← Book details Zynah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 23

Sashe 22

Zynah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

uwa nada daraja da muhimmmanci, kara rokon hjy tayi gafara sosai". ~~~~ ~~~~~~ _*kunci*_ Tunda rakiya ta sami labarin Sadiya tayi aure har ma ta tsallaka tabar kasan, yasa rakiya ha iyar zuciya ta yanke jiki ta fa i, gaba daya yanzu babu abinda ke aiki a jikinta, ita da gawa babu maraba". Ba garen zainab da usman kafin uwani ta haihu zainab taga abu iri iri, daga gun uwani har gun usmab in, amma tun bayan haihuwar, hawalar da tashi, yasa gaba daya tayi sanyi da al'amarin duniya, yanzu haka koda usman ya taso zai yi mata walakancin daya saba, uwani ke hanasa". Bayan wata biyar Allah ya azurta zainab da ciki, yayi da rakiya kuwa ta amsa kiran ubangiji, wanda a yanzu da haka zamansa mukeyi idan lokaci yayi". **** A bangare adyra da bakura kuwa, ba karami sanyi tayi ba, hakan yasa ta roki bakura gafaran duk abinda tayi masa, shima kuma ya yafe mata". Zynah kuwa dama bamai matsala bace, wanda tayi masu ma su yafe mata balle ita er'kallo, dykkansu bakura ya hadsu yayi masu fa a sosai akan su ha a kai, tun daga lokacin babu me jin kansu, duk da ba gida daya suke ba". Bayan wata biyar Am'abuwa ta haifi er'ta mace, yayi dasu zynah da Adyra kuwa suma duk sunada ciki". Idan muka waiga germany kuwa, watan da alhj Husaini da sadiya sukayi aure watan ta samu cikin, hakan yasa yanzu take faman da kanta sabida cikin ya tsufa sosai har ma ta shinye watar haihuwar " *kunci* Bayan wasu watanni zainab itama ta haifi anta baby boy, wanda yaro yaci sunan malam shehu, murna a gun usman kamar ya ha iyeta, da shike meson haihune sosai". Bayan sallar asuba sadiya ta tashi da nakuda, da sauri alhj Husaini ya dauketa zuwa asibiti, bata dauki lokaci suna zuwa ta haifi yara duk duk maza, daga alhj Husaini har yara sai murna, ana gobe suna suka iso gida nigeria, washe gari akasha suna, alhj Husaini be canza wa yara suna ba, haka ya barsu da sunansu". Tunda hauwa tazo gidan zynah, lokacin malah yazo gun bakura, yaga hauwa nan yakasa ya tsare shifa yaga matar aure, babu yadda hjynsa bata yi dashi ba, amma yaki, domin a ce warsa shima haihu yakeso, killan sanadiyar auren da zai kara matarsa zata samu ciki". Alhj Husaini yace yaji, amma yayi hakura saita kammala karatunta na nurse da takeyi a can germany in, duk da malah beji dadin hakan ba, amma yaya zaiyi dole yasa ya hakura". Satinsu biyu suka koma germany, idan malah yanajin ganinta binta yakeyi har can germany in". Ranar wata juma'a zynah ta tashi da nakuda, da sauri bakura ya sanar wa hjy, hjy tazo ta dauketa zuwa asibiti, yayin data haihu twist inta mace daya miji, ba'a suna ba adyra itama ta hauhu baby girl, hakan yasa aka ha a suna, na adyra taci sunan hjy, amma suna kiranta a *AMRAH* na zynah kuwa ba'a canza masu suna ba amma suna ana kiransu da *AZEEM DA AZEEMA". Bayan shekara biyu lokacin Hauwa ta kammala karatunta, suka dawo gida nigeria domin shan biki, a kunci akaje aka daura aure, sannan aka dawo abuja yin shagalin biki, wa zaiga su zainab a birni sai faman kauyanci suke zubawa, kallo kuwa kayar wacce aka wanke ma makanta" . Duk da an gama biki amma sadiya ta hanata tafiya saida tayi kwana bakwai, sannan suka hada mata abin arziki, har da waya suka bata, sannan kuma sukace duk abinda take bukata ta kirasu ta waya, insha Allahu zasu aika mata dashi". Biki sa sati daya malah ya kwashi matansa zuwa America, suna su sadiya suka koma germany. _Yayin da nima er'mutan zazzau nace bari na kwashi kayana zuwa zaria, tunda banida ku in jirgi balle na bisu na jiyo maku wacce irin wainar za'a soya a America_ Tamman billah _Alhamdulillah alhamdulillah_ *kuyi hakuri fan's labarin ba mai yawa bane, nidai fatana, sakon da nakeso nisarwa Allah yasa ya isa gareku Ameen ngd*
Chapter 22 · 0% Book details