← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 21

Sashe 5

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sungama Nura yabukaci a turo musu Aysher sugaisa nan yar bingel tamike ahanzarce tashige gidan dan ita yadikko wai adole tana kunya anzo maganar auren yarta.
Aysher bata kawo komaiba cikin ranta tasa hijabi tafita zuciyarta fess.

Bayan tagaishesu ne tayunkura zatabar dakin nan Nura yayi saurin tsayar da ita tare da cewa"Aysher bazaki tsaya kugaida da mutumin naki sosai ba (Yafadi hakatare da nuna Hon.mahmoud wanda yakame a kuje cikin mamaki Aysher in-ina Aysher tafara cewa wa....waye...ni....ni ai bansashiba yau nafara ganinsa cikin mamaki Alh.Nura yace "Bangane ba kina nufin bada saninki aka tura mana hotonki abuja ba?
Gyada kanta Aysher tayi _Anan tagano kudin hoton da yadikko tabata ashe tallanta za'akai abj_...

A hanzarce Aysher tabar dakin tana tunanin me yadikko take nufi da haka
Damm kirjinta yabuga da Aure yazo mata cikin ranta a'a bazai yiwu ba dasauri Aysher tadakatar da zuciyarta daga wannan tunanin.

Yadikko tana ganin yadda Aysher tashigo gidan aguje dakuma hanyar dakinta data nufa idanuwanta alamun kuka takeyi dasauri tacema yarbingel yi sauri kije kijiyo mana kodai batayi musu bane ko halin tsiyarta ta shuka musu suka korota keda kikace wata kila tafito da dubu hamsin kyauta.

Ahanzarce yar bingel ta fice zuwa dakin.
Ko sallama babu take tambayar lafiya kuwa.

Hajiya daman baku mata bayani bane kuka tura mana hotonta abj..
Cewar Nura

Cikin Alamun rashin gaskiya Yarbingel tace " Aa....eh bata saniba saboda yarinyar tanada son karatu munbari dai komai yayi dai-dai bazata kiba ai tanada biyayya kuma ai da sanin iyayenta uwa da uba ai kunga irin karban mutumcin da mahaifiyarta tayi maku.

Cikin alamar gamsuwa da bayaninta Nura ya gyada kai tare da cewa bari muje mu kama hotel zamu dawo da daddare.

Cikin motar Hon.Mahmoud yakalli nura dake tuki yace Nifa Nura ko ana ha maza ha mata sai na auri yarinyar nan dan ina bala'in sonta ko Amina banyi mata irin wannan son ba soyayyace mai shiga farat daya ta shigeni ina sonta dayawa dabi'unta sunyimin sanyinta dakomai yazo dai-dai da yadda nakeso matata tazama.

Kallonsa Nura yayi yace"Nikuma Hon. Tausayintane yakamani bata dace da mai irin laluranka ba kamilan yarinya karama da ita inama zaka barmin nayi ta biyu da ita dan gaskiya........wani kallon da Hon. Ya watso mishine yadakatar dashi daga karashen maganar sa

Hon. Mahmoud yace cikin fusata "Baka da hankali nura nace baka da hankali dabadan wani abuba dakuma yadda danayi dakai sosai dasai nace ko yan adawa sun siye kane kariga kasan akan rashin aure zan iya rasa kujerata amman kake fadin haka toh nikam kozan fadi zabe bazan hakura da Aysher ba naganta inasonta dayawa ba kadan ba jina nake kamar saurayi.........

MAMAN HANAN
[10/12, 10:13 PM] Zeetty: [10/12, 9:41 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

Page 14-15

© ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP

Bangaren Ahmad kuwa hankalinsa yakasa kwanciya saboda rashin ganin Aysher a wunin yau kasan cewar asabar ne ba makarantar boko sukeda shiba kuma gashi yau batazo gidan ba _Ashe ganinta dayakeyi kullum rahama ne agareshi kodai son yarinyar nan nakeyi_ bazai yiwu kawai raina ne yabiya akanta inaso namaida mugun yawu

Da daddare Ahmad kasa samun nutsuwa yayi yanaso yaje club amman ya yanke shawarar mai gadi yarakashi gidansu Aysher abokansa sunata kiransa yana cemusu gashinan zuwa akarshe ya kashe wayar dan bayaso ya gayyaci kowa gidansu Aysher sai mudansir toh shima din ransa ya biya akan Aysher haryana kirarin cewa zai aureta tsaki Ahmad yasake dakarfi baba maigadi yakalleshi yace"kaida waye kake tsaki haka"

Ahmad yace" Hmmm natuna wani abu ne"

Suna dosar kofar yasamu yaro ya aika akira masa Aysher yaune zuwansa kofar gidan nafarko yakalli baba maigadi godiya yamasa tare dacewa yatafi kawai.

Cikin gidan kuwa yadikko bata tambayi kowaye mai neman Aysher ba tace aje ace masa tana zuwa a tunaninta su Hon.mahmoud ne dan sunce zasu dawo da dare.

Aysher ta kwalawa kira kafin tace cikin daure fuska mai nuna alamun kada ki kuskura tace"kije kofar gida bakinki sunzo kindaiji gargadin dana miki ki kiyaye"

Cikin sanyin jiki Aysher tafita kofar gidan.
🍒🍒🍒🍒🍒

Wani sanyi taji cikin ranta lokacin data hangoshi a tsaye cikin shiga ta kananan kaya tayi masa kyau kuwa _lallai ashe gwara wani kiyayyar akan wani itakam gwara zuwan wannan fiye da zuwan masu manyan tumbin na_ Aysher tafada aranta cikin kwarin gwiwa tare da sassauta hade fuskar datayi ta karasa gurinshi da sallama ya amsa ta gaisheshi ya amsa yana murmushi rasa abinda zaice mata yayi _Shidai yaganta hankalinsa ya kwanta_

Cikin wata irin murya yace"Maiyahanaki zuwa yau"

Aysher tace"Yadikko ne ta dakatar dani wai zatayi baki but har sunzoma"

Kuramata ido Ahmad yana kallon bakinta yadda take magana abin yabashi sha'awa.

Yace"meye zakiyima bakin kuma mazane ko mata"

Aysher tace"Mazane wai daga abj"

Cikin nuna Alamun kishi Ahmad yace"Girkin naki sukaci harkin iya girkin abincin da wasu zasuci mstwwwww Ahmad yaja doguwar tsaki kafin Aysher tabashi amsa sai sukaji tsayuwar mota.

Waiyagawa Sukayi dan ganin kowaye
Nura ne yafara fitowa dan neman yaro yakira musu Aysher.

Dammm kirjin Aysher yabuga dan ganin Nura datayi tagane sune sukazo da rana
Ahmad yana lura da ita.
Waige-waigen da Nura yakeyine dan neman yaron da zai aika idonshi ya hango masa Aysher
[10/12, 10:12 PM] Zeetty: Dasauri yakarasa gurin dasuke yayi sallama kafin yace"Dan Allah abokina kadan sallameta yanzu maigida yana mota yana jiranta"

Wani matsiyacin kallo Ahmad ya watsa masa tare da cewa"Maigida? Shi maigidan dan gidan uban waye dan iskanci muna tsaye kace wai nasallameta mai gida yana nemanta....ke daman kinsansu ne
Suna zuwa gurinki?

Cikin yanayi na tsoro saboda gaba daya Ahmad ya canja tace"Sune bakin yadikko wanda nayi musu girki dazun sunedai wanda nake fada maka sunzo daga abj"

Wani malalacin kallo Ahmad yabita dashi kafin yace"Saurayinki dai ko kinyi masa girki yaci makaryaciya nizaki yima karya wato har zance kikeyi a mota ko?
Kai Aysher take girgiza masa alamar bahaka bane
Cikin tsawa yace"Kifadamin zance kike dashi a mota yar figigiya dake kin iya jaraba"

Nura daya fuskanci zance Ahmad inda yasa gaba kuma da alamar rashin yarda da ita daya darsu a cikin zuciyarta yanzu yace aransa _Barin wanke yar mutane ni ai tausayima take bani da alamar bata da budewan ido_ dan haka yadafa kafadar Ahmad tare da cewa "Calm down my friend duk karikita yar mutane toh muma yau muka fara zuwa gurinta bata ta6a haduwa damuba sai yau kuma ga menemanta can a mota"

Ture hannunsa Ahmad yayi cikin masifa da hargagi yafara fadin dan iskanci shine zaice taje tasameshi a mota kai kafito kabasu guri wato yayi mata duk abinda yaga dama ko macuta azzalumai toh ni Ahmad nace bazata jeba zanga uban daya isa yasata taje gurinsa kaje kafada masa tunda kaine kanzaginsa idan baija motarsa ba daga gurin nan Narantse da Allah yau koni koshi motarku saita canja kammanni"

Sum!Sum Nura yaja jiki yabar gurin dan ganin yanayin Ahmad duk abinda yace zai aikata zaiyi din daga ganinsa yanada jarumta
Mota da sauri batare dayacema Hon.Mahmoud komai ba yaja motar sukabar gurin.

Ahmad kallon Aysher yayi hakika yanayinta yabashi tausayi amman shikam yafi tausayama kansa a yanzu yakalleta yace"Waye ya hadaki da wadannan"

Aysher tace yadikko ne.

A ina suka ganki?

Tace"Hotona wai ta tura musu abj"

Dafe kai Ahmad yayi tare da fadin Oh my God! Kika dau hotonki kika bata why Aysher why pls....kansa yana sunkuye dan wani irin sarawa dayake masa (yanada ciwon kai na gefe daya magrine)

Aysher tabude baki tace"Wlh....stop Aysher just Go!Go!! I said go yafada da karfi cikin tsawa dagudu Aysher tabar gurinsa dan ta tsorata gida tashiga dasauri.

Ahmad yadade a gurin kafin yaja kafarsa dakyar dan zuwa gida _Maman hanan tace Ahmad kaida kake sha'awarta meye nashiga damuwa dan masoyinta yazo mujedai zuwa_

*************

Kai Nura meye kawani figi mota aguje kabar gurin batare da kayimin dogon wani bayani ba bayan naga kajima a waje har lekowa nayi naganka da My love tare da wani.

Wani kallo Nura yayi masa azuciyarsa yana takaicin hali irin na Hon.Mahmoud dan haka ya shaftaro karya yace masa"wato maigida saurayin daka ganta dashi abuge yake yasha tayi masa karo yayi mankas gefen hagunka kuwa dan baka kallon gurin ne abokanansa ne yan bana bakwai sunyi masa rakiya sunkai su goma danaje gurinsu nima natafine da niyyar hayaniya amman inaji yana kwala musu kira nanemi sulhu daga karshe rantsuwa yayi dacewa idan bamu ja motarmu daga gurin ba zasu cinna mana wuta dukan mu mu kone yakara da cewa akan Aysher zai iya rasa ransa koya hallaka mutum shine naji tsoro nazo naja motar muka tafi dan naga alamarsa babu Allah a ransa wani abin takaicin ma Aysher da alamar tana bala'in sonshi dan yana magana tana cewa nagode nawan kubar kofar gidan kunji abinda masoyina yace muku.

Tsaki Hon.mahmoud yayi kafin yace"Lallai za'ayi mutuwar kasko kuwa dan akan Aysher nima zan iya rasa rayuwata kai zan hallaka mutum akan wannan babyn kaima dai matsoracine amman kuma kanada gaskiya bamusan abinda suka taka ba mubari gobe muzo da rana ido na ganin ido kuma mu fadawa mahaifiyarta cewar arabata da wannan dan iskan yaron kawai may be komawarmu ma sai jibi monday kawai.

_shege kaima saikace wani na Allah ne banda yanzu da duniya takoyama hankali wato bazaka hakura da yarinyar nan ba kenan maye kawai_ Nura ne kefadin haka a zuciyarsa a fili kuwa cewa yayi yadda kace haka za'ayi Honourable.

MAMAN HANAN
[10/13, 3:15 PM] Zeetty: [10/13, 2:45 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 16-17

Wayyo Allah nashiga uku dan Allah yadikko kiyi hakuri wallahi ba dan iska bane a gidansu Alh.lawan yake Allah baitaba zuwaba sai jiya cikin shesshekar kuka Aysher take fadin haka dan hakika tadaku yau kam agurin yadikko.

Barta haka Mama hakika tadaku sosai yau ai zataji maganarki wannan uban duka haka ni wallahi sainajima kamar jikina kike duka kawai dai gidansu yaron zakije aja masa kunne yarabu da ita, ita kuma daga yau nahanata zuwa aiki gidan zandinga biyanki abinda kike samu duk wata har ninkawa zanyi dan yaronnan baida imani daga ganinsa jiya fa dakyar muka sha mama _Hon.mahmoud ne ke wannan bayanin harda karya wai yaga Ahmad kamar dagaske_
Chapter 5 · 0% Book details