← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 21

Sashe 17

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dafarko ina neman gafararka Abba bisa ga rashin jin maganar ka da banyi ba hakika ni ba Noma da Kiwo nakeyi a saudi'a ba kamar yadda ka buk'ata asalima Masters dina nakoma dan nayi a makarantar KING FAHAD dake madina kayi hakurin rashin sanar maka da banyi ba nayi hakanne saboda na baka mamaki Abba amman kagafarceni"

Shiru Alh.Aliyu yayi kafin yakalli yayan matarsa Alh.Lawan murmushi sukayima junansu kafin Alh.Lawan yafara magana da cewa"Alhamdulillahi lallai Allah abin godiya Ahmad girma yazo tabbas chanjawar da abokinka yake cewa kayi ashe gaskiya ne ni tundaga zuwanka na fahimci hakan Allah yataimaka ya kuma k'ara shirya mana ku"
Ameen suka amsa gaba d'ayansu kafin Alh.Aliyu yace"Niba wannan ba Ahmad ina kasamu kud'in registration da sauran abubuwa ko Fallata ne yabaka Abin yabani mamaki ya akayi katafi da takaddun karatunka bayan bamu tafi da su ba ko dai kazo Nigeria ne a 6oye bamu sani ba ka koma inaso kasanar damu komai a yanzu"

Ahmad kansa a sunkuye yafara magana "Abba kayi hakuri daman nabar takaddu na a gurin Mudansir sanda kazo mutafi bayan naje Asir Abu-Fallata dakansa yacemin bazai ta6a mantawa da Alherinka gareshi ba dan haka bazai iya horar dani ta hanyar dakace masa ba yanemi shawarata akan haka.
Nikuma cikin farin ciki nayi masa bayanin inason komawa makaranta da burinka kenan daman akaina.

Abu-Fallata yacemin bashi da kudin da zai mayar dani makaranta yarantsemin da saiya mayar dani batare da saninka ba nikuma anan nace masa inada kud'i a account d'ina masu d'an dama toh Abba da wannan kud'in nafara karatu kuma ina juyawa anayimin business daga saudi'a zuwa nan kasarmu Nigeria da kuma Dubai.

Komai yana tafiya ta hanun Abokina Mudansir takaddun makaranta na kuwa Mudansir ne yakawoma Saddiq yakaima Agent din dayayi mana Visa aka biyashi yaturomin da su Abba yanzu nayi nisa a karatun masters d'ina Abba Inda nasamu kud'i kuma Abba shine kud'in dana samu danayi wakar nan ne dafatana zaka gafarceni" Ahmad yakarasa fadar tare da karasawa gurin Mahaifin sa durkusawa yayi a gabansa gwiwoyinsa a kasa alamar yana neman gafara.

Alh.Aliyu dafa kan Ahmad yayi tare da fad'in Alhamdulillahi Ahmad naji dad'in samun Nutsuwarka Allah yamaka Albarka bakomai nayafe maka yanzu saura maganar matar ka dan Mahaifinta yacemin abarta anan tazana jarrabawa kuma na amince masa mezakace?

Gyara zama Ahmad yayi Mudansir ya zuba masa ido dan jin abinda zaice dan yanaso yak'ara tabbatar da rashin kunyar Ahmad.

Ahmad yace"Abba nidai a son raina abani matata kawai mutare tunda wata biyu zanyi inyaso kafin hutuna yak'are ta gama zana jarrabawarta zanyi mata registration makarantar da Saddiq yayi nasa kaga Center d'insu tanada kyau dan haka Abba kataimaka kasa baki a fasa wancan maganar ta tare a kano ni banason wani biki ma duk bidi'a ne"

Murmushi mahaifinsa yayi dan yasan halin a 'Dan nasa zaiyi abinda yafi haka ma musamman akan Aysher dan haka Alh.Aliyu yace"Badamuwa zanyi masa magana akan hakan dan tunda kamin magana akan zakayi wata biyu nima nafara wannan tunanin bazai yiwu abarta tayita zama gaban iyayenta ba maganar biki kuma kasan bazai yiwu ace anfasa ba Mahaifiyar ka bazata yadda ba kodan akanka zamu fara aurar wa dan haka gobe zan wuce sai kutsara yadda komai zai kasance kafin kutaho jibi zan nemi mahaifin ta naji yaushe zasu kawota Alh.Lawan meye zakace akan haka.

Alh.Lawan yace hakanma yayi Alh.Aliyu gobe sai muje musami Baffa Usman d'in kafin mu wuce"

Tattaunawa sukaci gaba dayi kafin su Ahmad suyi shirin tafiya masaukinsu dake gidan Alh.Lawan

Nifa abokina naso abani matata mutafi tare k'afata k'afarta wai dole ne sai 'yan uwanta sunkaita ne mtswwww wannan Al'adar batayi ba wallahi.

Kanka akeji nidai nagama nawa k'ok'arin cewar Mudansir yana fad'in haka yawuce bayan gida dan watsa Ruwa........

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/25, 8:06 AM] Zeetty: [10/24, 10:01 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

Page 51-52

Tattaunawa a kayi sosai tsakanin iyayen Aysher wato Baffa Usman tare da Alh.Lawan da Alh.Aliyu an tsayar da magana ranar Alhamis iyayen Aysher mata zasu wuce da Amarya tare da sharad'in zata zana jarrabawar kammala karatun sakandire a kano.

Ahmad ba haka yaso ba yaso ace tare zasu tafi da Aysher domin shi ranar laraba zasu wuce da mudansir bayanda zaiyi haka dole ya hakura.

A kano shirye-shiryen biki sosai Umma takeyi da 'yan uwanta tare da abokan arziki sanarwa akeyi a k'afafen yad'a labarai tako'ina bikin Ahmad Aliyu Hameed da Amaryan sa Aysher Usman Damare.

Da daddare Ahmad yaje gurin Aysher dan suyi sallama saboda sammako zasuyi dan a mota zasu tafi Fatima ya aika aka fara kira masa bayan ta fito sun gaisa Ahmad ya fad'a mata yanaso tayi masa magana da Aysher ta amsa tare da shigewa cikin gidan.

Mintuna kad'an suka dawo tare da Aysher wannan karon d'akin Baffa akwai bak'i dan haka a k'ofar gida suka tsaya mota Ahmad ya bud'e ma Aysher yace tashiga ta zauna batayi musu ba ta shiga yazaga d'aya gefen yazauna ita kuma Fatima suna waje da mudansir.

Kan Aysher a sunkuye ta gaida Ahmad ya amsa tare da fad'in "Amarya bakya lefi kin wuni lafiya"?
Aysher tace "Lafiya kalau ya gajiya?

Ahmad yace " Lafiya k'alau Alhamdulillahi gobe zamu wuce gobe da wuri meye kike buk'ata kayan aurenki gobe zasu taho dashi wad'anda zasuzo tafiya dake daga cikin dangi na kina bukatar wani abu ne ki fad'amin mata na?

Kai Aysher ta girgiza kafin tace"Bana Bukatar komai Allah ya sauke ku lafiya Ubangiji ya k'ara bud'i"

Sabuwar waya Ahmad ya bata tare da sabon layi sannan ya ajiye mata rafar kud'i 'yan dubu d'aya guda d'aya yace"Ga wannan kud'in kirike a hanun ki kafin ku shigo kano ga waya zan dinga neman ki ba number kowa a ciki sai nawa a kwai kud'i nayi miki recharging nashi duk wasu shirye-shirye kuma Fatima da Mudansir zasu tsara komai ko akwai wani matsala kuma?

Bakomai Nagode amman da kabar kud'in babu abinda zanyi dashi.

Kai Ahmad ya girgiza mata kafij yace"A'a kidai rike banason aja maganar pls kayan wancan mutumin an mayar mishi da su ko ba naso ki tafi ta kayan shi koda Allura ne"

Aysher tace"Tun washe garin d'aurin aure yaturo danginsa suka zo aka had'a musu har kyautar da yake aiko min dashi na bayar daman banyi amfani da su ba"

That is my wife (Yauwa matata) Ahmad yafad'i haka yana murmushi"Naji dadin hakan da kikayi matata Allah yabani ikon faranta miki da rikon amanar ki Ameen"

Mudansir ne yazo yace musu dare yayi sosai fa dan haka a gurguje Ahmad yayi sallama bayan ya bawa Aysher kiss a kumatu badan ransa ya so rabuwar su da matar sa ba babu yadda zaiyi ne dole ya hakura cikin mota ma Mudansir tsokanar sa ya dinga yi"
[10/24, 10:09 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒

A gidan Radio Feedo taji sanarwan auren A.A Hameed wani ihu ta saki kafin ta zubo wani uban Ashar fad'i take yi"Karya ne Ahmad ba aure zaiyi ba dan bashi da wata mata sai ita yayi mata Alkawari"

Wayar ta ne taji yana ringing da sauri ta d'auka kawarta ce 'yar auta,
Feedo tana d'auka taji 'yar auta tana cewa k'awata kin samu labarin bikin A.A Hameed kuwa dan har an daura auren a yola biki za'ayi amaryan ta tare a nan kai kawata munada chasu fa biki ne na manya"

Kee 'yar auta kinci kaza-kazar ki na rantse da sarkin dake busan numfashi duk wanda ya halarci gurin nan indai yaje sunan sa k'o nanne ni Ahmad zaiyima haka ni zai yaudara na rantse da Allah daga shi har Amaryan tashi da duk wanda zai halarci gurin bikin sunan sa k'onanne......

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/26, 5:25 PM] Zeetty: [10/26, 5:17 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

_Ina jindadin zama tare daku, ina matuk'ar kaunar ku, 'yan Group din Zauren littattafan Hausa_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

Page 53-54

Ranar laraba mutanen kano suka sauka a garin yola domin juyawa da Amarya washegari, kar6a na mutum ci sosai suka samu daga gurin dangin Aysher da na mahaifin ta.

Sun taho da kayan aure akwati biyar da d'an kit cikon na shidan, masha Allah komai yaji dan Yadikko a ranar sai yanke jiki tayi a gurin ta fad'i daga an kira ta tazo taga kaya, kayane sun ninka na Honourable sau uku a tsada da kuma yawa.

Cicci6ar Yadikko akayi aka kaita d'akin ta tare da d'ebo ruwa aka yayyafa mata, ajiyar numfashi tayi gami da bud'e idonta tana k'arema d'akin kallo da jama'ar d'akin kafin daga bisani ta lumshe idanuwan ta.

Washe gari Alhamis da wuri aka shirya Aysher dan tafiya kano, motoci guda 5 aka turo daga kano dan haka sunyi komi nasu cikin shiri da tsari suka shirya kowane mota mutum 4 za'a dauka baya mutum uku gaba kuma mutum d'aya, wani abin burgewa shine garar da Baffa Usman yayiwa 'yarsa dan kuwa yayi k'ok'ari ba kad'an ba.

Motar da Aysher take ciki ita da Fatima ne da k'anwar mahaifin Aysher Adda Kubura, Sai gaba aka saka mutum d'aya, Ahmad yanata kiran wayar Aysher yaji muryan ta amman kunya ya hanata d'auka tanajin ringing d'in wayar a cikin jakarta.

Dan haka Ahmad yakira Mudansir dan yazo d'aukar Amarya a cikin motar sa ma aka saka Amarya, dan Ahmad yace bai yadda kowa ya d'auko masa matar sa ba sai Mudansir saboda tuk'in sa kawai ya yadda dashi.

Cikin salon tsokana Mudansir ya d'auki wayar tare da fad'in"Ango kasha kamshi munzo ance anfasa bamu amarya sai gobe juma'a"

"Dan girman Allah Mudansir dagaske?"

"Kwarai kuwa gamu dai anata fafatawa munce yau ango yakeson matar sa a kano"
Chapter 17 · 0% Book details