← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 21

Sashe 4

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata uwar ashar Ahmad yamaka masa kafin yakatse kiran hanunsa ya dunkule kafin yakaima bango naushi _oh my God nakira Guy dinna yabani shawara but yakara kunoni tayaya zan fahimtar dashi cewa taki yimin magana ballantana nasamu hadin kanta_
[10/10, 11:26 PM] Zeetty: A bangaren Mudan kuwa dariya yafara yima Ahmad yace" Nizanyi maganin mai taurinka tare da fadin rai Nawan saikayi kuka akan wannan yar fulanin dan daga gani kafada dayawa"

🍒🍒🍒🍒🍒

A Abj kuwa Yarbingel tana sauka gidan Hajiya falmata.
Aranar data sauka tabata hotunan yan matan datazo dasu a washe gari Haj.falmata takira Honourable Mahmoud akan yazo yazaba ankawo.

*WACECE HAJ.FALMATA*

Haj.falmata asalinta yar maiduguri ce amman tazo abj saida abinci takeyi gefe guda kuma takasance kawalin mata (dillaliya)
Saboda akwai manyan yan siyasa da take kawoma yan mata dan fasikanci wasu kuma masu kudin tana kawo musu kyawawan yanmata ne daga garin Maiduguri (Shuwa), cameron,manbila da yola saboda masu kudin sunason auren kyawawa dan su samu yara masukyau farare masu kama da larabawa basu damu da ilimi ko rashin ilimin yarinya ba kawai dai su aureta idan yaso daga baya saita waye.

Haj.Falmata tana hada aure kuma tana hada lalacewa danhaka take samun kudi masu tsoka yanzu wannan hotunan da aka kawo mata duk neman masu bukatarsu takeyi bisa kudi masu tsoka kuma duk hoton yarinyar da akazo dashi da yaddar ita yarinyar ne da iyayenta ko marikanta.

Wannan kenan
***********

MAMAN HANAN
[10/11, 6:19 PM] Zeetty: [10/11, 6:15 PM] Zeetty: [10/11, 6:10 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒

Page 10-11

*INDABAWA O.H.W Ina godiya maman Hanan tama sonku kamar yadda kuke sona love u more*

©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA

Hankalin Ahmad yatashi dan ganin yakasa samundaman yin magana da Aysher akwai ranar data taso aiki tafito tatsaya gaisawa da baba maigadi cikin fulatanci takemasa magana.

Ahmad yakalleta tare da fadin ni bazaki gaisheni bane? Yana magana yana busa hayaki (sigari)

Takalleshi a tsorace kafin tace"Minanate hausare sai fulfulde"

Ahmad yarasa abinda take nufi dahakan ita kuma tana gama fadin haka tasakai tawuce abinta baba
Maigadi shine yakalleshi yace"Tana nufin batajin hausa sai fulatanci"

Daman batajin hausar ne dagaske? Ahmad yatambaya

Baba maigadi yace"Aradun Allah bansaniba nidai bantaba jinta tayi hausa ba naga alamar ma kamar tsoron wannan abin hannun naka take _Yafada tare da nuna sigarin hannun Ahmad_
Yakara da cewa nikaina abin yana cutar dani dan ance duk wanda yake shakar iskar hayakin yafi wanda yake sha cutuwa"

Jefar da sauran sigarin yayi kafin yace'waye ya fada maka haka"

Maigadi yace"Wani likita ne dayazo"

Ahmad murmushi yayi yace" shikenan nadaina daga yau baka fadamin dawuri bane dabazan cutar dakai ba ita wancan yarinyar inane gidan su? Ahmad yafada tare da nuna hanyar da Aysher tabi.

Mai gadi yace "Aysher wai".

Ahmad ya gyada kansa

Maigadi yace nan ne gana kadan wajen shagon da aka chargin wayar nan yarinyace mai hankali sharrin matar ubanta ta hadu dashi dan wannan aikin datakeyi a gidan nan ubanta mahaifi baisani ba tana zuwa makarantar arabi da boko nima agurin maidakina naji.

_Tab wannan shine fadi ba'a tambayeka ba_ Ahmad yafada cikin ransa kafin yace" Tana zance kuwa ina nufin tanada samari?

Wani dariya maigadi yayi kafin yace"Ina zansan wannan Ahmadu amman natabbata tsaleliyar yarinyar kamar wannan bazata rasa saurayi ba"

Doguwar tsaki Ahmad yaja kafin yamike yashige gida mota yadauko yafita wata yarinya yakira yake shaida mata zaizo da daddare sudan debi current din juna ma'ana yanaso yaji dumin jikinta he is bored"
[10/11, 6:11 PM] Zeetty: ******************

Hon.Mahmoud yana duba hotunan babu wanda hankalinsa ya kwanta akanta irin Aysher dan haka kai tsaye yanunama abokinsa nura hoton shima dai yayi na'am da wannan kyakkyawan yarinyar dan haka Haj.Falmata suka nunama hoton Aysher akan cewa itace zabin Hon mahmoud.

Yarbingel wanda tayi masauki a gidan Haj.Falmata suka kira tazo dasauri.

Takwana gidan sauki dan wannan diyar aminiyata ce bata dawani matsala yanzutake aji biyar a sakandire tayi saukar qur'ani sati daya daya wuce _wannan shine bayanin da yarbingel tayi musu a sanda suka nuna mata hoton Aysher amatsayin wacce Hon.Mahmoud yazaba_

Jin wannan bayani daga bakin yarbingel yasaH Hon.Mahmoud farin ciki ashe baiyi zabin tumin dare ba.

Nan dai suka gama magana akan cewar zasu tafi a satin saboda gabatowar zabe dan Hon.bayason ayi zabe bashi da aure kuma zaben saura watanni takwas.

🍒🍒🍒🍒🍒

*Al-qarya* multi-media nan Ahmad yaje ya rera wakarsata hiphop batare da sanin abokinsa mudansir ba dan yadaina nemansa ko school kuma Ahmad din yadaina zuwa he is not serious about his study at all ayanzu.

Wakar tasa tasamu karbuwa a gurin samari da yanmata matasa kai harma da masu aure fadi suke ai wakar *A.A HAMEED* yahadu ba kadan ba.
Kasan cewar wakar yayisa da salon soyayya da bege a ciki dan haka ma'abota soyayya suka afka cikin kogin son wakar.

Wani abin mamaki kuma duk yadda Ahmad zaiyi su hadu da Aysher yayi amman takasa bashi fuska yadaina shansigari a gurin maigadi yakuma daina zuwa makaranta saboda ita dan kawai yaganta su hadu amman shiru ba labari.

Ranar dai lokacin saura kwana 2 Aysher su koma school ranar juma'a da yamma Ahmad yaci kwalliya cikin manyan kaya na shadda kansa hadda hula idan kagansa ahaka kamar wani mutumin kirki.
Dayamma yatare Aysher a hanyarta takomawa gida cikin tsoro Aysher ta tsaya tana kallonsa.

Ahmad yarasa da wani yare zai mata magana dan gaskiya bazai iyafula tanci ba dan haka can wata dabara tafado masa dayatuna abinda innawuro tafada masa lokacin dayaji 'yarta Nafisa tana Faransanci cewa tayi _Ai yawancin yaran garin nan namu na yola sunajin french dan ana koya musu sosai_

Dan haka Ahmad yace bari yagwadata yaji yace mata"Bonjour"

A tsorace Aysher ta dubeshi tare da cewa" Comment Allez vous (yakake)

Yace"Je suis bien Normal (ina lafiya)

Aysher tayi shiru tare da juyawa dan cigaba da tafiya taji Ahmad yace"Est ce que ont peux etre des amies?
(Zamu iya zama abokai?)

Tace "Nom y'a pas d'amitie entre une fille et unbgarcon" (Babu abota tsakanin mace da namiji).

Yace"d'accord je peux etre ton grand frere? (Zan iya zama yayanki)

Cikin hanzari dan ganin mutane suna wucewa suna kallonsu Aysher ta bashi amsa da cewa"O.k je suis d'accord" (Ok nayadda). Ta fada tare da zurawa aguje dan karasawa gida.

Wow Tayadda am happy today.

Ahmad yafada tare da tafa hannuwansa yana dariya.

********
[10/11, 6:19 PM] Zeetty: Ahmad cikin kwanaki kan-kani yayi suna ta ko'ina idan kazagaye garin yola saidai kaji wakar A.A Hameed yana tashi.

Alh.lawan baisan abinda yakefaruwa ba shidai yaji har yarinyarsa Nafeesa tana maganar wakar A.A Hameed dan tana yawan jinsa a gidan radio

Kaca-kaca Ahmad sukayi da Mudansir akan wakar daya fitar dan ran Mudansir idan yayi dubu ya baci.....

MAMAN HANAN
[10/12, 7:48 PM] Zeetty: [10/12, 7:12 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 12-13

©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP

Hakika A.A Hameed yayi suna agarin Yola da kewayensa 'yan mata kuwa sukace idan bakayi bani guri gurin tururuwan zuwa gurinshi a school wadan da sukasan shi yayi wakan kenan.

Wanda basu saniba kuma ido suka xuba sunatunanin hanyar da xasuga A.A Hameed.

Duk yadda 'yanmatan sukayi dan susan gidansu Ahmad yaki yadda yabasu fuska dan yana tsoron Alh.lawan yana gudun kar yafadawa mahaifinsa dan fuskanci tsananin bacin rai daga gurinsa

Wata kilama dai yahanasa karatun gaba daya.

Abangare guda kuwa yayi-yayi yasamu kebewa da Aysher yarasa hanyar hakan gashi bashi da wani abokin shawara mudansir yafita harkansa kwata-kwata.

Gashi Inna wuro tadauki hutu a gurin aikinta dan haka tasama Aysher ido taki yarda Ahmad yasamu ke6ewa da ita dan bata yadda da take-takensa ba.

Dayaga alamun hakan sai shima yafita harkan Aysher ammanfa a gaban Innawuro
Dan a zuciyarsa bazai ta6a iya cire sha'awarta dayake ba.

Ahankali yasamo mafita wata ranar laraba suntaso daga makaranta kwatsam yataresu ahanyar makarantar Aysher wanda ta zage cikin kawayenta tana hira cikin harshen hausa ita yadinga bi dakallo tare da mamakin karyan data zubo masa cewar batajin hausa.

Dasauri ya isa gurinsu tare dayimusu sallama Aysher ce taganeshi dan haka ta6ata rai.

Daya daga cikin abokan tafiyarta azima ce tayi tsagal tare da cewa"wa'alaikassalam gidan waye kake tambaya"

Ahmad yace"No bagidan kowa nake tambaya ba inason magana ne da wancan yarinyar" _yafada tare da nuna Aysher_
Jin haka yasa Fatima tacema sauran kuzo mujirasu acan dan Allah _Tafadi haka tare da yima aysher alama da ido cewar tasaurari abinda zaifada mata_

Ahmad Aysher yakalla yace"Sannu Aysher sannu da kokari amman nasan malaminku yafada muku karya bakyau ko"?

Aysher cikin kwarin gwiwa tace"yafada mana haka zalika yafadamana cewar abinda kakesha haramun ne"..

Dan gajeran tunani Ahmad yayi kafin yatuna da abinda take nufi wato sigari azuciyarsa yace _Shi kadai tasani batasan inashan iyayensu bama, batasan cewar itama da abinda yasani zuwa gurinta ba_

Azahiri kuwa dariya yayi yace"Ai nikam nadaina tunda nafahimci bakyaso but amman meyasa zakimin karya meye dalilinki da hakan nimafa fulani ne kawaidai dan banajin yaren ne ballantana kimin wariyar launin fata danni ba kad'o bane"

Kara daure fuska Aysher tayi kafin tace"Eh banyi maka karyaba dan hausa ba yarena bane Fulatancine yaren nawa kuma ba karya namaka ba dalilin dayasa nace haka kuwa shine saboda Banason doguwar Alaka dakai zan wuce sai anjima.

Tana gama fadin haka tawuce idanuwansa yabita dashi yana kallonta tare da kara mai-maita abinda Aysher tace *BANASON WATA DOGUWAR ALAKA DAKAI*

Nantake wani bacin rai ya ziyarci cikin zuciyarsa hakika kallamar tayi bala'in bata masa rai _Toh kabarta mana ga mata nan manya masu class sunfita komai_ wata zuciyar ne take basa wannan shawaran dan haka a zahiri yace NO dakarfi dole saina ciki burina akanta sigari yadauko wanda yake aljihusa cikin kwali ya cinna masa wuta yafara zuka ransa yabaci.
[10/12, 7:48 PM] Zeetty: Yarbingel tasauka garin yola lafiya itadasu Honourable kai tsaye gidansu Aysher suka yima tsinke yadikko tayi musu karba maikyau dan tasamu labarin zuwan nasu dakin mijinta tayi musu masauki anan suka kara gaisawa takawo musu abinci wanda akan girkin abincin yau tahana Aysher zuwa gidan aikinta tace zasuyi baki.

Hon.Mahmoud sundan taba girkin dan yayi musu dadi balaifi.
Chapter 4 · 0% Book details