← Book details Zynah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 23

Sashe 21

Zynah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaba wa kansa, itama bazata kira sa, koda shekara nawa zai yi, domin tasan koda ta kirasa tasan cewa zaiyi yanada mara lafiya, to ina ruwana da rashin lafiyarta, tunda ba uwata bace, tama mutu mana". Daga ban garen maiduguri kuwa, kullum suke waya da ummata, haka take zama tayi ta shirya wa umma tata karya, tana bata labarin jikin hjy, ita kuma umma tata duk abinda zata fa i tana yarda, sabida a duk lokacin da zasuyi magana, kamar wata me allalmusu, duk abinda zata fa i yana zuwa iri daya da abinda daddy yake fa i masu akan hjyn". Kwana hjy Ashe bakwai sannan ta dawo, jiki kam sai son barka, domin a hakin yanzu hjy tana iya komai da kanta, sai dai wanda baza'a rasa ba, su zynah da bakura basu dai bata tuwan addu'a tana sha ba, duk da rashin gani Ni'eemat a gunta yana damuta,amma tunda Dr yace ta daina yawan surutu yasa tabar abin a zuciyarta". A lokacin da mijin Am'abuwa yake zuwa duba hjy ne, tace ta ha a kaya tabi mijinta haka, ta gode Allah yayi mata albarka ya bata masu saka mata". Da shike an albarka ne yace ya yafe mata ta zauna taci gaba da jiyar hjy har lokacin da zata samu sauki, yanzu haka ma gobe zai koma gida Nigeria's nan suka sallama, ku i masu yawa ya bawa Am'abuwa ha e da sallar saiya sake dawowa uba mai jiki". Ita kuwa Yah-na tunda aka kawo hjy tazo sau daya, ta tafi bata sake zuwa ba, har wannan lokacin". Bayan wata daya da jin saukin hjy aka sallamaesu, domin yanzu hjy ta dawo dai-dai, daddy yaso su biya germany su kara hutawa amma hjy taki, an haka suka kwashi kayansu gaba daya zuwa gidan Nigeria, suka inaso hjy Ashe ce da malah suka tar besu, daga airpot nan suka daukesu har gida, abinci kuwa kafin su isa hjy Ashe ta gama komai". Anan gidan su hjy duk suka kwata, har da su zynah, domin hjy tace su bari su huta kafin suje gida su kama aikin gyara" Kafin 12:PM gida ya cika angi da abokan arziki, matan abokan hjy duk suzo gaida me jiki, basu bar gidan ba,sai bayan la'asar, hjy Asiya ce ta kai har dare, sabida mijinta amini daddy ne sosai, taso zuwa egypt duba jikin hjy, abinda ya hanata zuwa, itama ba wani isasshen lafiya ne da ita ba, hawan jini ke damuta". Saida sukayi sallar isha sannan suka bar gidan ita da hjy Ashe". Koda adyra taji labarin dawowar su hjy, bata zobs sai ayan washe gari sannan tazo, dai-dai da isowar en'maiduguri, hakan yasa gida ya sake cika fakilll da jama'a, gani haka yasa bakira daukar zynah suka tafi gidansu". Masu kuka suyi masu kuma jsjsntawa duk suyi, tsakani bakura da Ni'eemat kuwa sai ido, kamar akaya ta zuba ido tana kallonsa tana jira ya gaisheta, hakan yasa shima ya zuba mata ido". Su hjy da daddy suna aki, bakura yayi sallama, a ladabce ya zauna, sannan ya meda dubansa ga daddy yace daddy inada magana da kai, amma Allah yasa ku fahimceni". Daga daddy har hjy suka tattara hankalisu su bawa bakura, nan bakura ya fa i masu yadda suke zaune da Adyra, da kuma yadda sukayi da ita a lokacin da yazo daukar ta". Himm kawai hjy tace". Bayan sallar isha, lokacin duk su ha u a falo suna hira, nan hjy Khursum ta tada magana a gaban en'uwansu da sukazo daga gida msiduguri, har da kin zuwa jinyarta da tayi". Nan kowa yasa salati, itako mmn Adyra bata iya cewa komai ba, harrr sai da mutane daga gun sukayi shiru, sannan ta kira sunan bakura, bakura dake duke yace am'an umma". Idan ka cika cikin uwarka da ubanka,inaso ka saki Ni'eemat saki uku".............. Duk jama'an dake gun sukasa salati". Umma taci daga da cewa, ke kuma dan ubanki daga lokacin daya baki takarda inaso ki nimi wata uwar amma bani ba, ke harrr kin isa ki raba mana zumunci, wlhy kinyi kadan". Dan haka rubuta kabawa shege, take Ni'eemat tasa kuka tana fa in na duba umma, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min". Mikewar da zatayi ta haye kan Ni'eemat, ta hauta da duka, anyi-anyi ta tashi daga kanta amma taki". Da kar aka samu ta sauka, gani bakura na zaune, beda niyyar tashi balle ya dauko paper da pen ya rubuta takarda yasa tayi kansa, da sauri aka riketa, dakar dakar aka samu ta hakuri, saida komai ya lafa, hjy tace wa bakura ya kira mata zynah". Bakura na kiran zynah ta waya nan take tazo, da sallama ta shigo falon bayan su gaisa da baki ne, hjy dake zaune ta fara bayani, tanayi tana kuka, ha e da niman gafarar zynah, akan dukkani abinda ya faru a bayan". Babban yayi su hjy ce, tayiwa hjy fa i ha e kuma da nasifa, shi dan Adam ba abin walakantawa bane, kuma kowa da kagansa a rayuwa yanada ranarsa, to kare ma yayi rana balle an Adam". Ita dai hjy batace komai ba, idan ba kuka ba babu abinda takeyi". Itama zynah dake duke kuka takeyi tana fadi babu komai ns yafe maki, Allah ya yafe mana baki daya". Nan mmn Adyra tace wa bakura, daga yau, umarni take bashi, yadawo da Ni'eemat cikin gida su zauna tare da hjy, daga yau kuma kada hjy su sake daukar er'aiki, tunda ga Ni'eemat nan, idan kuma batayi ba, bakura ya zuba mata ido ya kyaleta har taji labarin, musamman zuwa zatayi da kanta ta hukunta shi, tunda shi ya kasa hukunta ta". Nan akasa dariya, masu jin zynah da wasa kuma sunayi". Washe gari duk suka shirya zuwa gida maiduguri, bayan tafiyarsu da sati daya, daddy da hjy sukasa bakura ya kira zynah, sukace ta fa i duk abinda tasoke in har baifi karfinsu ba, zasuyi mata". Zynah tana kuka tace babu komai, ita dai dama damuwarta daya ne, ummata takeso ta dawo kusa da ita". Da sauri hjy da daddy sukace idan shine kada ta damu". Washe gari daddy yasa driver da bakura suka tafi dauko sadiya, dai-dai lokacin rakiya ta biya wasu samari akan idan dare yayi, suzu su sawa sadiya da su hauwa wuta a daki". Hakan yasa rakiya tayi bakin ciki ba ka an ba, ranar bakura ya isa, washe gari suka dauki hanyar abuja, daga kayan sawa babu abinda sadiya ta dauka". Karfe takwas suka isa abuja, zynah tayi murna sosai, a akin hjy suka fara sauka, saida sukayi sallah sukaci abinci, sannan hjy tace zynah taje ta gyara masu side in da bakura yayi samarta ka, kafin a saman masu inda zasu zauna". Kwana Am'abuwa biyu da dawowarsi mijinta yazo ya dauketa suka tafi gidansu, duk a cikin abuja in ne". Bayan wata daya da zuwan su sadiya abuja, Allah yayi wa Asiya rasuwa, an kwanta da ita Amma ba'a tashi da ita ba". Kafin sallar asuba duk aka sanar wa su hjy khursum da hjy Ashe, hjy Khursum ta dauki sadiya suka tafi tare, cikin ikon Allah itace da zynah sai wata mata dake area suka yiwa gawa wanka suka shiryata". Dama tun a kauye idan anyi rasuwa sadiya ake kira, tayi wa gawa wanka, sabida tanada ilimin addini sosai, hakan yasa ta koya wa zynah". Anayi bakwai kowa ya watse, yarage yara da babansu, babu yadda en'wan Asiya basuyi da alhj Husaini akan yabasu yara su tafi tare ba, amma yaki, dole yasa suka bar yaran tare da babansu, da shike ba masu girma sosai bane, babbansu 15year ne da ita, sabida basu sami haihuwar da wiri ba, sai kanninta biyu,maza". Lokacin da zai koma bakin aiki a germany gidan su hjy ya kawo yaran, tun daga lokacin haka yakeyi, suma da shike su saba yasa basu damuwa". Daddy ya ha a hauwa da Fatima ya sasu makarantan su Zara'u yarinyar Asiya". Hjy nada wata biyu da dawowa sannan Yah-na tazo, tun daga kofar falo, hjy ta hanata shiga mata gida, babu yadda ba'a da hjy ba amma taki, har saida sadiya tasa baki, gwiwa bibiyu Yah-na ta duka mana rokon hjy gafara, ga shohon cikin dake jikinta, amma be hana hjy yi mata fa a ba, da kuma nuna mata kuskurenta". Tawan Asiya biyar da rasu, ranar da alhj Husaini yazo gidan su hjy, lokacin sadiya tana falo suna hira da hjy yayi sallama, tunda ya shigo idonsa ke kan sadiya, gani haka yasa tabar gun, tana fita slhj Husaini yake tambayar hjy Khursum waye ita?" Bata boye masa komai ba, akan sadiya, alhj Husaini be tsaya su gaisa bama, balle suyi hira, ya mike ya bar gidan, yana fita ya kira daddy bayan su gaisa yake sanar wa daddy abinda ke ransa game da sadiya". Daddy yaji dadi hakan sosai, nan ya kora hjy ya sanar da ita, hjy Khursum batayi mamaki ba, sabida dama biri yayi kama da mutum, koda hjy ta sanar wa sadiya, sadiya bata musu sa, nan hjy ya fara zuwa zance, yara da rashin wayo, middu suga babansu yazo murna sukeyi sosai, hakan yasa koda maganar auren ya taso, ba karamin murna sukayi ba, samumman Zara'u sabida sadiya na koya mata duk wani abu daya shifi addini, alhamllh yanzu ta kara sani sosai ba kamar dah ba". Ita kanta zynah murna tayi sosai, bayan sati uku, ranar asabar aka daura auren sadiya da alhj Husaini, da dare su hjy Khursum da hjy Ashe suka rakata gidan alhj Husaini, kwana nan su uku da daura aure ya kwashesu zuwa germany, harda su hauwa da Fatima, ha e da nasa yaran".. Gani pakhryya ta tafiya ko ina, yasa hjy Khursum amsarta ta yayeta, a cewarta zynah ta huta da tsotso". ******* Bayan wata biyar tun dare Yah-na ke nakuda, gani haka megidanta ya dauketa zuwa asibiti, nan akai ta fama, kwananta biyu tana labour daga karke har aka yanke shawarar za'ayi mata operatinon, cikin ikon Allah, saiga haihur yazo zanga-zanga idan banda kiran hjy babu abinda takeyi". Da kar aka samu baby ya fito, amma ta kafa, ba takai da akasan baby na fitowa ba, shi isa tashi wiya sosai, satinta aya sannan aka sallamesu, dole yasa aka kaita gidan su hjy, a lokacin ne ta kara sani
Chapter 21 · 0% Book details