar, amma duk a banza. Duk magungunan da turarrukan da aka hada mata tana amrfani da su amma bai shiga dakinta balle ta sa ran za su yi tasiri. Shi ya sa duk ta qosa su tattara su koma Kaduna, gurin aikinshi, kuma gurin iyayenta, tunda ta samu labarin ba yanzu Aisha za ta tare ba, amma ya ce sai ranar Lahadi, lokacin an yi kwanaki takwas da daura auren kenan.
Chapter 24 · 0% Book details