← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 21

Sashe 8

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani farin ciki Ahmad yaji a ransa sanda yahango mahaifin Aysher ya nufo inda suke _Sabanin Da idan sukaje zance mahaifin budurwa yazo daniyyar cewa sufito sai suji wani kunci da bacin rai_

Tsugunnawa sukayi cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa fuska asake tare da fadin _Bismillah kushigo daga ciki_

Dakinsa ya shigar dasu tare da mikewa tsaye yashiga gida yafito musu da lemon gwangwani da ruwa su Ahmad suka kara gaishe shi ya amsa a mutunce.

Mudansir ne yafara gabadatar dakansu a gurin mahaifin Aysher tare da cewa su suna zaune a kano state ne amman suna karatu a yola kuma Alh.Lawan yayan mahaifiyar Ahmad dinne.

Baffa Usman ya yaba da nutsuwar su Ahmad dan haka yace"Na yaba da nutsuwarku Allah tabbatar da Alheri Aysher dai karatu takeyi nan da wata 8 zata kammala kuma bani da burin tayi ilimi mai zurfi a gaba na wannan ma data samu Alhamdulillahi idan har mijinta yayarda takarasa a dakinta barin turo muku ita"

Yamike yashige cikin gidan yatarar yadikko tanata zazzaga masa bala'in cewar tariga tabada Aysher ma wani dan haka bazata fita ba,..

Bai saurareta ba yace Aysher tawuce taje gurin masu kiranta yadikko bata isa tayi iko akanki ba.

Dasauri Aysher takarasa dakin da sallama suka amsa kamshin turaren Ahmad gaba daya ya gaureye dakin tashaka tare da lumshe idanuwanta ta nemi guri nesa dasu kadan tazauna a kan carpet tare da gaishesu suka amsa Ahmad sai washe baki yakeyi kamar gonar auduga.

Ganin Aysher taki sakewa dashi suyi hira yasa Mudansir mikewa dan yabasu guri ko Aysher zata rage kunyar datake yima Ahmad.

Ahmad yana ganin mudansir yafita yamike ya karasa kusa da Aysher durkusawa yayi a gabanta tare da cewa"My baby kunyarki tayi yawa a fulanin kekam dabance pls yau kadai ki kalleni kice kina sona idan ba hakaba zan shiga wani hali"

Kara sunkuyar da kanta tayi takasa dago kanta takalleshi tana wasa da yatsun hanunta.

Ahmad yakalleta yana murmushi gami da fadin " Aysher dan Allah karki gujeni duk wuya duk tsanani pls be with me zan zamo jarumi indai akan soyayyarki ne zan iya komai koda ace shadi za'ayi bisa al'adar garinku zanyadda inasonki ne tsakani da Allah,

Allah ya doramin sonki kuma jikina yana bani kece matata shisa nazo garinnan da niyyar karatu Kinsan ance matar mutum kabarinsa Ina sonki ina matukar kaunarki Fatana Allah ya nunamin ranar da zanganki a dakina amatsayin matata uwar 'ya'yana.

Hakan daya furta yasa Aysher rufe fuskanta da tafukan hannayenta.

Yakara da cewa"Aysher kece muradin raina abin fahari na kinzamo fitila mai haske "yan mata na nad'aki sarauniyyar birnin zuciyata I love u so much my wife"

Dariya Aysher tafara harda kyakyatawa kafin tace"Ya labarin gurinsu mom dafatan suna lafiya kagaisheta idan kunyi waya pls"

Dariya Ahmad yayi yace"So kike kiyimin wayau bakyaso kifurtamin cewar kina sona ko badamuwa su mom lafiya kalau mun kwana biyu bamuyi waya ba cos i switch off all my phones but nakunna yanz......

Wayarsa ce tafata ringin yaduba sunan mai kiran my Bro yagani a rubuce dan haka yadauka da sauri gaisheshi saddiq yafarayi kafin yace"Yaya meyasa ka kashe wayarka tun last 3 days toh akwai problem dad yagano komai cewar kaine kayi wakar nan so yanzu haka yatafi abj jiya zaka iya ganinsa ako da yaushe ma'ana yau ko gobe ko jibi a garin yola yarantse kabar sake karatu a garin yola difffff wayar saddiq ta dauke Ahmad yakira yaji it's not reachable dan haka dole ya hakura ya kalli Aysher tare da mikewa yana fadin Swthrt barin tafi zandawo gobe in sha Allah tunda munsamu babanmu yadawo nasan bamu da matsala zanzo gobe da daddare.

Aysher tace Allah yakaimu kahuta gajiya kacema Yaya mudansir sai da safe.......
[10/14, 7:11 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒

Lokacin da aka aika dasu Ahmad suka aika ayi masu sallama da aysher baffa Usman yana zaune a tsakar gidan wanda ya sauka garin yola da safe.

Abin yabashi mamaki dayaji yadikko tana fadin aje ace musu anyima Aysher mijin aure.

Dakatar da dan aiken yayi ya dubeta tare da cewa "yau she nace miki nayi mata miji bayan asalima bansan wani da yake zuwa gurintaba dan bata fita zance sai yau amman kina cewa kinyi mata miji"

Cikin dakewa yadikko tace"Nayi mata mana mallam lokacin kana lagos kuma kaga yau kadawo bamu samu wani dogon zamaba sosai nidakai shiyasa banyi maka bayani ba.

Kai Baffa Usman ya girgiza tare da cewa mata!Mata!!mata!!!
Sai abarku kunada wuyar sha'ani Aysher yakalla yace ke kinsan anyi miki mijine kuma kina sonsa...girgiza kai tayi alamar bata sani ba dan Haka baffa Usman yamike yasakai yafita shine yasamu su Ahmad a waje.

Cikin gidan kuwa Rankwashin Aysher yadikko tadinga yi tare da cewa'Aradun Allah dole saikin auri dan Abj ko kinki ko kinso bari shima uban naki zaishigo ya sameni ne"

Toh shigowar baffa ne yasa tadakata da bala'in da take surfawa Aysher...

Wannan kenen

***********

Daga Abj kai tsaye Alh.Aliyu da Alh.Labaran yola suka yima tsinke bayan sun kama hotel gidan Alh.Lawan suka yima tsinke bayan gaigaisawar da sukayi tare da tambayar bayan rabuwa Anan Alh.lawan yake bama Alh.Aliyu labarin karar Ahmad da uwar yar aikinsu takawo cewar a rabashi da yarta tundaga wannan rana yau kwana kusan sati daya ban kara ganin Ahmad a gidan nan ba nayi binciken sirri a makarantarsu an tabbatarmin baya attending lectures ma gaba daya amman ana ganinsa a cikin Compound na Hostels din school din so may be yana tare da wani abokinsa ne dan haka nasa kudi mai tsoka akan a ganomin dakin dayake kwana kuma waye wannan abokin nasa dan haka kayi hakuri mujira wayar sa daga yau zuwa gobe.

Alh.Aliyu yayi na'am tare da godiya gami da bawa Alh.lawan hakuri tare da cewar yasamo kauyen da zai turashi a can saudiyya inda kwata kwata babu wani dan Nigeria sosaima a gurin ballantana yasamu abokan lalacewa......

MAMAN HANAN
[10/15, 12:25 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

Page 25-26

©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA

Hankalin Ahmad yatashi sosai dajin maganar zuwan mahaifinsa babban damuwarsa ayanzu shine mahaifinsa bazai ta6a sauraransa har yayi masa uzurin zuwa gidansu Asher dan neman masa aurenta ba.

Kana kallonsa kasan yana cikin tashin Hankali

Zama yayi a gefen katifar dake dakin Mudansir yadafe kansa da Hannunsa (Ciwon kansa yatashi) cikin karfin hali yadago idanuwansa da sukayi jawur yakalli Mudansir yace"Mudansir abokina nasan kai abokine nagari dan Allah ga amanar Aysher tunda kana garin nan kasamin ido akanta karka bari a cutarmin ita karka yadda a aurar da ita da wani idan bani ba zan iya mutuwa idan narasa Aysher inasonda dayawa dan Allah nawan.

Mudansir cikin tausayawa yakalli Ahmad _Hakika yana cikin wani hali cos Ahmad yana karfin hali da jarumta da wuya kagane abinda yake damunsa but akan son Aysher gashi yau Ahmad yakaraya yazamo rago yana neman yafara ZUBAR HAWAYE_

Mudansir yadafashi cikin sanyin murya yafara magana da cewa"Ka kwantar da hankalinka Nawan in sha Allahu Aysher matarka ce baka da wata mata sai ita da yaddar Allah nasan ma Abbanku bazai dauki komai da zafi ba karka damu kaji"..

Mudansir yafada masa haka da ya kara masa kwarin gwiwa.

But Ahmad cikin karaya yace"Nasan halin Abba I know him very well bazai ta6a yadda yabar ni ba zai dauki mataki akaina ne dan yasha fadamin abokina kai kanka kasan banajin magana amman wallahi a Da ne yanzu na nutsu narage wasu abubuwan ni babban tashin hankalina ma za'a nesantani da aysher"

Awannan daren Bacci kauracema idanun Ahmad yayi saida Mudansir yayi masa dabarar bashi lemo wanda yayi mixed da codin kwalba daya batare da sanin Ahmad ba ya kwankwade aikuwa mintuna kadan bacci yayi awon gaba dashi.

**********

Hello!

Yauwa Alh. Kanajina mungano Dakin dayake jiya da daddare anan hostel din Apti ne dakin wani abokinsa wanda bincike yanuna mana tare sukazo daga kano shima abokin dan kano ne Hostel Room number sa 15 sunan abokin nasa Mudansir.

Toh madallah nagode xakuji alert yanzu nagode. Cikin doki Alh.Lawan ya labar tawa su Alh.Aliyu komai nan take suka mike daniyyar tafiya dan yamma tayi kuma suna nesa da School din.

Waya Alh.Aliyu yajawo ya fara kira bugu daya aka dauka.

Hello!
"Abba ina wuni ya yola dasu baffa"

"Duk lfy kalau saddiq kaje airport gurin agent dinnan kaga komai yana zuwa da sauki kace masa anga yaron yashirya mana komai gobe morining flight nakeso mubi zuwa Saudiyya dan ko gida bazamuzo ba saina dawo"..

Toh Abba barin karasa daman ina kusa airport sadiq ya katse wayar.

Jikinsa har rawa yakeyi wajen kiran dan uwansa *Allah sarki naka sai naka*

Ahmad yana zaune yagama shirya kayansa yana jiran abinda zai faru nan gaba yamika komai ga Rabbi.

Yaji wayarsa tana ringing *My bro* yagani a rubuce dan haka yayi saurin dauka.

Hello Yaya ina wuni kayi sauri ba time sosai kashirya komai naka gasu abba sun gano inda kake zasuzo......

Ahmad cikin sauri batare daya saurari karashen bayanin kanin nasaba ya katse wayar cikin sauri yakalli mudansir yace" Nawan bawani time sosai gasu Abba nan zuwa hostel pls ka adanamin wadannan abinda nabaka idan na bukace su saddiq zaizo yakarba and pls karka kawosu gidansu Aysher duk abinda zasuyi kujirani anan barinje nayi mata sallama dan Allah karka kawosu karikesu banaso atayar mata da hankali sai nadawo".

Yana gama fadin haka baijira cewar mudansir ba yasakai da gudu yafice daga dakin.

Ta boyayyen kofar fita daga Hostels din yafice yatari mashin sai Anguwae Damare.

Yana zuwa a gurguje yasamu yaro yaturashi yayi masa sallama da Aysher.

Yadawo yace gatanan zuwa
Aysher tafito fuskanta da alamar annuri amman tana kallon gogan nata tasan cewar yana cikin tashin hankali gaisheshi tafarayi ya amsa tare da tambayar yadda take tace tana lfy lau.

Cikin jarumtaka Ahmad bayaso Aysher tanago weekness dinsa yafara magana da cewa" My love a gurguje nazo ne nayi miki sallama babana yazo xamu tafi tayiwu nadawo nan kusa may be kuma sai an kwana biyu so pls Aysher ta dan Allah ki tsaremin kanki karki fada tarkon masu yaudara masu jan hankalin 'yan mata kituna kullum aranki cewa dukkan yanwa tana tare da sauki
[10/15, 1:23 PM] Zeetty: [10/15, 12:45 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

Page 25-26
Chapter 8 · 0% Book details