← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 21

Sashe 20

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yimin shiru, ki wuce mu tafi police station zamu je mukai kan mu, dan idan ba haka nayima Feedo ba, baza tasan cewar nafita tantiranci ba, zan tona asiri uban kowa ma ya mutu dan ubansa."

Dakyar Aysher ta mik'e, Ladi Reza ta kamo hanun ta suka fice, tasaka Aysher a mota, dakan ta taja motar suka bar k'ofar gidan da sauri.
Tunda aka kai Aysher sai yau ta fito k'ofar gida, sai yau taga haske a idanun ta, dan haka dak'yar take bud'e idanuwan ta.

Fagge Division Aysher taga an rubuta, guri Ladi Reza ta samu ta faka motar ta, ta zagayo ta bud'ema Aysher, tare da kamo hanun ta, kai tsaye cikin police station d'in suka shiga.

Ladi ce tafara magana da d'an sandan da tagani a tace masa"Yallabai gani nakawo kaina, na kasance mai laifin sace wannan yarinyar........ Yi shiru ('Dan sandan ya katseta daga maganar ta)."

"Bari a fara rubuta statement d'in naki," biro ya d'auko daga aljihun rigar sa, tare da jawo wani babban littafi kafin yace"ina jinki meke faruwa"

Nan Ladi Reza ta fara bashi labarin yadda akayi da cewar" Wata rana Feedo ta sameni a Club tacemin zata bani wani kwangila ni da k'awata Ummi 'yar tsinke, tayi mana alkawarin kud'i mai tsoka amman da sharad'in zata fara bamu rabi, rabi kuma sai bayan mun kammala aiki, toh mukuma jin yawan kud'in yasa muka amsa mata, kwangilar kuwa shine wannan yarinyar za'a sato mata ranar da akeyin dinner ta, Feedo itace ta samo min hatta kayan da zanyi amfani dashi, wanda shine ankon gurin dinner, ni da k'awata 'Yar tsinke muka kammala had'a komai, na yadda za'ayi a d'auko amaryan dan Feedo ta bamu labarin saurayin ta ne ya yaudare ta bayan sunyi alkawarin aure, toh mun gama mata aikin komai hatta gidan da aka ajiye yarinyar nan (tafad'a tare da nuna Aysher) gidan mu ne, saida Feedo taga komai yayi dai-dai, yau kwanan yarinyar uku a hanun, amman Feedo tayi mirsisi tace bazata biya mu kud'in mu bai sai bayan ta shawo kan Ahmad sunyi aure, kaji rainin hankali Officer? Ni kuma akan kud'i zan iya komai Aradu, shine nakawo kaina, suma a nemosu, ga yarinya nakawo a sadata da danginta, ni ba bakuwar zuwa gidan yari bane (Ladi ta k'arasa fad'a tana taunar cingam d'in dake bakinta irin na gogaggun 'yan duniya)."

Shiru 'Dan sandan yayi, dan tabbas yanada labarin amaryan da aka saceta ranar Dinner, ya tabbata Aysher ce, dan haka tisa k'eyar Ladi Reza yayi zuwa bayan kanta, kafin yafara kiran wayar DPO.
[10/30, 12:37 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒

Ahmad dai maraban shi da gawa numfashi ne kawai, saboda ko wane lokaci cikin zuga masa Alluran bacci nursing da doctor suke, dan yana farkawa zai fara tambayar anga Aysher kuwa? Idan daga nan Sai jiki ya rikice.

Dangin Aysher na yola duk sunzo hatta Yadikko tazo, zuciyar ta cike take fall da farin ciki, a zahiri kuma nuna wa take kamar tafi kowa bak'in ciki.

Kana kallon Baffa Usman kasan yana cikin damuwa, da labarin 6atar 'yar sa daya zo masa,

Suna zaune a asibiti cikin alhini da jimami, dan Ahmad ma yau ko farfad'owa baiyi ba ga damuwar rashin samun labarin inda Aysher take, wayar Alh.Aliyu ne yafara rurin neman d'auki, Alh.Aliyu ya d'auka tare da sallama.

"Hello! Wake magana?"

"Yauwa Alh.Aliyu ne dan Allah?"

"Eh nine, waye nawa?"

"Kana magana da DPO, na Fagge division, idan ba damuwa muna buk'atar ganin ka yanzu, kazo muna ganin kamar yarinyar da kuke nema ne, aka kawota yanzu......sai dai kazo kawai kaji sauran bayani."

Da sauri Alh.Aliyu yace"Ikon Allah! Alhamdulillahi DPO gani nan zuwa 'yanzu in sha Allahu, harda mahaifin yarinyar."

"Okay sai kunzo"

Ya katse wayar.

Su Umma ya kalla yace musu"Bari muje fagge da alamar Allah ya amshi addu'ar mu, anga Aysher"

Kowa ka kalli fuskar sa a gurin yana d'auke da annuri, sukayi musu fatan dawowa lafiya tare da dacewa.
***********

Rungume mahaifinta Aysher tayi tana kuka tare da fad'in "ita kam tafasa auren Ahmad, dan Allah Baffa ya taimaka a raba auren, dan ta wahala sosai", alama mahaifin ta yayi mata da cewar tayi shiru, nan aka zauna Ladi Reza ta k'ara bada labarin abinda yafaru.

Kowa a gurin yayi mamaki tare da Allah wadaran hali irin na Feedo, nan Ladi Reza ta bada kwatance na inda za'a samu Feedo da Ummi 'yar tsinke, take anan DPO ya tura 'yan sanda.

Aysher kuma sun yanke shawarar asibiti zasu kaita, dan tana buk'atar ganin likita itama.
Sun fito harabar Asibiti, wayar Alh.Aliyu tafara ringing, ganin number matarsa ya d'auka da sauri, kuka yaji Umma tanayi tare da fad'in" Alh.kazo asibiti yanzu dan Allah, Ahmad Allah yayi masa cikawa (taka'arasa fad'a cikin kuka)"

Ahmad ya rasu? Innalillahi wa'inna ilahi raji'un (Abinda Alh.Aliyu yafad'a kenan a bayyane).

Wani ihu sukaji Aysher tayi kafin ta yanke jikinta ta fad'i.

Cikin tashin hankali suka cicci6i Aysher, suka sakata a mota sai ZEEMAN'S CLINIC, hakika kana kallon wad'annan mutanen kasan suna cikin tashin hankali gwanin tausayi, kai tsaye A&E aka wuce da Aysher, Alh.Aliyu ko waiwayar inda aka kwantar da Ahmad baiyi ba, dan yasan tashi tariga ta k'are, saura aceto rayuwar Aysher (Baiwar Allah).

Nursing suka iso gurin da sauri, suka cicci6i Aysher dan d'orata a gadon marasa lafiya, HALIMA daman anan kike aiki? Baffa Usman ya ambata a rikice, wacce aka kira da Halima ta juyo da sauri kafin tace"Na'am Usman daman kana garin nan?"

"Yanzu ba lokacin wannan maganar bane Halima, taimaka ku shiga da ita ciki, ki taimaka ki ceto rayuwar 'yar mu"

"Kana nufin Aysher dana samu labarin bikinta itace a wannan hali? Yasalam kushige muje"

Da sauri suka tura gadon dan shigewa da ita d'akin bincike.

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[11/1, 6:26 PM] Zeetty: [11/1, 7:33 AM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

Page 63-END

'Yansanda sun kamo su Feedo da Ummi 'yar tsinke, iya wahala sun shata kafin su amsa laifin su, dan haka DPO ya tsaida ranar da za'a turasu zuwa kotu (wato kwanaki uku masu zuwa).

Ahmad ashe ba rasuwa yayi ba, doguwar suma ne, dan sanda aka fasa ihun mutuwar shi, basu kira likita ba, saida likita yazo ya dubashi, kafin ya sanar musu doguwan suma yayi.

Nan take daki yayi tsit suka saurara daga koke-koken da sukeyi, likita yakallesu tare da cewa"Kufita waje ku bani gurin zan dubashi dakyau", da sauri suka fice duk jama'ar cikin d'akin, hanyar cikin harabar asibitin duk suka nufa dan shan iska, fitarsu keda wuya suka hango Alh.Aliyu tare da Baffa Usman fuskarsu babu walwala, da sauri suka nufi gurin da suka hangosu.

Umma ce tafara magana bayan sun k'arasa da cewa"Alh. Lafiya kuwa muka ganku haka, kuns shigo asibitin baku k'araso dak'in da muke ba, Ina Aysher take?", duk wad'an nan tambayoyi Umma ta jerama Alh.Aliyu bata jira amsar shi ba, ta k'ara da cewa"kaji Ahmad d'in ma ashe doguwar suma yayi, rud'ewa mukayi shiyasa mukayi tunanin ya mutu, saida likita yazo tukunna yanzu haka ma doctor d'in yana d'akin Ahmad din."

Hamdala Alh.Aliyu da Baffa Usman sukayi a bayyane, kafin suka fara rokon Allah yatashi kafad'un Aysher.

"Meyafaru da Aysher kardai wanda suka saceta sun cutar da ita?". (Cewar Umma),

Alh.Aliyu yace" Kiran wayana da kikayi, tare da sanarmin rasuwan Ahmad, shine yasata suma amman ko badan hakan ba, daman muna da buk'atar taga likita".

Aunty Maryam (k'anwar maman Aysher) cewa tayi"Ikon Allah, wannan aure nasu akwai abubuwan Al'ajabi a cikin sa, Allah dai ya basu lafiya."

Gaba d'aya aka amsa da ameen yarabbi.

************

Suna zauzzaune cikin Alhini da jimami, wasu kuma suna tsaye, duk suna sauraron zuwan likita daga 6angare biyu na Aysher da Ahmad.
Mahaifiyar Aysher ce ta fara fitowa daga 6angaren Emergency, gurin su Alh.Aliyu ta nufo, kallon su tayi cikin murmushi kafin tace" Toh Alhamdulillah! Ta farfad'o, cikin ikon Allah ba'a sameta da wani matsala ba, kuzo mu k'arasa d'akin da take (takasa fad'in sunan Aysher, kasan cewar Aysher ce 'yarta ta fari, kuma guda d'aya tilo data mallaka, kunyace irin na fulani).

'Dakin da Aysher take suka nufa dukansu, sun sameta idanuwan ta a bud'e tana kallon sama, tana ganin shigowar su tafara kuka tare da tambayar su "Dagaske ya rasu?"

Fatima ce ta k'arasa gurin ta da sauri, hanun Aysher ta kamo tare da fad'in"Allah mungode maka, k'awata kece nake gani? Kwantar da hankalin ki, mijin ki yana nan da ranshi bai mutu ba, yi gaggawar mik'ewa ki tashi, saboda mijin ki yana buk'atar taimakon ki."
Gaba d'aya kunya tagama rufe Aysher, ta rufe fuskarta da hannun ta wanda ba'a saka mata k'arin ruwa ba, murmushi Aunty Maryam tayi tare da k'arasawa gurin ta, tanayi mata sannu, nan fa duk jama'ar d'akin suma suka d'auka fad'i suke "Allah yabaku lafiya".

Nurse ce tashigo da sauri tace" Alh.Aliyu ya k'arasa d'akin Ahmad Likita yanason magana dashi."

Dasauri suka fita daga d'akin shida Baffa Usman, kai tsaye 6angaren da aka kwantar da Ahmad suka nufa, Likita suka tarar a d'akin yana tsaye yadafa kan Ahmad, bayan su Alh.Aliyu sun k'arasa shigowa, likita ya dubesu kafin yafara magana"Toh Alh. Yaron kufa yana buk'atar addu'ar ku, sannan kuma yakamata aguji duk wani abu da zai sashi cikin damuwa, gudun kamuwa da wani babban cuta, kunyi sa'a ma jinin shi normal ne bai hau ba, ku matso kusa da shi idon shi biyu nayi masa magana, yak'i bani amsa.

Alh.Aliyu ne yak'arasa tare da fad'in"Tashi Ahmad mugodema Allah, Addu'ar mu ta kar6u, anga matar ka Aysher, yanzu haka tana cikin asibitin nan.
Zum6ur Ahmad ya mik'e tsaye kamar wanda aka tsikareshi, yana fad'in"Dan Allah Abba da gaske, ina take Aysher, suwaye suka aikata haka a gareta?"

Murmushi Alh.Aliyu yayi kafin yace"Koma ka kwanta, kaida baka da lafiya, zakaji komai idan kasamu lafiya."

"Lafiyata k'alau Abba, naji sauk'i, dan Allah Abba muje naganta."

Alh.Aliyu zai k'ara magana, likita ya dakatar dashi da cewa"Alh. ku rakashi ya ganta, hakan shine k'arin samun lafiyar shi, muje gaba d'ayan mu."
Chapter 20 · 0% Book details