← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 21

Sashe 14

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maigaiya mai Aiki Hon.Mahmoud bakaramin shiri yayima auren ba ganin zai auri karamar yarinya soyake a dirjeta dakyau anan yola kafin yawuce Abj dan bazai iya hakuri harsai tagama zana jarabawa ba.
Da badan wannan jarabawar nata bama da Honey moon zasu tafi
Ganin Aysher bata da wani wayewa a harkan zamantakewar aure shikuma bayaso ya kwaru yafiso takoya dan yadinga samun gamsuwa dakyau yayin amarcinsu dan haka yasa Woman leader ta gombe ta samo masa wata mata na musamman danta koyama Aysher yadda ake mu'amalar auratayya tsakanin mata da miji tare da gyaran jiki na amarya dilka da halawa harma da kunshi ita zatayima Aysher.
Yagana yar maiduguri ce dan haka tataho da shirinta na sati biyu ciff a garin yola.

Aysher taso ta botsare amman Fatima ce tabata shawara akan ta amince zaimata amfani tare da zazzare ido gurin yadikko.

Dan Haka aka fara yima Aysher gyara sosai cikin kwanaki hudun da suka wuce Aysher takoyi abubuwa da yawa.

Bayan gyaran jiki gaba daya Aysher tadawo kamar yar india ankoyama Aysher abubuwa kamar haka:-

*KISSAR TAFIYA*
*KISSAR MAGANA*
*KISSAR IYA ZAMA DA MIJI*
*KISSAR KWALLIYA*
*KISSAR TSAFTA DA KWALLIYA*
*TSAFTAR JIKIN MAIGIDA*
*SHAGWABA*

Duk abubuwan nan da ake koyama Aysher tana makale da kawarta tare ake koyar dasu a dakin Aysher.

Tsumi kuwa da gumba kai harda wani magani wai *TABAJE* cikin roba yagana take bama Aysher da madara.

Hakika ita kanta aysher tasan ta canja komai nata ya cicciko Ana saura sati daya biki Hon.Mahmoud yadiro a yola yadda yaga Aysher jiyayi kamar yaje ya rungumota kai Lallai Allah yakai damo ga harawa zai kwashi dadi a jikin nan.............
[10/19, 5:29 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒

Nura da mudansir sun sauka a yola ana saura sati daya biki dan Ahmad baisamu visa dazai taho Nigeria ba an hanashi yanzu haka yana kwance bashi da lafiya saboda tsananin damuwa.

Dan haka su Nura suka iso yola amman duk yadda zasuyi dan suga Aysher abin yafaskara saboda bata fita ko'ina dan gyaran jikin da ake mata ko sun aika ayi musu sallama da ita sai a turo yaron cewar wai bazatazoba aurenta xa'ayi.

Haka zalika sunnemi ganin mahaifin Aysher anshaida musu bazai dawo ba sai biki yarage kwana biyu.

Jikinsu ba kwari suka dawo kano
Nura ne yace "sunemi mahaifin Ahmad su baiyana masa komai yataimaka yaje yola kafin ranar daurin auren"

Ahmad suka kira dan fada masa shawararsu shima hakan yace yayi dai-dai nima dazau ambasador yace zaisamin hannu abarni nazo so pls barin kira Abban nawa Mudansir kuyi masa jagora idan na'iso shikenan Amman duk yadda za'ayi zandiro kafin ranar daurin auren Aysher koda hakan zaijawomin koma baya a harkan karatuna nayadda dana rasa Aysher.

Addua zakayita yi katashi yanzu katafi kaje kayi dawafi ka kaima Allah kukanka da'alama ma baka addua Ahmad soyayyar Aysher ya makantar dakai to tunwuri katashi tsaye da addua kaida kake gari mai Albarka haka garin da kana roka za'a amsa maka inji Mudansir.

Angama nawan nagode da tunatarwanka gareni wallahi namanta da wani abu waishi addua saboda tsabar rikicewa amman Insha Allahu daga yau nadaina bacci saina mallaki Aysher........

MAMAN HANAN
[10/20, 1:15 PM] Zeetty: [10/20, 1:11 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 42-43

©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA

Aranar da Mudansir sukayi waya da Ahmad da daddare suka isa gidansu Ahmad din kai tsaye suka shige cikin gidan dan maigadi yariga yasan mudansir batare da wani bincike ba
Guri Mudansir yasamu ya faka motarsa yafito shida Nura can suka hango saddiq yafito daga kofar dazata sadaka daga cikin gidan kai tsaye gurinsa suka nufa shima ganinsu yasa yanufosu yana Dariya.

Yace"Yaya mudansir ina wuni lafiya kuwa na ganku da daddaren nan"
Mudansir yace"Inafa lafiya dan rigiman abokina yatasomu Abba yana ciki kuwa"

Hahaha kai kake biyema Yaya Ahmad wallahi Abba yadawo tun 7:00pm barinyi masa magana

Shigar saddiq bawani dadewa sai gashi yafito yace Yaya Mudansir wai kushiga ciki bismillah kuzo muje.

Durkushe suke gaban Alh.Aliyu bayan sungaidashi tare da yimasa bayanin dalilin zuwansu.
Shiru Alh.Aliyu yayi kafin kuma daga baya yafara magana "Tabbas Ahmad yafadamin wannan maganar yarinyar nan amman dayake nasan halin shiriritarsa shisa banyi wani yunkurin zuwa gurin mahaifinta ba saboda ina gudun kar Ahmad yabani kunya duk kuwa da cewar nayi mamaki da Ahmad dakansa yace naje natambayo masa auren yarinyar dan abinda baitaba ceminba kenan.
Yanzu kai Mudansiru kana ganin Abokinka yayi Nutsuwar da za'a nemo masa aure?

Cikin sauri mudansir yadaga kai yakara da cewa" Tabbas Ahmad ayanzu idan kaga Ahmad saikayi mamaki ya zama babban mutum mai halin kwarai magidanci kamar yadda kakeso kagansa harya wuce tsammaninka Abba kataimaka kasa hannu abawa Ahmad auren yarinyar nan wanda za'abata kaji yanada matsala babba a tare dashi wanda hakan zaizamo cutuwa ga ita Aysher.

Nura shima yakarba da cewar"Abba taimako zakayima rayuka biyu rayuwar Aysher da Ahmad dan rashinta zai iya zamo babban matsala ga rayuwar shi Ahmad din wanda hakan zai jawo ZUBAR HAWAYE daga kowane bangare"

Shiru Alh.Aliyu yayi cikin dogon nazari kafin yace"Yaushe ne mahaifin yarinyar zai dawo yaushene kuma daurin auren?

Mudansir yace"Gobe Alhamis zaidawo daurin auren kuma ranar Asabar ne"

Toh shikenan gobe kuzo mubi jirgi zuwa yola dukanmu zanyima Alh.Lawan magana yasan da zuwanmu Alh.Labaran daga nan zaimin rakiya tare daku zanyankar muku ticket dikanku madallah da kokarinku nagode"

Suma godiya sukayi masa kafin suyi masa sallama subar gidan.

***********

Party kala biyu Hon.mahmoud ya shirya daya a nan yola za'ayi rabar da aka daura aure da daddare daya kuma a Abj shida jama'arsa.

Ya iso yola tuntuni Hon.Mahmoud kenan

Washer gari misalin 12:00pm Alh.Aliyu suka sauka a garin yola kafin sutaho sunyi waya da Ahmad yace shima yana nan zuwa Ranar juma'a ko asabar da sassafe.

Kai tsaye gidan Alh.Lawan suka fara sauka bayan gaishe-gaishe Alh.Aliyu yayi ma Alh.Lawan bayanin dalilin zuwansu Hakika Innawuro tayi farin ciki dajin wannan labari addua taringayi akan lamarin takara da cewa hakika Ahmad idan yasamu Aysher yayi sa'ar mace tagari.

Alh.Lawan ma haka yace yadinga fada musu kyawun halayen aysher da Nutsuwarta.

Wannan abu bakaramin dadi Alh.Aliyu yaji ba dajin wannan yabo da surukarsa matar dansa insha Allahu take samu. Dan haka Alh.Lawan yace su hanzarta tashi suje su samu baffa Usman tare da biyawa makarantar Almajirai suka bada sadaka ayi musu saukar karatun Qur'ani Allah zaba abinda yafi alheri.

Da yamma suka isa kofar gidan Baffa usman shima dai saukar safe yayi a garin yola.

Ikon Allah bayan sungaisa Alh.Lawan yagabatar da Alh.Aliyu a gurin mahaifin Aysher da bukatarsu suka kara da cewa duk da sunsan neman aure cikin aure haramun ne amman wannan akwai matsala.

Tambayar Baffa Nura yayi cewar shin yayi bincike kuwa akan Hon.mahmoud kuma Baba yakamata kasasu shida Aysher tunda yana gari yaxo suje ayi gwajin jini kasan yanxu ba'ayadda ayi aure haka saboda matsalar cututtuka da'ake dauka wajen mu'amala.

Kai Baffa ya girgiza kafin yace"Hakika naji dadin zuwanku guri na saiyau naji abinda ya dunkule yadannemin kirjina yasauka hakika nima bansan yadda akayi na bawa Aysher auren wannan mutumin ba ganina dashi nafarko hankalina bai kwanta ba Amman kwatsam daga baya naji inason lamarin danhaka idona yarufe nakasa tsayawama nayi wani bincike akansa amman yanzu Alh.Lawan ya za'ayi aure jibi nefa kar amaidani mutumin banza kuma mutumin nan babban mutum ne dan siyasa karna tozartashi kuyi hakuri hakika tun ganina da Ahmad nafarko naji yakwantamin araina ashe Ba mijin Aysher bane.

Kafin kowa yace wani abu Nura yayi saurin cewa "Baba kacema Mahmoud din yazo gobe ayi gwajin jina agani idan har ba'asameshi da wani cuta ba wanda Aysher zata iya dauka mun hakura a aura mata shi idan kuwa yana dauke dashi toh Allah yayi rabon Ahmad ne dan haka ashirye muke jibi adaurama Ahmad aure ko Mahmoud muna tafe da iyayensa gasu kagansu.

Na'am baffa yayi da wannan shawarar dan haka a gabansu yakira wayar Hon.Mahmoud yacemasa bayan sungaisa" Yazo gobe suje lab ayimusu gwajin jini dan tabbatar da lafiyan junansu"

Arikice Hon.Mahmoud yace shifa lafiyarsa kalau kuma baya zargin Aysher.
Baffa yace"Duk da haka kuzo zansa kanwar mahaifiyar Aysher datazo biki tayi muku rakiya kazo da wuri dan Allah"

Baffa yana fama fadin haka yakatse wayar.

Sallama sukayi dasu Alh.aliyu da bayan sun karbi number baffa akancewar xasu kirashi gobe suji abinda ake ciki.

A hanyar komawarsu gidane Nura yake sanar musu matsalar da Hon.Mahmoud yakeda ita hakika suma hankalinsu yatashi sukadinga adduar Allah tona masa asiri mugu macuci.
Sunkira Ahmad tare da fada masa yadda ake ciki tare da kwantar masa da hankalin cewar In sha Allahu Aysher rabonsa ce....

Ahmad komawa yayi dakin ka'aba yace gaba da kaiwa Allah kukansa tare da jiran akira wayarsa dan tahowa Nigeria.
[10/20, 1:15 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒

Saina Hallaka Nura nayi Alkawari idan Narasa Aysher sainaga bayan Nura dan shine munafiki a tsakaninmu da ita bayan doctor na Nura ne kadai yasan Wannan matsalar tawa.

Hon.Mahmoud kenan yake fadin haka a ransa yana zaune a dakin daya kama a hotel

Doctor dinsa yakira yayi masa bayanin halin tsaka mai wuyar da yake ciki.

Doctor yace "kakwantar da hankalinka ga shawara..........Nan dai sukayi shawarar abinyi tare da cewar yama kashe wayarsa gobe karyaje yabari sai jibi ranar da za'a daura aure.

Farincikine ya kama Hon.Mahmoud godiya yadinga yima doctor nasa tare da yimasa transfer din kudi masu yawa wanda doctor din zai turo masa da maganin da xaiyi amfani dashi gobe.............

MAMAN HANAN
[10/20, 3:09 PM] Zeetty: [10/20, 2:52 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 44-45

©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA

Aranar juma'a wato ana gobe daurin auren Aysher da Alh.Mahmoud kua ranar da akayi zaizo yaje ayi blood test saiya kashe wayarsa bisa ga shawarar da likita yabashi.

Aranar Doctor din ya iso yataho masa da maganin dasukayi magana

Nan take Hon.Mahmoud yazuke maganin Doctor yakara da cewar Honourable hakika kawuce gurin ko anje gwajin gobe baza'agano matsalarka ba idan maganin yakwana a jikinka shikenan zaiyi hidding matsalarka for 24hours so kayi kokarin zuwa goben with your full confidence dan baza'agano komai ba.

Sallama makudan kudi Hon.Mahmoud yayima Doctor sukayi sallama yajuya zuwa abj.

**************
Wunin Ranar juma'a baffa yanata neman wayar Hon.Mahmoud akashe duk hankalinsa yatashi dan ganin wannan abu da Hon.Mahmoud yayi hakika jikinsa yafara sanyi da wannan abu daya faru.
Chapter 14 · 0% Book details