Sashe 7
A dalilin Da Namiji Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hajiya Mariya ita ta ci gaba da amsar daidaikun baqin qawayensu masu zuwa gaisuwa. a ranta ta yi wa kanta alqawarin daina harkar neman jinsi da bin bokaye da malaman tsibbu gaba daya. (Allah ya ba ta iko, Ubangiji ya shiryi sauran masu yi gaba daya, amin).
*** *** ***
Aisha na tsaye gaban madubi tana shafa hoda a fuskarta ta jiyo vibration din wayarta da ke gefen gado. Sanin mai kiran nata ya sa sai da ta dan ja aji tana gab da tsinkewa sannan ta latsa madannin amsa kiran tana fadin
“Hellooo....”
Murya qasa-qasa ya amsa kamar wanda ya farka daga barci. Cikin shagwava da marairaita ta ce,
“Mijina daga wayewar garin yau zuwa yanzu qarfe takwas da rabi na safe ka kira wayata sau goma sha biyu, Wai ni mene ne ne?” ta yi tambayar tana tura baki kamar yana kallon ta.
“Ke ce matata... ke ce wallahi! son ki ya hana ni rintsawa dukda yau lahadi ya kamata in kai sha biyu na rana ina barci”
“Ni dai babu ruwana, jiya fa muka dawo daga Kaduna, amma za ka wani ce ni ce na hana ka barci...”
“To ai ni ba na gajiya da kallon ki, ko son jin tattausar muryarki, bayan kina ganin har wani rowarki Mummy ta ringa yi min.”
“Allah ya huci zuciyar mijina, ai Mummyna ba ta son ka wahalar mata da diya ne.”
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, “Duk ranar da na dauke diyar ba sai in ga wanda zai yi min rowarta ba?”
Dariya ta yi kawai bakinta ya yi mata nauyi ta rasa irin amsar da zata bashi, don haka ta yi shiru tana dan dariya mai sauti da har yake iya juyota ta cikin wayar.
“Yi dariya dakyau yarinya, yanzu ai lokacin ne. Kin gama shiryawa ne?”
“A’a yanzu dai powder nake shafawa.”gama
Ta amsa kai tsaye tana kallon powder da take ajiye a gabanta.
“Wani irin powder kuma matata? Ke da na ce kada ki yi kwalliya don kada wasu maza su kalle min ke dukda dai na san hakan ba mai yiwuwa ba ne.”
“Su waye wasu maza mijina, taro ne fa na family daga qannenka sai iyayenka ka ga ai babu bare balle har a kalle maka mata ko?”
“Su qannan nawa ba maza ba ne? Ni fa wallahi ina tsananin kishin wani ya gane min mata, kuma kar ki kuskura ki yi musu dariya balle har su yi sha’awar ki.” Ya fadi hakan cikin fada.
“So kake su dauke ni a matsayin miskila mai girman kai? Kada ka manta taro ne da Ardo ya hada don gabatar da ni a matsayin daya daga cikin ‘ya kuma jini ga danginku, ka ga dole in sanya murmushi a fuskata ko don su karbeni da hannu bibbiyu.”
“Wane irin kaya za ki sanya?” Ya tambaye ta duk da haka bai sassauta maganarshi ba.
“Doguwar rigar shadda da mayafinta.”
Ta amsa kai tsaye zuciyarta na neman 6aci da fada-fadan da yake mata.
“Ban yarda ba.... ni wallahi ban yarda ki yi wannan shigar ba matata, kawai ki nemi kayan da kika san sam ba za su yi miki kyau ba, wannan qaton hijabin Mummyn naki za ki sanya, ban yarda kina budewa wasu garada fararan haqoranki ba. In ban da Ardo ya hana ni zuwa taron da duk wannan kallon da za su yi miki bara suyi ba...”
Haushi da masifar da yake neman ya tsiro mata da shi wai duk don yana kishinta ya sa ta katse wayar ta jefa ta a kan gado. Sai da tayi minti goma tana maida numfashi da jujjuya maganganun Abdul a zuciyarta. Sannan taci gaba da shirinta, kuma bata fasa sanya kayan da tayi niyya ba.
Tana ganin kira har sau goma sha daya, a kira na goma sha biyu ta dauka rai a 6ace ta ce
“Wai meye ne? Idan kuma masifan ne ba ka gama ba sai ka dora daga inda ka tsaya...”
Tana jin yadda yake sauke ajiyar zuciya sauri-sauri, muryarshi da dan rawa-rawa ya ce
“Allah ya ba ki haquri matata, ni wallahi ba masifa nake miki ba, kawai son ki da nake yi ne ya haddasa min tsananin kishinki a zuciyata, don Allah ki yi haquri”
“Na ji!!!”
Amsar da ta bashi kenan ta sake katse wayar.
Bai yi fushi ba ya sake kiran wayarta. Sai da ta tsinke sau biyu, sannan ta dauka a karo na uku. Shiru ta yi ba ta ce komai ba don har a lokacin ba ta sauko daga dokin zuciyar da ta hau ba.
“Matata ba ki haqura ba ne? Don Allah na ce ki yi haquri...”
“Na haqura, amma gaskiya ka 6ata min rai Abdul, irin kalamin da ka yi amfani da su gurin bayyana min salon kishinka suna nuna kamar ba ka yarda da son da nake yi maka ba ne, kana tunanin a gaban idonka ne nake son ka a bayan idonka zan ci amanarka ne? Ba ka yarda da ni ba ne?”
Tana gama jera masa wadannan tambayoyin ta fashe da kuka, domin idan ba hawayen ta zubar ba ba za ta samu sauqin quncin da ya mamaye zuciyarta ba.
“Oh my God! Matata don Allah ki yi haquri, wallahi ban yi wadannan maganganun don in bata zuciyarki ba, don Allah ki yi haquri kin ji matata, ko kina son ni ma in yi kukan ne?”
sai da ya dau tsawon lokaci yana rarrashin ta har ta daina kukan gasken ta koma yin na shagwa6a, tana bayyana mishi irin son da take yi masa sannan ta haqura.
“Ni a haka ma zan je gurin taron da hawaye a fuskata tunda dai na fahimci mijina bai son kwalliyar.” Ta fada tana turo baki kamar yana kallonta.
"Wanke fuskarki ki yi kwalliyarki matata, ai na san babu wanda ya isa ya qwace minke daga gare ni.”
“Ina son ka mijina...”
Ta fada cikin salon jan hankali dan tabbatar da saqonta ya isa gare shi. Sai da ya dau tsawon minti daya yana maida numfashi sannan ya ce
“Ni ma ina tsananin son ki matata.”
Da haka suka yi sallama da shi ta gyara fuskarta cikin sauri don ta san Mummy tana can falo tana jiran fitowarta.
Tun suna mota ba su isa gidan ba Ardo ya kira Mummy yana tambayarta sun iso ne? Sanar da shi ta yi ga su nan a hanya sai ya ba ta umarnin idan sun isa ta tura Aisha dakin da yake ganawa da baki na waje. Don haka suna isa kai tsaye can falon ta nufa ba tare da ta shiga cikin gidan ba.
Takalman da ta gani a qofar falon shi ya tabbatar mata da baqi a ciki, don haka ta qara gyara zaman mayafin kanta da ya yi matuqar dacewa da shaddar jikinta, ta yi sallama gami da dakatawa a qofar tana jiran a amsa. Sannan a ba ta umarnin shiga cikin falon.
Gaba xayansu suka amsa, sannan ta ji muryar Arxo yana fadin,
“Bismillah shigo daga ciki.”
Kanta a qasa ta kutsa cikin falon, sannan ta nemi guri can nesa da su ta zauna. Gwiwoyinta a qasa ta gaida Ardo sannan ta maida fuska kan wadanda ta gani a cikin falon ta fara gaishe su.
Idanunta cikin na mahaifan Yasmin, jifan ta sukai da wani mugun kallo. Sam sun kasa amsa gaisuwar da ta yi musu, ita kuma tun daga gaisuwa daya ba ta qara ba, illa musayar kallo da suke yi a tsakaninsu.
Yasmin a fili take watsa wa Aisha harara, su kuma iyayenta suna jifan ta da kallon tsana a fakaice. Ba ta rama martanin kallon da Yasmin ko iyayenta suke mata ba don ta san idanun Ardo suna ganin duk abinda ya ke faruwa.
“Gyara zamanki da kyau Aishatu”
Ardo ya fadi hakan idanunshi suna kanta. ta zauna da kyau sannan ta saukar da qwayoyin idanunta zuwa qasa tana sauraron Ardo.