← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 21

Sashe 18

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin muryan lallashi Ahmad yace"Abokina kataima ka a bada ita yau tunda har na wakilta ka kazo kayimin iyaka k'kokarin ka pls kamar ina gurin, ni yanzu je ka nemo min ita ka had'ani da ita a waya yau kwata-kwata banji muryan ta ba wani iri nake jina."

"Sannu rasa kunya idan baka da kunya, ni inada ita, bazan iya zuwa neman Aysher ba ka kwantar da hankalin ka tana mota na yanzu zamu taso da yadda Allah amman magana awaya kam ha hali saboda sai anyi siyan baki a Al'adance" Mudansir ya bama Ahmad amsa da hakan.

Tsaki Ahmad yayi kafin yace"Wannan al'ada yakamata a dainata tunda ba addini bane Allah ya kawoku lafiya" yana gama fadin haka ya katse wayar da alama ransa ya 6aci.

Sun sauka a kano da wuri dan haka bayan ankai Aysher da danginta masauki sunci abinci Umma ta aiko da wata Alkyabba, tace Aysher ta shirya a cikin ta dan za'ayi walima karfe 4.

Aysher tayi kyau cikin shigar kamar balarabiya kwaliyan da Fatima tayi mata mai sauki ne amman ta had'u.
Malama Jamila sulaiman (Ammi) ita aka dauko dan fad'a karwa. Tafara bud'e taro da addu'a kamar haka:- *INALHAMDULILLAH,NAHAMADAHU WANASTA'INUHU,WANASTAGFIRUHU,WANA'UZU BILLAHI MIN SHARRI ANFUSUNA,WAMAN SAI'ATU,A'AMALUNA,MANYAHADIHLAHU FALA MUDLIL LAHU WAMAN YADLIL FALA HADIYA LAHU,WA ASH HADU ANLA'ILA HA'ILLALLAH WAHADAHULA SHARIKALAHU WA ASH HADU ANNA MUHAMMADU ABDUHU WARASULUHU,SALLALLAHU WA ALAIHI WA'ALA ALIHI WA ASHABIHI WASALLAMAN TASLIMAN KHASIRAH*

YAN UWANA ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI TA'ALA WABARA KATUHU,INAMUKU SALLAMA IRIN TA ADDININ MUSULUNCI!

kamar yadda kukasani ba mutaru a nan domin komai ba, face dan taron walimar auren Aysher da angon ta Ahmad wanda muke musu fatan samun zaman lafiya.

To Aysher nasiha ta gare ki da sauran mata baki d'aya shine ki kula da mijin ki, yi nayi bari na bari, kuma shi aure ki d'aukesa a matsayin ibada domin hakan ne zaisa kiyi hak'uri da juriya akan zaman gidanki.

Sanan basai na fad'a miki ba kasan cewar daga ganinki nasan ked'in mai tsafta ce saidai in k'ara miki tuni daki k'ara akan wanda kike dashi, sanan abu mafi wuya kuma mafi so shine kizama mai 6oye fushin ki da yafiya, karki zama mace mai gaba da mijinta in yamata wani abu, kizama mai taushin hali, kuma banda rainuwa, duk k'ank'antar abu mijin ki yakawo kizama mai yaba masa koda ba haka bane a zuciyarki, domin zaiji dad'i da karfi gobe yakawo wani, sannan Allah zaiyi farin ciki dake a ranar gobe k'iyama.

Mafi akasarin mata sai kiga mazajen su sun zauna dasu tsawan shekara goma sha suci dasu, su sha dasu amma rana d'aya in magana ta taso sai ace mekata6a mun to wallahi 'yan uwana mata mukiyaye domin Manzon Allah S.A.W lokacin dayaje sama yaziyarci gidan wuta yaga mafi yawan su mata ne, sanan an tambaye sa, meyasa mata ye sukayi yawa a wuta?
Abun da yace"shine:-

*Suna sa6awa mazajen su.*

*Suna yawan tsinuwa.*

*Suna bayyana saraici.*

Dan haka mata mukula wallahi duniya fa ba gidan zama bane kamar yanda kake zuwa bak'unta in kagama adadin kwana kinka kakoma to haka kake zaune duniya, sannan babban tashin hankalin mu yanzu yanda mutuwa bata mana alama kana tsakiyan rayuwar ka sai kajika kwatsam a cikin kabari, an tashi da kai amma kan dare ka kwana a cikin kabari.

Karna cika ku da surutu domin in zan kwana bazan gama ba.

Amma jan kunnen da zanyi mana shine kiringa tausasa muryarki yayin da kike cikin bacin rai, ko kuma karkiyi magana sai kin huce domin babu alkairi acikin maganar da za a fad'e ta cikin fushi.

Mata dan Allah mudena sa turare in zamu fita haramun ne duk namijin daya ji k'amshin kuma ya burge sa to kina da lefin zina dai-dai kuke da wanda yayi, dan Allah akiyaye, kituna wanda fa kikayi domin kibirge su wallahi randa kike cikin azaba ba mai iya cetan ki suma takansu sukeyi.

Mata murike iyayen muji duk da ba a musu gwaninta amma a fita hakin su, arike su kamar 'yan uwa.

Sanan mata kunga shigan dakukeyi to wallahi kuyi hankali, shiyasa yanzu matan aure idan kuka fita kiga maza na muku magana kamar 'yan mata, sabida irin shigan 'yan mata da kukeyi kizama mai 6oye surarki, shiyasa a yanzu bamu da daraja a idan duniya sabida tsiraicin mata abayyane yake ba abinda ba a sani ba ko ba a ganiba akiyaye.

Abu na karshe kunga tsinuwa to wlh kubari domin duk gidan ma da ake tsinuwa, albarka basa zuwa gurin, katsinewa d'anka ko kace Allah tsinewa wane bakyau yana kai mutum jahanna ma mukiyaye kuma muyawaita sadaka.

Gamu mata munfi maza wahala ko gun haihuwa, rainon ciki, raino bayan haihuwa matsalolin rayuwar aure amma ace munyi sakacin da zamushiga wuta, to dan Allah mukiyaye.

Allah yarabamu da Jahannama, inawa duk 'yan group dina ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA fatan Alheri, Allah kasa dukkan mu 'yan Aljanna ne, ka k'ara shirya mu kan dai-dai ameen.

Sannan kuma 'ya'yanki ki koya musu ladabi da biyayya, su dunga girmama na gaba dasu, ki nuna musu suyi da'a ga Allah da manzonsa, sannan sai iyayensu.

Ki koya musu yadda za suyi zumunci da tausayin junansu. Ki kassance mai yiwa mijinki addu'a dan samun bud'i ki rok'i Allah ya d'aukaka mijinki, zuriyarki, d'aukakar addini, ki zamo mai k'yakk'yawan mu'amala da mak'otanki

Aysher ina so ki zamo matar k'warai abin alfahari a gurin mijin ki domin shine Aljannarki shine abin alfaharin ki.

Zan tak'aitane sabida lokaci, Aysher Allah yabaku zaman lafiya keda angon ki kula da addini Allah ya Albarkaci Auren ku da zuri'a d'ayyiba. Ameen Allah maida kowa gidan sa lafiya

*WASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH*

Addu'a akayi kafin aka tashi walimar bayan anyi rabon abubuwa na biki.

Nasiha sosai masu shiga jiki da zaman takewar aure Ammee Jamila tayi ma Aysher.

Aysher kuka take tayi cikin alkyabbar ta Ahmad kuwa sai kiranta awaya yakeyi harya gaji da nemanta, yafara kiran na K'anwarsa ta sanar masa suna gurin walima kuma ba damar d'aukar waya, rok'onta Ahmad yayi da cewa"ta taimaka masa da daddare ta had'ashi da Aysher a waya idan ba haka ba wallahi zai shigo gidan har inda matar sa take sai dai a ce masa yayi rashin kunya"

Dariya tayi kafin tayi masa alk'awarin had'asu da daddaren.........

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/27, 9:41 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

Page 55-56

Ahmad yana zaune cikin abokan sa (A gidan su Mudansir) amman hankalin sa gaba d'aya yana gurin matar sa dan haka wayar Amatullah k'anwarsa ya kara kira yaji shiru, mik'ewa yayi yafito daga gidan su Mudansir d'in batare yayima kowa magana ba ya mike yabar gidan, kai tsaye motar da yake amfani da ita, tun bayan dawowan sa (daga saudi'a) ya nufa bayan ya shiga yajata bai tsaya a ko'ina ba sai gidan Mahaifinsa.

Ku tsawa yakeyi ta ko'ina abokan wasa suna ta tsokanar sa da cewa"Ango kasha kamshi", bai kula da abinda suke cewa ba kai tsaye falon Mahaifiyarsa ya shiga yana zazzare ido sai da ya tabbatar Umma bata falon sai wasu danginta, hankalin su yana kan kallo basu lura da shigowar shi ba dan haka yayi amfani da wannan damar cikin zafin nama ya shige d'akin da yake tunanin nan aka sauke matarsa.

Aikuwa yayi sa'a dan kuwa a d'akin Umma dake falon k'asa akayi masu masauki, dan kuwa Ahmad yana bud'e k'ofar yaji wasu mata suna fulatan ci, dan haka yajuya da sauri.

Dole bayadda Ahmad zaiyi a wannan ranar bai ga Aysher ba, ya cika fam ya k'ullaci Amatullah k'anwarsa (Ahmad ba hak'uri)

**********
Washe gari dinner za'ayi daga nan a wuce da amarya gidan ta, da daddare kowa ya gama shiri 'yan uwa da abokan arziki duk an tafi.

Hakik'a dinner ya yi kyau Amarya da Ango sun had'u ba k'arya, anci, ansha da abubuwa da aka tanadar domin taron.

K'arfe tara aka fara d'auko mutane ana dawo da su gida, Ahmad mikewa yayi ya kalli Amaryan sa cikin shauk'in so da k'auna yace"Ina zuwa kijirani tare zamu koma ba zaki bi su Aunty Khadija ba (K'anwar maman sa)".
Kai Aysher ta d'aga masa dan bazata iya mishi magana ba saboda tunda aka shigo Hall d'in yake rik'e da hanun ta duk inda zasuje har gurin fita rawa yak'i sakin hanun ta, ita kuma kunya take ji duk iyayen su ne a gurin.
Saboda haka taji dad'in wannan fita tashi daya ce zaiyi saboda duk a takure take.

Cikin taron ta kutso kai tsaye gurin Aysher ta nufo waya tacire a kunnen ta, takalli Aysher tace "Ahmad yace kizo muje ta wancan k'ofar kutafi".
Waigawa Aysher tayi taga ba kowa a kusa da su duk an fita waje dan komawa gida, ganin budurwan yarinyar da ankon dinner a jikinta yasa Aysher mik'ewa tsaye, budurwan tace" Laaa naga kinayin abu sanyi-sanyi ko dan baki gane ni bane sunana Safiya daga Gombe mukazo ni family yaya Ahmad ne.

Tunawa da Aysher tayi cewar Ahmad suna da family a Gombe yasa ta mik'ewa cikin kwarin jiki suka bi ta hanyar da budurwan ta nuna musu, suka fice (Hanyar ba jama'a kwata-kwata)

Wani had'ad'd'iyar mota budurwan ta bud'e ma Aysher gidan baya ta shige da sauri cikin k'warin gwiwa danjin kamshin turaren mijinta a cikin motar, zama tayi batare da takalli na kusa da ita ba, domin kanta yafara mata ciwo saboda hayaniyar jama'a da kuma gajiya, budurwan ta bud'e gidan baya ta shiga direba yaja motar sa ya figeta da gudu suka fice daga haraban hotel d'in.

Aysher sai da taga tafiya tak'i k'arewa idon ta daman a rufe yake dan haka ta bud'e a hankali takalli na kusa da ita, wani k'atoton mutum tagani ya zaro mata ido tare da saita kanta da bindiga yana mai yi mata nuni da cewar tayi shiru ko ya harbeta....................

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/28, 9:11 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Chapter 18 · 0% Book details