Sashe 5
Zynah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
babu wanda ya kaisa jin dadi duniya". an yasa yanzu yake sheke ayarsa da zynah, gashi zynah tada abu daya, koda kwana zaiyi a kanta bata magana, domin itama abinda takeso ne". Hjy tayi gudun garane ta fa i ma sago, domin yanzu irin da sukeyi, sai Allah, amma kuma, inda a cikin gida suke dole su rage wani abu, an ma har yanzu zynah bata gama kilewa ba, wani abin bakura ke koya mata, gani harda rashin boko ke cutarta, yasa bakura duk lokacin daya tare da ita, yana kokarin koya mata A.B.C.D, bayan ta iya, sannan ya fara koya mata two letter world three letter, da shike mai kwakwalwace, har ta iya, yanzu kam ta fara iya rubuta sunanta da nashi". Wani lokaci kuma idan anzo karatun, mancewa akeyi da shi a kama soyayya". Kullum na barawo, rana daya ta me kaya, abinda sa ido irin ta hjy, bayan bakura ya sallameta akan zaije kasuwa, yana zuwa bayan yaran shago su bu e shagon, tunda bakura yabar kasuwa, kai tsaye suleja ya nufo, gun zynah, be koma akan lokaci ba, domin duk lokacin daya tsicci kansa tare da zynah, mancr komai yakeyi". Bayan azahar hjy ta shirya zuwa kasuwa, tun a bakin kofa ta fara zargin bakura baya shago, bata gasganta ba saida ta shiga ciki, ganita yasa duk yaran shagon suka mike, sukazo suka gaisheta a ladabce,bayan su gaisa ne, hjy take tambayar ina bakura?" Magana in shago yace, tun safe daya shigo, ya sake fita bai dawo ba har yanzu, take hjy ta juya harshe tana fa in wlhy idan har ysnzu suna tare da shegiyar yarinyar nan ne, saina bata masa rai". Yau da gobe ya wuci wasan yaro, ashe yaron shagon yaji abinda hjy ke fa i ". Hjy na juyawa yace, yau ne kawai ya fara haka ko yau ne kawai?" Daya tuno irin alkhairin da bakura keyi bamu yasa shi rufa masa asiri, yace yau ne kawai hjy". Ba tare data tanka masa wayar ta ta ciro daga cikin jaka ta fara kiransa, bakura yana gani kiran hjy yaji gabansa ya fa i, hjy tayi kira har sau uku amma bakura bai daga wayar ba". Lokacin da bakura yaga kiran hjy, lokacin yana kan network yana sending messages ne ya hanasa daga wayar". Tsaki kawai hjy tayi, ha e da juyawa, cikin bacin rai tabar gurin". Yana sauka yaje yayi wanka, yau be da e ba kamar sauran ranaku, yana zuwa shago suka sanar mata da zuwan hjy". Shiruuu kawai bakura yayi yana tunanin ta ina zai fara?" Bayan ya koma gida, yana shiga, kai tsaye falon su hjy ya nufa, lokacin suna zaune dukkansu falo, gani yadda hjy ta daure fuska yasa, yasa bakura zuwa kusa da ita ya zauna, bayan ya gaisheta fuska a daure tace, bayan shago ina kake zuwa?" Ina ko zanje hjy bayan, shigo? Yau ma da kikazo baki sameni ba, motatane nakai gyara, sabida kwana biyun nan naji birkin motar tana rawa, yau ma wlhy dan Allah ya kiyayene" sannan kuma lokacin da kika kirani ina masallaci ina sallah, sann wayata tana slent, yasa banji kiranki ba, amma dan Allah kiyi hakuri insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba". tsakani dah da uwa sai Allah, nan hjy ta ije fushin da takeyi". Daga nan bakura yaci daga da gashinsa, ciki kuwa yananan yana girma, yanzu haka cikin zynah wata hudu kenan". *~~~~~ ~~~~~~* *KUNCI* Me hali baya fasa halinsa,bayan rakiya ta zubar wa zainab da wacce cikin, sai gashi taje ta sake wani, Wannan karon ma, haka sukaje inda aka basu magana suka zuwar da wacce, cikin dare rakiya ta dauki magani batawa zainab, a cewarta kafin safe, cikin ya fita, tunda zainab tasha magani jini yake zuba mata, har asubs, rakiya bataso kowa ya sani ba, amma gani zainab nayi kamar zata mutum, yasata kiran sadiya, tazo ta taimaka mata". Gani irin jini dake zubowa daga jikin zainab yasa sadiya fahimtar abinda ake ciki, amma kama bakinta tayi tai shiru, tunda basu fa i mata ba, ita kuma tayi alkawarin bazata tambayesu ba". Hankalin malam shehu ya tashi matuka, sabida yadda yaga jini ke kwararowa daga jikin zainab". Babu irin tambayar da baiwa rakiya ba, amma taki fa i masa, cewa kawai takeyi, yayi hakuri ya kwantar da hankali, bataso ya yanke hukunci cikin fushi, kuma koma menene ya bari har zainab ta samu lafiya sannan sai ta fa i masa". Ana sanar asuba, rakiya da sadiya suka dauki zainab zuwa asibiti, da'kar da taimakon Allah aka samu ragowar cikin ya fita, kwanata biyu, kuma duk sadiya ke kwana da ita, sannan aka sallamesu". Bayan kwana biyu lokacin girki ya dawo hannu rakiya, cikin dare, rakiya ta tashi zaune, tagumi tayi tayi shiruu kamar me tunanin, juyawar da malam shehu zaiyi yaji bata kusa dashi, da sauri ya mike ya zauna". Gani yadda tayi tagumi yasa malam shehu tambayar lafiya". Kai kawai ta ka e ha e da cewa babu komai, da kar malam shehu ya lallabeta, kukan mana ficci tasa mata, tana fa in, naji zan fa i maka amma dan Allah inaso kayi min alkawarin koda na fa i maka, bazaka dauki kowani mataki a kaiba, sabida tariga ta rokeni, dana rufa mata asiri, na yafe mata, kuma kada nabari koji wannan maganar". Kaga idan har kata da zance, ya nuna ban rufa mata asirin ba kenan, kamar yadda nayi mata alkawari". Nan malam shehu yace yaji kuma ya amince, ba zai tada maganar ba". Nan rakiya ta kwashe karya ta shrya wa malam, har kukanta winwinwin, akan zuban jini da tayi, sariya ce, ta zuba mata guba a cikin abinci, ina fitowa bayi yana tana zubawa, koda nayi mata magana sai tace nayi hakuri na yafe mata, sannan kuma na rufa mata asiri kada na bari kaji maganar". Yadda take kuka sai taban tausayi, sabida yasa nace mata insha Allahu bazakaji maganar ba, to kuskuren da nayi, a lokacin ban dauki abincin na zubar ba, sabida yadda naga tayi nadama, na dauka har cikin zuciyarta ne, ashe ba haku bane, kawai muna kwance cikin dare, naji yarinya na kukan ciki, kafin nawi wani yunkuri sai ga jini". Malam shehu dake zaune yace, anya kuwa, sadiya zata iya aikata hakan?. Kodai gani kake kamar shirri nayi mata?" Ni bance haka ba, amma lamarinne abin dubawa ne". Yan har kokwanton abinda sadiya zatayi kakeyi? Bayan kafi kowa sanin tun daga lokacin da Amina tabar gidan nan, sadiya ta janye jikinta bata shiga harkan kowa, to wlhy bari kaji, yadda Amina tabar gidan nan, sadiya bataki kowa ma yabar gidan ba, niba hatta kai da kanki, kuma bari kaji idan har bazaka dauki mataki akan hakan ba, ni zan dauka, domin inaji ina gani bazan zauna a kasheni ba". Gsni yadda ta birkice mada yasa malam shehu cewa yanzu me kikeso ayi?" Nidai banaso a karota a gidan, domi har ga Allah tausayi take bani, idan ka koreta a gidan da wanne zataji? Ga rashin miji ga kuma rashin yarinya, girki kawai zata daina yi, tunda ta nanne take niman halakamu, idan muyi sai takawo kwanu asa mata ita da yara, idan ma magani zatasa, wannan kuma kanta zatayi wa?". Koda girki ya zagayo kan sadiya, tana idar da sallar la'asar ta share gindin murhu ta gyara ko'ina". Tana cikin kwashe sharan kenan taga rakiya tazo tana ha a icce". Da mamaki tace rakiya yaya haka kuma?" Ba tare data fasa abinda takeyi ba, kuma bata aga ba, tace jeki ki tambayi malam da kike zamansa, amma nida amsar tambayar a nan". Bakin kofa ta koma ta zauna tana kallo ikon Allah, bayan isha lokacin malam yanacin abinci rakiya dake zaune kusa dashi tana yi masa fifita, sadiya tazo ta duka a gefe, bayan ta gaishesa tace dan Allah malam magana nakeso muyi dakai". i ina jinki". Shiruuuuu tayi kamar bazata magana ba, amma kuma da taga baida niyyar tashi, dole yasa tayi maganar ". Yau nice da girki, kodai mantuwa kayi?" Ba mantuwa nayi ba, ina sane, nayi haka, kuma daga koda bakizo kin tambayi dalili ba, ni zanzo da kaina, daga yau bazaki kara dora sanwa a gidan ba, rakiya ce zata rika yin abinci, idan tayi zata zuba maki keda yaranki". Ido kawai sadiya tabi malam dashi, har yakare magana". Har ta bu e maki zatayi magana, malam shehu ya dakatar da ita, da banason jin komai, idan kuma ba haka ba, nida kece a gidan nan". Sadiya na kwallo ta mike zuwa aki, kuka sadiya tayi sosai, akan irin hukincin da malam shehu ya yanke a kanta batare da tasan dalili ba". Ita kuwa rakiya tun daga lokacin ta fito da sabon salo, wani lokaci koda malam bai kwanta da ita ba, idan har malam zai shiga akinta jansa da hira takeyi,wanda saiya dauki lokacin, bayan wasu awanni ko mintoci sai kaga ta fita da buta taje wanka, dan dai kawai ta cusa wa sadiya bakin ciki". Tun abin yana damu sadiya har tazo ta saba, sabida, duk da ba girki takeyi ba, amma malam shehu baya bari girkinta ya wuce ba tare daya bata hakkinta ba". *~~~~~~ ~~~~~~~* _*JABI*_ Bayan wata biyu daddy ya dawo daga Germany, duk suna zaune a falo suna hira, cikin wasa da dariya, me dauka da jin dadin gani mahaifinsu, duk cikinsu babu wanda yayi tunanin sanar wa daddy abinda ake ciki". Da safe bayan bayan goma, duk suka shigo akinsa gaida sa, kamar yadda suka saba, bayan su gama gaisuwa, har su mike hjy ta dakatar da bakura, su sauran suka fita". Gwiwa bibiyu bakura ya duka a gaban iyayensa". Hjy ta meda dubanta ga alhj dake zaune cikin girmamawa ta kira sunan sa, da alhj". Amsawa yayi da na'am, yana kallonta". Kallo da yake mata ne, yasa hjy dukan ta kanta kasa, shiru tayi ta rasa ta ina zata fara masa bayani". Gani tayi shiru yasa alhj cewa ita sauratanki". Nan ta fara kame-kame, ha e da wasa da yatsun hannunta, alhj yace kiyi magana mana Khursum". Sannan ta fara da, da farko dai kafi na fara magana, zan fara da baka hakuri, sabida nasan duk kokarin da nakeyi akan yaran nan ba gani kakeyi ba, haka ma bai faru ba, yaya aka