Sashe 17
Zynah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi tana zaginsa, da safe ma haka, bakura bebi ta kanta ba, tashi yayi yaje ya shirya, yana gamawa yaje ya ha a tea, falo ya dawo ta zauna yana sha, adyra na fitowa suna ha e ido, cikin jin haushi tace oh!! An dai ji haushi". Mudai ji haushi, domin na tabbata bani kadai naji haushin ba, au na mance bance maki yaya gajiyar jiya ba, ko za'a bani na kara ne?". Dariya ya kwashe mata dashi, jin haushin hakan yasa adyra inda take shiga banan take fita ba". Ashe duk abinda takeyi hjy na bakin kofa tana jinsu, jin zagin yayi yawa ne, ita kuma nazata iya jure jin hakan ba,da sauri ta juya ta koma da baya". Tunda hjy ta koma gidan irin maganganun da adyra ke fa i wa bakura ya dami hjy, yadda abin ya dameta ji tayi kamar ta kira hjy Ashe ta sanar da ita, sai dai kuma idan tayi haka tamkar da tona wa kanta asirine, dole yasa ta bar maganar a zuciyarta yaci gaba da cikinta, domin ko daddy taki fa i mawa,abinda sufi kusa da adyra akan daddy". Shi kuwa bakura, al'amarin adyra ya daina damusa, domin idan da sabo yariga daya saba"Shiyasa yanzu idan ya shigo gida in har be takareta suyi fa a ba, bayajin da Cikin satin nan daddy zai dawo, sabida zasuje gida maiduguri, shida bakura, akan maganar auren su am'abywa da Yah-na, gakan yasa daddy yace wa bakura ya shirya yana isowa zasu tafi gida". Tunda adyra taji labarin tafiya gida, tun daga lokacin ta fara lallabarsa, sabida tanason zuwa gida". Da shike bakura ya gano, duk yadda tabi haka shima yake binta, da haka har daddy ya dawo, ranar tafiyarsu yayi, zynah ce kawai ya sallama amma banda adyra, har suka isa, gani yamma yayi be dawo gida wayarta ta dauko ta kirasa, bakura yana daga, saida suka gaisa, ha e da tambyarsa ya kasuwa, a lokacin ne yake sanar da ita yana maiduguri, take tasa ihu e da hurgi da wayar"""".. ~~~~ ~~~~~ *kunci* Tun bayan komawar su zynah abuja zazzabin malam shehu ya tashi, da haka har ya kaisa ga kwanciya". Bayan kwana uku da kwanciyarsa cikin dare ciwo yayi zafi, malam shehu yayi murkusu-murkusu har rai yayi halinsa,shiruuuu da rakiya taji ne har karfe takwas na safe malam shehu bai fito ba, yasa taje dubashi, tun kafin ta karisa bakin fokar take kwa a masa uwar kora, amma shiru, hakan ne yasa ta karasa akin da sauri". Tana shiga ganinsa tayi yayi wani irin kwanciya, take gabanta yayi mummunar fa uwa, da sauri tayi kansa, koda tabasa shiru tayi,take tasa wani irin ihuuuu tana fa in na shiga uku na lalace". ",Abinka da kauye, take gida ya cika da jama'a har da sadiya da yaranta duk suzo, ba'a dauki lokaci ba aka yiwa malam shehu wanka aka shiryasa kamar yadda addinin musulinci yace ayi, bayan an kaisa ne, sadiya ta kira Bakura ta sanar dashi rasuwar malam shehu, salati yayi ya sanar wa ubangiji, sannan yace insha Allahu suna nan zuwa". Bayan su gama waya da sadiya ne yaje ya sanar wa daddy, washe gari bayan en'gidan mazajen su Am'abuwa da Yah-na suka neman aurensu, kuma aka basu, ha e da sanya masu rana, washe gari suka baro maiduguri zuwa abuja". Bayan su iso ne, daddy yasa bakura yaje yazo da zynah, saida yayi mata nasiha sosai sannan ya sanar da ita rasuwar malam shehu". Itama salati tayi, sannan yayi addu'ar Allah ya jikansa, daddy yace ta shirya gobe sanmako zasuyi". Bayan fitar su, hjy ke tambayar daddy, a cewarta bata fahimci maganar da sukeyi ba". Nan daddy ya sake fa i mata, daga nan yace ta shirya suje tare"".. Da sauri tace, wahhhhh!! Allah ya kiyaye, saidai wata ba niba, gani daddy ya matsa ne ta amince zata". Bayan su koma gida bakura yaje gidan adyra, tana zaune a bakin gado, bakura na sallama bata amsa masa ba, gani haka yasa be biye tata ba, shima zauna , nan yake sanar da ita rasuwar malam shehu baban zynah". Tamkar bada ita yake magana ba, yana gama fa i ya mike ha e da sallamarta, domin tafiyar asuba ce zasuyi". Tsaki kawai tayi masa, ba tare da tace komai ba, har bakura yakai bakin kofar fita falo, da sauri adyra ta mike da cewa yanzu sabida Allah kayimin adalci kenan? Kwananka nawa baka gari kuma yau da dawowarka kace zaka sake wani tafiya? To nan dai gaskiya bazan yarda ba sai dai kasan abinyi". Murmushi bakura yayi sannan yace, to yanzu me kikeso ayi?" Sai dai ka fasa tafiyar". Shi kawai kike so?". Eh". To kinga yanzu kinsan abinda za'ayi?" Sai ka fa Bari naje na dawo, domin yanzu daddy yana jirana akwai wani maganar da zamuyi dashi ne". Duk da zuciyarta yana fa i mata, ba gaskiya bakura ya fa i mata ba, amma tace to saika dawo". Da ido ta bisa dashi har ya fita daga gidan". Bakura na fita ya kwashe da dariya, ha e da cewa sha-sha-sha". Tunda bakura ya shita adyra ta zauna zaman jiransa, shiru-shiru be dawo ba, wayarta ta dauko ta fara kiransa, lokacin bakura na tare da zynah suna shirya kaya, duk uban kiran da Adyra keyi yana gani amma be aga ba". Gani tayi kira har ta gaji, be aga dole yasa ta hakura da kiran, sannan taje ta rufe gida". Bayan sallar asuba, duk suka shirya, aroud 7:AM suka dauki hanyanr kano, bakura da zynah mota aya hjy da daddy sai driving suma mota aya". Da safe ma haka, zuba ido adyra tayi rana jiran shigowar bakura amma taji shiri, daga nan ta hau fushi bata sake tunanin kiransa ba kuma". Su daddy basu isa garin kunci ba sai bayan la'asar, kai tsaye gidan su zynah suka nufa, gani sune yasa en'zaman makoki duk suka zuba ido, da son gani suwaye a motar". Da shi motar su bakura ne a gaba, yasa shida zynah suka fara fitowa, sannan su daddy da hjy, duk en'zaman makokin sukabi su da ido suna kallonsu, galala, kamar basu taba gani mota a rasuwar suba, daga kiman har maigari duk suka mike suka yo kansu, da sannu da zuwa". Hjy na fitowa daga mota, ba tare da daddy ya gani ba, yawun dake bakinta ta tsar an dashi, ha e da jan tsaki, zynah na kallonta da sauri ta dauke kansa tayi kamar bata gani ba suka nufi cikin gida". Zynah ce a gaba, hjy kuma a baya, tana tafe tana aibanta gidan, da haka har suka isa ciki, duk matan dake zaune jin sallama yasa suka juyo kansu, gani haka yasa hjy ta kara tsuke fuska ksmar tanajin warinsu, abinda ta mutumin kauye sai faman yake baki sukeyi suna kallon zynah da hjy". Har akin ummata zynah ta kai hjy, duk da aki babu laifi, domin a share yake tsaf babu datti, kuma ga ledar kasa daya rufe ko'ina, amma hakan bewa hjy ba, domin kin zama tayi a kasa, gani hakan yasa sadiya cewa ta zauna a bakin katifa". Nan sadiya ce ta fara gaida hjy, bayan su gaisa, matan dake waje, da gulma suka kara shigowa suna gaida hjy, amma dan tsabar rashin mutunci iri na hjy, ko kallo basu isheta ba, sadiya ce take amsa masu sai kuma zynah". Nan labari ya kai kunni rakiya, jin haka yasa rakiya cewa basai naje ba balle suyi min kallo banza?" Ruwan swan sadiya tasa aka siyo masu, dasu juice amma duk ba mai sanyi bane, sabida garin babu wata, mutum daya ne yake kunna genarato, a ranar kuma baya nan yaje cikin kano siyayya, koda aka kawo saida ta ibawa su bakura da daddy nasu sanna aka bawa hjy nata, ka an kawai hjy tasha sannan tace zatayi sallah". Da sauri zynah taje ta zuba mata ruwa a buta, sannan tazo ta sanar wa hjy, to kawai hjy tace, tana mikewa ruwan swan in da sadiya ta siye mata tashi dashi tayi alwala sannan tazo ta fara sallah". Nan take sadiya ta fito da ku i ta aiki wata kanwarta kasuwa tayo mata cefane, hjy na idarwa sadiya tace zynah ta rakata akin rakiya su gaisa". Zynah ce ke daga hjy na biye da ita, da takalmi hjy ta shiga akin rakiya, duk da mutuwar da akayi wa rakiya, amma besa ta daina masifa ba, suna ha a ido da hjy tun daga sama har kasa ta ibi hjy dashi sannan ta zubar". Hjy dake tsaye tace sannunku". e bakin rakiya tace, kema sannunki". Tun daga sannan rakiya bata sake magana ba, matan dake zaune a akin rakiya ne suka amsa wa hjy, daya daga cikin matan tace hjy ga gun zama".. Da sauri hjy ta dauki mayafinta ta rufe hancinta dashi, sannan tace ina gun zaman yake?" Jin haka da shike rakiya ta fahimci abinda hjy ke nufi, tsaki tayi, ha e da cewa aikin banza, ni za'a kawo wa rainin hankali?". Ba tare da hjy ta tsaya jin abinda rakiya zata ceba ta fita daga akin". Koda aka gama abinci a ka bawa hjy, kin ci tayi, biscuit da juice hjy ta dauko daga handbag inta taci ta kwanta" kafin hjy ta kwanta saida ta feshe akin da turare, gani sadiya zata ruwa akin da sauri hjy tace a'a bata yarda ba, sabida bazata iya kwanciya a aki irin wannan kuma a rufe kofa ba". Sadiya bata nuna damuwar ta ba, haka ta tashi ta bu e kofar,a lokacin ran zynah ya baci sosai sabida tunda suka shiga aki hjy take masu wani irin kallo na raini, gashi kuma duk kokarin da sadiya keyi a kanta bata gani". Washe gari kuwa babu yadda ba'a da hjy ba tayi wanka amma taki, a cewarta bazata iya amfani da ruwan garin ba" nan hjy ta tsama sai dai su tafi, daddy beki ba, sabida shima akan hanya yake, daddy ku i masu yawa ya bawa sadiya da rakiya, shima maigari da liman ba'a barsu a baya ba, alkhairi yayi masu sosai, kafin su tashi saida sukayi masa addu'a sannan su daddy suka dauki hanya shida hjy, bakura kuwa yace tare zasu dawo da zynah". Bayan anyi addu'ar uku ne, bakura ya shigo har akin