← Book details Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 21

Sashe 1

Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[10/9, 8:52 AM] Zeetty: [10/9, 8:46 AM] Maman Hanan: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE

Page 1-2

*Assalamu alaikum barkanem be nyalomare midon yela on nanai beldun kubaruji am*

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka dafatan zakuji dadin wannan labarin*

*Wannan labarin nawa kagaggen labarine banyishi dan cin zarafin wani ko wata ba basira tace ba taki/taka bace sarrafashi ta kowane hanya zan dauki mataki aguji aikata hakan*

*Idan yayi dai-dai da rayuwarki/ka ayi hakuri Arashin sanine*

*DAN UWA RABIN JIKI*
Ubangiji Allah yagafarta maka hakika nayi rashi wanda bazan ta6a iya kankaresa daga raina ba harsai ranar da tawa tazo gareni,
Na jijjiga nayi kuka asanda labarin mutuwarka ya riskeni Allah yasa mutuwa hutuce a gareka Samarin Aljanna Allah yabamu hakurin Rashinka *Ibrahim Sulaiman* bazan manta dakaiba dan kana d'aya daga cikin wanda kake bani Kwarin gwiwa akan fara rubutun littafi Allah ga bawanka nan ya Allah kasadashi da rahamarka muma idan tamu tazo Allah kasa mucika da imani *We love u but Allah love u more* Dr.Sule family munyi rashin dan uwa mai zumunci
©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP

🍒🍒🍒🍒🍒

Garin yola kowa yasan mazauna wannan garin mafi akasarinsu fulani ne.

Anguwar DAMARE yan matane da samari yara da manya sunyi cincirindo a gurin diban ruwan Borehole da ake siyarwa bokitin sharon Naira Goma bokiti uku Naira ishirin,
Yawanci anfi zuwa gurin ranar da aka kwana biyu babu ruwa kasan cewar mafi akasarin wadanda suke siyan ruwa a gurin Masu saida ruwan jarka ne wanda suke amfani da kuran ruwa (amalanke)
Idan kaga wata yarinya ko yaro sunzo siyan ruwa gurin toh ba shakka iyayen marasa karfine sosai ko kuma masu cikakken son banza.

Aysher tana zaune a gefe tanajiran layi yazo kanta dan batazo da wuri ba saida Yadikko taga ankawo wuta sannan ta turota
Dan idan da wutan nefa zaka sayi ruwan yafi arha akan idan sun tayar da Gen.

Aysher tasowarta kenan daga makarantar boko harta zauna zata fara cin abinci yadikko tace tatafi ta nemo mata mai ruwa.
Toh ganin ankawo wutan Nepa ne yadikko tace tazo tasiya mata bokitin Penti babba guda uku.

Kasan cewar Aysher ba ma'abociyar son hayaniya bane yasata komawa gefe tazauna tanacin dankalin hausa danye wanda kawarta fatima Alhasan tabata daman ta6oye a jakarta ganin zata taho diban ruwan ne yasata daukowa aboye ta taho dashi.

Sai da tayi awa d'aya kafin akazo kanta aka zuba mata tadinga daukar bokitin da guda d'ai-d'aya harta gama tana shiga gidan da sallama kanta dauke da bokitin sahun karshe tana mai farin ciki zataci abinci ta wuce makarantar islamiyya dan shirye-shiryen saukar karatun Qur'anin da zasuyi nan da sati biyu masu zuwa.

Bayan tagama cin abinci ta mike ta wanko hanunta daman tayi sallah tundaga makaranta
Hijabinta ta dauko da alqur'aninta ta daga labulen yadikko cikin yaren fulatanci tace"Yadikko nagama zantafi makaranta"

Yadikko tadago fuska a had'e tace"Bazaki tafi yanzuba kitafi gidan Innawuro kigama mata aikinki na safe da baki kammala ba kafin kizo kitafi inyaso idan kidawo daga makarantar ko sha ukun dare ne saiki gama aikin gidan nan
Ina dalili ubanki yabugi kirji yace karatu zakiyi toh gaki ga karatun naji dadin wannan saukar da zakuyi aradun Allah kina gama saukar nan babu wata islamiyyar da zaki sake zuwa aiki zaki kamayi tukuru gidan Innawuro tunda ubanki yahana kimin talla toh ai shikenan"

Cikin sanyin jiki Aysher taja kafarta maida Qur'anin d'akinta kafin tafito tabar gidan takama hanya dan zuwa gidan Innawuro.

WACECE AYSHER
Aysher Usman Abdullahi shine cikakken sunanta shekarunta 16 tana S.S one a boko, islamiyya kuma tana ajin karshe Aysher cikakkiyar bafulatana ce dan idan taga dama saita wuni batayi maka magana da hausa ba miskilace takarshe kyakyawa balaifi.
Mahaifinta yana harkan gwarine zuwa lagos balaifi yanada rufin asiri dai-dai gwargwado.
Mahaifiyarta kuwa aysher bata santa ba sai a hoto.
Ayanda mahaifin Aysher yake bata labari tuntana wata takwas wata rana da sassafe ta tsallake tabar Aysher akan fo tabar gidan.
A lokacin yadikko ce uwar gida tanada yara 3, Muhammad,Bilal, da zulai wanda yanzu haka anyi mata aure dan yadikko taki yadda tayi karatu.

Bayadda ba'ayi da mahaifiyar Aysher tadawo gidan ba amman taki dawowa kuma balaifin tsaye bana zaune tsakaninta da Baffa Usman (Kamar yadda ake kiransa)
Bayanda baffa zaiyi dole yasaki matarsa yanaji yana gani bakuma sonta bane bayayi.

Bayan tagama iddarta labari yazo masa cewa Hafsat (mahaifiyar Aysher ta tafi kano karatun aikin jinya)
Fatan alheri yayi mata tareda da cewa"inda rabon musake zama zamu zauna tare Hafsat"

Anguwar damare takasance anguwa wanda take gauraye da talakawa da masu kud'i.
Gidan inna wuro yakasance d'aya daga cikin gidaje masu sukunin anguwar
Aysher tana zuwa aiki gidan ne bisa neman alfarman da Yadikko tajeyi gidan batare da sanin aysher ba ta samo mata aiki gidan danyin wanke wanke shara da girki dan innawuro tana aiki a Nepa bata zama agida sosai mijinta kuma ma'aikacine a CBN.

Mahaifin Aysher baisan 'yarsa tana zuwa aikatau ba kuma yadikko taja mata kunne da cewa muddin ta tona mata asiri saita kaita lahira.
Aysher taji tsoro dan haka takame bakinta kam
[10/9, 8:52 AM] Maman Hanan: ***********
Durkushe yake gaban iyayensa mahaifinsa yanayi masa fad'a kansa a sunkuye.
Alh.Aliyu yacigaba da cewa"Nagaji nikam da kararka da ake kawomin duk gidan nan kaine babba shekarunka 28 amman ace haryanzu bakayi hankaliba yau kaine gurin wannan yarinyar gobe gurin wancan da zarar ance katuro manya saika gudu hartakai takawo ana zuwa ana sallama dani tare da gargad'in muddin baneman aure zakaje gurin yarinyar mutane ba kadaina zuwa

Nibansan meye yadawo dakai Nigeria ba daga Ghana kace lallai a Nigeria zakayi masters toh nikam nagaji kashirya tafiya cikin satin nan zan nema maka karatu a reshen makarantarku dake India.
Alh.Aliyu yana gama fad'in haka yabar falon yahaura sama ransa a 6ace.

Idanuwansa sun kad'a sunyi jazur Alamar 6acin rai yadubi mahaifiyarsa yana mai cewa"Umma kitaimaka kisa baki kar aturani India wallahi basai ankaini wata k'asa zan k'arasa lalacewa ba anan dinma akwai mataimaka dan haka kawai zancen zuwa india a fasashi"
Yana gama fad'in haka shima yabar falon fita yayi gaba d'aya daga gidan.

Umma tayi shiru tana jinjina maganar 'Dan nata cikin zuciyarta haqqun haka maganarsa take tasan d'anta bayajin magana amman tafiyarsa Ghana karatu danyin degree dinsa yadawo da wasu mugayen d'abiu marasa kyau babu abinda yaragu saima karuwa dayayi zuwansa can saukinta ma yadawo da sakamako maikyau.

Umma tamike jiki ba kwari yazaman mata dole tasamu maigidanta dan lamarin d'an nasu gaba yakeyi ba baya ba.
Saman tahaura itama tasameshi yana zaune a falon yana kallon news dan haka tashiga da sallama
Ya amsa mata,
Guri tanema tazauna tana fad'in"Alh. Kayi hakuri abar yaron nan yazauna a kasar nan yayi karatunsa dan Allah idan ba hakaba yak'ara komawa wata kasar ina gani abinda zaisake koyowa saiyafi haka kaduba maganata"

Alh.Yusuf yace"Shawarar da Alh.Labaran yabani kenan yanzu mukq gama waya dan haka zanbarshi anan din amman ba'a kano ba"

Umma cikin jindad'i tace"Shikenan Alh. Inaganin kawai katurasa Yola gurin yayana Lawan yazauna a gidansa nasan zaisaka masa ido sosai.

Kaitsaye Alh.Aliyu yayi na'am da shawarar matarsa.

WAYE ALH.ALIYU
ALH.ALIYU HAMEED shine cikakken sunansa d'ankasuwane nagaske a garin kano hamshakin maikud'i ne gefe guda yana harkar siyasa kad'an.
Matarsa guda d'aya ce maisuna Zuwaira wanda yaranta suke kiranta da Umma
Yaransu guda 7 Ahmad ne babba sai Saddiq, sai Amatullah, Nusaiba,Sai waleed da auta Safiya.

Anyi auren amatullah watanni 3 da suka wuce bayan tayi diploma a legal.

Ahmad tun tasowarshi mutum ne marajin magana ga taurinkai bashi da tsoro ko kad'an yanada fad'ar gaskiya baya 6oye laifinsa indai antuhumesa kai tsaye yake amsa laifinsa indai ya aikata dagaske.

Yanzu shekarunsa 28 yayi karatu a MAHATMA GHANDI UNIVERSITY dake accra a ghana ya karanci Medicine yanzu shekarunsa 2 da watanni dagama degree dinsa yadawo gida.

Ahmad masoyin matane acewarsa mata abin sone.
🍒🍒
Fitarsa daga gidan kai tsaye dabansu yatafi (Majalisa) da suke had'u wa a fine time restaurant
Yasamu abokansa wanda akasarinsu yaran masu hanu da shuni ne sunata d'an bushe-bushensu anan shima yanemi guri yazauna tare da karb'an tasa nad'in tabar wiwi din.
Bayan yagama zuzzuk'a yakalli Mudansir (abokinsane sosai sunfi shiri) yace"Ya nawan zo mu lafe anguwar birget mana gurin wannan 'yar k'wai-k'waidin
Mudansir yakalli Ahmad yace" Dole ne mu lafe nawa yafad'a tare da mikewa tsaye"

Wani daga cikin abokansu ne yakalli Ahmad yace"Nawa-nawa"

Ahmad yace"Ya akayi ne nawan"
Abokin yace"Nawa kanason mata"
Ahmad yace"Dole ne naso mata abokina domin sud'in abin sone"

Yakarasa fad'a tare da tafiya gurin daya faka motarsa mudansir yana biye dashi.

MAMAN HANAN
[10/9, 1:42 PM] Zeetty: [10/9, 12:18 PM] Maman Hanan: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 3-4

*Tabbas al-qur'ani mafitace ga dukkan wani musulmi*

©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP

Batare da 6ata lokaci ba aka samarwa Ahmad Aliyu Hameed admission a AMERICAN UNIVERSITY OF NIGERIA (APTI) university na garin yola.

Da daddare babansa yake sanar masa tare da cewa jibi zaka tafi dan anriga anfara lectures nima alfarma akamin aka dauke ka
Dubeka Ahmad babba dakai kaida za'ace kana tsaye akan karatun su saddiq amman kaine baya komai saina tsaya nayi maka saboda shiririta irin taka you are not serious about your studies at all but nasan maganinka kana gama masters dinnan aure zanmaka idanma baka kawomin mata da kanka ba nizan samo maka"

Ahmad kansa a sunkuye yace"Nagode Abba Allah saka da alheri"

Alh.Aliyu fuskarsa dauke da murmushi yace "bakomai Allah yakara shiryamin kai"

Umma tace "Amin"

Mikewa Ahmad yayi yana cema iyayensa zaije gidajen abokansa yafara musu sallama tun yau.
Suka masa fatan dawowa lfy yasakai yafita.

Kai tsaye gidansu Mudansir yafara zuwa yake bashi labarin tafiyarsa yola jibi domin yin masters
Cikin farin ciki Mudansir ya rungume Ahmad tare da cewa"Like seriously abokina nima wallahi jibin zantafi dazun tsoho yake fadamin (Baban mudan) daman inaso naje na fada maka ne tare da alhinin xa'arabamu ashe muna tare wayyo nawan"

Ahmad yace "Kai amman munada sa'a zomu tafi Musamu guys mudan busa kafin anjima"

Haka suka shige motar da Ahmad yazo da ita dan zuwa fine time restaurant.
Chapter 1 · 0% Book details