← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 21

Sashe 7

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matarsa yakalla yace"Zuwaira wallahi idan har nabincika nagano cewar Ahmad shine yayi wakar nan da gaske inamai tabbatar miki zan daukeshi daga kasar nan naturashi can yankin larabawa a bautar dashi bazan ma barshi a nigeria ba kona kaishi gidan horo anan can kasar larabawa zanturashi aikin bauta tunda yaki karatun kuma zance banda lada karsu biyashi ko naira nagaji da halinsa tunda bazai fasa ba yana gama fadin haka ya haura sama.........

Umma saddiq takalla tace"kai ka tabbata shine yayi wakar nan?
Saddiq ahankali yace wallahi umma shine ainakira wayarsa jiya nake masa magana yace waishi yanada damuwar datafi wannan barima dai nasake kunna miki kiji har raping din turancin Yaya Ahmad ne....
Yadanna Alamar zaikunna wakar Umma tayi saurin dakatar dashi tana fadin"Kaci gidan ku karka kunna nidama yakunna wayar tasane ma sainayi masa magana amman barin kira yaya lawan naji........

MAMAN HANAN
[10/14, 1:47 PM] Zeetty: [10/14, 1:21 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
20-21

*TASHIN HANKALI*

Hankalin Umma yatashi lokacin data kira wayar Alh.lawan yake mayar mata da maganar karar Ahmad da aka kawo shekaran jiya dakuma nemansa dayayi a gidan yarasa a tun shekaran jiyan hankalin Umma yatashi dajin cewa ba'aga Ahmad ba dan haka ta katse wayar cikin sauri tare da haurawa sama gurin maigidanta.
Tasameshi tace"Alh. Kasassautama yaron nan kaga tun shekaran jiya yaya lawan yace yanemeshi baisan inda yatafi ba.

Cikin bacin rai yace"Meya shafeni duk inda zaitafi yatafi mana aiba yaro bane ace shine babba a gidan nan yakasa yima kansa future mai kyau toh duk inda zaije a fadin kasar nan yatafi zansa a nemoshi muddin abinda nake zargi akansa hakane narantse da Allah saina turasa can kasar saudiyya nasamu kauyen da zan kaisa har mungama magana da mutanen da zanturashi gurinsu bautar dashi zasuyi sosai nafada masu.

************

Adaren wannan ranar Ahmad yatakurama Mudansir dole yarakashi yaga Aysher yaga halin datake ciki.

Mudansir yace kabari mana sai gobe tunda yau takabaro anguwar kayi hakuri abokina...

Dakyar Ahmad yahakura amman washe gari da sassafe Ahmad yatashi mudansir yace masa tashi mutafi mu risketa a hanyar school mana

Cikin magagin Bacci Mudansir yace"Pls nawan kabari sai sun tashi daga school din zamu samu lokaci sosai muyi mata magana"

Nan madai shiru Ahmad yayi yana jiran lokaci yayi sunatafi.

12:30pm suka yima anguwar damare tsinke a hanyar makarantar su Aysher suka zauna a cikin mota suna hango makarantar karfe 1:00pm aka tashi 'yan makaranta suka fara fitowa idanun Ahmad yana hanyar da dalibai suke bulbulowa yakafesu da ido yanaso yahango ta inda Hasken idaniyar zata baiyana.

Can yahangota ita da kawarta fatima wani sanyi yaji cikin zuciyarsa dan ganinta su biyu kawai.

Dasauri yatabo Mudansir yana nuna masa ita mudan dariya yayi tare da cewa "kabari sudanyi nisa sai mubisu a baya saboda idanun malamansu kar yajawo mata matsala"

Kai Ahmad ya gyada dan baya bukatara abinda xaitaba lafiyar Aysher ayanzu.

Saida sukayi Nisa da makarantar yadda ba'a hango makarantar ma gaba daya kafin Mudansir yaja motarsa yabisu a baya,

Horn yadinga masu kafin fatima tacema Aysher su tsaya kamar dasu akeyin horn din.

Dakyar Aysher ta tsaya a lokacin Mudansir yasamu guri yayi parking Ahmad ne yafara fitowa dan haka hankalinsa yanakan Aysher.

Ganin Fitowar Ahmad ne yasa Aysher rikicewa tana girgiza kai tare da fadin Fatima zomutafi Yadikko tarabamu dashi kar aje a fada mata ta dakeni.

Rike Hanun Aysher fatima tayi tare da cewar ki nutsu ki saurareshi kiduba dakyau suma sunyi aiki da hankali babu munafikin dazaije yafadawa yadikko idan bani kuma kike zargi ba,

Jin haka yasa jikin aysher sanyi a lokacin Ahmad yakarasa karasowa gurinsu.

Sallama yafara musu suka amsa a tare gami da gaisheshi Ahmad yakalli Fatima yace"Kawarmu kitaimaka kifahimtar da kawarki abinda nakeji araina game da ita nasan kinfita wayewa dai-dai gwargwado nasan kin fahimceni tun randa nafara tareku a hanyar makaranta.........
Haba malam kabari mana nazo natayaka fighting din nagabatar da kaina agurinta da bukatarmu gareta mudansir ne yake fadin haka a lokacin daya karaso.

Sallama yayi musu shima suka amsa tare da gaidashi Aysher dai kanta yana sunkuye dan wani iri takeji a jikinta.

Sunana Mudansir Mustapha ni abokin Ahmad ne na hannun dama garinmu daya kuma tare muke karatu amman kowa abinda yake karanta daban.

Munzo da kokon bararmu gareki Aysher abokina yagani yanaso duk da anyimasa tsakani da gidanku wannan shine dalilin dayasa muka tareku a hanyar dawowarku daga makaranta dafatan zakuyi mana gafara wannan ce kadai muke ganin damar da xamuyi magana dake dan muji tabakinki dakuma inda zaku dinga haduwa kafin komai yazama normal.

Aysher takasa cewa komai sai wasa takeyi da hannun jakar makarantar ta.

Fatima ce takalleshi tace dan Allah kubamu lokaci nan da kwana uku zatayi shawara sai mu hadu anan wato nan da juma'a kenan.

Girgizakai Ahmad yafarayi dan yakasa magana mudansir ne yace"Kawar mu duk da bansan sunanki ba kwana 3 yayi mana nisa dan abokina yanada matsala cikin kwana ukun nan komai zai iya faruwa dashi akwai matsalar datake fuskantarshi bayan amincewa da soyayyarsa agurin Aysher"

Jin haka yasa fatima tadubi Ahmad _Hakika kana kallonsa da yadda yaxubama kawarta ido zakasan dagaske sonta yakeyi bana wasa ba kuma gashi very handsome dashi da'alama yana tattare da nutsuwa a tare dashi_

Fatima tagirmi Aysher da shekara biyu kawai dai kawance ne dakuma yanayin girman jikin Aysher kuma fatima tafi Aysher wayewa dan tana zuwa garuruwa dayawa gurin danginta idan anyi musu hutu har zance tanayi dan haka takalli Mudansir tace"sunana fatima gobe idan antashi kamar lokacin da kukaxo yau goben ma haka zakuzo muhadu a gurinnan zakuji amsar kawata"

Hamdala Mudansir yayi tare da yimata godiya Aysher dai takasa magana shikuwa gogan naku ya zuba mata tsumammun idanuwansa kamar yacinyeta danye.

Fatima tace zamu wuce sai goben.

Ahmad yace'Aysher bawani dan sweet word ne?

Murmushi tayi masa bayan tadago takalleshi kafin taja hanun fatima suka fara tafiya tace sai gobe.

A mota mudansir dariya yaketayima Ahmad dariyar shakiyanci tare da cewa Allah abin godiya gaskiya true love daban yake yau anyi maka kamun kazar kuku sakayyar babies din daka dinga kwasar rabar jikinsu ne yakamaka one time Hakki aiba wasa bane wow thank God yau ina class din naka ka kare a under 18 hahahaha.

Ahmad daya gama fusata tsaki ya saki dakarfi kafin yace gwara ni rabarsu nake kwasa kaida kake keta gona da iri fa zina kakeyi gwarani under 18 nakeso aurenta zanyi wallahi kai idan baka tuba ba kamar yadda natuba idan Allah yatashi kamaka saika rasa na aure ko ka auri bazawara idan Allah bai hadaka cutar tsida ba.

Shiru mudansir yayi dan yasan abokinsa yafishi gaskiya
[10/14, 1:47 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒

Kayi hakuri Alh.Aliyu kuskurene Ahmad yariga ya aikata amman karkayi fushi dashi dan Allah kabari muje abuja wannan taron idan mungama nan da kwana biyu ko uku sai muwuce yolan muji dalilinsa nayin wakar Hiphop CI yarasa ko SUTURA dazaisaka wanda harzai kaishi zuwa studio yin waka idan suna yakeso yayi a duniya ai ko a karatunsa yatsaya zaiyi suna ta bangaren wannan kuma za'ayi alfahari dashi a kasarnan basaita hanyar waka ba idan kuma sha'awa yabashi toh yayi na farko karya sake aikata na biyunsa" wannan bayanine daga bakin Alh.Labaran aminin Alh.Aliyu mahaifin Ahmad.

Bawani sauraransa da zanyi Alh.Aliyu turasa zanyi yaje can yayi hankali idan ba haka nayi masa ba inamai tabbatar maka Ahmad bazai taba kintsuwa ba ko aure nayi masa ba nutsuwa zaiyi ba zai hadu dani taso karakani naje nayi masa visa dan randa naganshi bazai kara kwana daya a Nigeria ba.

A'a kasassauta wannan fushin naka dan Allah ai wakar ba laifi bane yaran manya sunayi sosai suma sunfi yi a kasashen waje kadaiyi hakuri.

Nafariga nagama magana zoka rakani imigration office.

Wannan shine tattaunawa tsakanin Alh.Aliyu da amininsa Alh.labaran a cikin office din Alh.Aliyu.

*YOLA*

Aysher dai ta amince da soyayyar Ahmad da taimakon shawarar da Fatima tabata tare da kara mata karfin gwiwar cewa wannan ne kawai mafitar da zata samu idan Babanta yazo tasanarma Ahmad yaturo manyansa gudun auren Hon.mahmoud jin hakan yasa Aysher amincewa da soyayyar Ahmad acewarta *Dawani gwara wani*

Ranar juma'a 16-March ranace da tana daya daga cikin ranakun da Ahmad bazai manta dashi ba dan a wannan ranar Aysher ta amince da soyayyarsa duk da bata fada masa baki da baki ba saboda kunya amman fatima ta ari bakinta taci mata albasa.

Kudi Ahmad yaciro a accont dinsa masu dama awannan ranar ya dinga rabawa sadaka.

Gidan radio yola kuwa sunata kiranshi akan yazo ayi hira dashi dan masoya wakarsa sunason sanin wanene shi.

Yace musu ayi masa hakuri bashi da wannan lokaci a yanzu.......

MAMAN HANAN
[10/14, 7:12 PM] Zeetty: [10/14, 6:53 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 23-24

*Nasadaudar da wannan page din ga duk masoya wanda suke kaunar junansu dan Allah ko kuna tare ko kuma wata kaddarar ta rabaku toh wannan page din IS DIDECTED TO YOU GUYS*

Soyayya ta kankama tsakanin Ahmad da Aysher a kwanaki 2 kacal Ahmad wani mahaukacin so yakema Aysher wanda ya makantar dashi matsalar dake fuskantarsa

Da daddare yadamu mudansir da cewa shidai bazai iya bacci mai dadi ba saiyaga Aysher yau da daren nan duk abinda zaifaru saidai yafaru.

Mudansir yace"Haba nawan kar idonka ya rufe mana kaje kajawoma yarinyar mutane tashin hankali mana pls kayi hakuri gobe muje musameta ahanyar makaranta koda da safen ne ma kafin ta shiga class"

No Mudansir i can't wait idan bazaka rakani ba just give me ur key zantafi da kaina.

Mudansir dayaga dagaske yakeyi yamike a hanzarce tare da cewa Mayen Aysher zomuje ko gidansu ka hango hankalinka ya kwanta Romio"

Akofar gidansu Aysher sukayi parking Kafin su sami yaro yashiga dankira masa Aysher.

Wani yaro suka hango ya siyo pure water guda biyu a hanunsa Mudansir yakirashi ya nuna masa gidansu Aysher yace yayi masa sallama da ita.

Can jimawa saiga yaron yafito tare da cewa wai ga babanta nan zuwa.

Kallon juna suka shiga yi tsakanin Ahmad da Mudansir kafin mudansir yace"My man saika shirya Allah yaso manyan kaya muka sako yau zaka gaisa da mahaifin aysher"
Chapter 7 · 0% Book details