← Book details Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace toni kabani ita inaso yace a habadai Dr aikafi 'karfinta,yace a,a 'Dana me irin halinka xanbawa ,yace Allah yakiyaye ai sai Mara aji ,yace a a Abdul karfa wataran axo ana danbe dakai akanta,yace in Allah yayarda hakan baxata ta6a faruwaba a kaina ba ,shidai Dr dariya kawai yakeyi,yace to anemo mata abinda xataci,yace to Dr yana dariya shima yanayi.yana fita likitan yacigaba da dariya,yace kanata dawainiya da mutum sannan kanata aibatashi ai kyan Abdul suyi abota da nasir tunda halinsu daya,yamike ya koma dakin salwan yace ya jikin naki tace da sauki ,tace dan Allah Dr kasallameni banasan kwana a asibitin yace to baga yayankiba tace a a katemakamin ai nasamu sauki ya kalleta yace to sai abinda yayanki yace ,tayi shiru tarabu dashi ya kalleta yasan dauriya kawai takeyi dan tanajin jiki,Abdul ya bude kofar ya shigo da leda a hannunsa yace sannu Dr
Yace yauwa yadire ledar hannunsa take away ne kusan roba biyar ya bude daya yasa cokali ya mi'ka mata,idan kinga dama kici idan bakiga damaba ki xauna yinwa takasheki,ke kika sani danni ko kuka baxanyiba,kar kari muje mu binneki muna murna salwa ta mutu munhuta,Dr ya kalli Abdul din yana dariya sosai yace hukumar wannan Asibitin xataci tararkafa,sbd kana daya daga cikin mutanan da kake 'karamata hawan jini ,kainefa da kanka kakawota Asibiti danta samu lfy ,Amman kuma kana gayamata abinda yake tayar mata da ciwo,to nayi shiru tunda kafadi hakan,ya kalleta dallah malama dauka kici abinci danni ba bawanki bane nasiyo abu ki'kici shidai likitan banda dariya babu abinda yakeyi ,danshi a yadda ya fuskanci yarinyar bamata damuwa da abunda yake yi mata,ta dan garacin abincin a hankali gashi abincin da 'dan yaji,Amman babu damar mgn yanxo agayamata abinda xai daga mata hankali, bataci da wani yawaba sbd yajin abincin ,ya mi'ko mata lemo da ruwa shidai likitan kallan su kawai yakeyi suna bashi sha,awa,saida ya tabbatar da tagama da komai ,sannan yajuyo kan likitan, yace Dr bisimillah yace a a nawa yana office yana jirana,ko so kakeyi aci tarata a gida ,yace dan ka'kici sai kayi laifi ,yace sosaima kuwa ,wayar ya Abdul ce tayi 'kara ya dauka yace aiduk ga wadda tajimin na manta dashi ,dan Allah habu direba ka kawominshi ai kasan Asibitin da muke xuwa dasu mommy to sai ka'karaso ba a dadeba suka shigo sultan ya rungumeshi yana kuka shine uncle katafi kabarni ko,to yi hkr baxan sakeba,sultan ya kalleshi uncle nayiwa aunty sannu ya gyada masa kai,yace sannu aunty Allah yasawake ,ko kallan inda yake banyiba,kaga uncle bata kulaniba ko ,kuma nifa sannu kawai nayi mata,to karta sake kulaka mana ai kaima kahuta,suka tafa sukasa dariya kamar wasu sa ,anni,likitan yace gaskiya Abdul kanaji da yaronnan ,kuma kace min ba kayi aureba ,shidai Abdul ya dauko robar abinci guda daya yana bawa sultan a naki ,sannan ya kalli likitan yace munrabu da mamansa likitan yace 'karyafa babu kyau Abdul, ya kalleni yace ni sainagama da Salwa suke kama ,Abdul yace Allah ya kiyaye haba likita ya kake hadamin yaro da wannan banxar ni yarona me mutuncina ba irintaba,shidai likita yayi musu sallama ya tafi dan wannan abunda Abdul din yakeyi saiya hanashi aiki yayi musu sallama ya tafi,har dare ba a sallamesuba dayan likitan ya tafi sai wani yaxo yace sallama sai gobe,shi dai Abdul ko a jikinsa ,salwancema ta damu sosai,da abinda likitan ya fada,daman gado dayane a dakin sultan yayi bacci ya dorashi a gadon ,waishi besaba da kwanciyar 'kasaba,kuma babu Wanda ya isa ya takura masa,ni dai kawai jinsa nakeyi ,wata xuciyar ta dinga xugani akan na hantsilo yaron ya fado naga abinda xa ayi ,sai dai kawai narabu dashi ,shi kuwa kwana yayi idonsa biyu yana hidimar sultan ,likitan safe yana xuwa ya sallamemu,a kofar gida ya direni ya koma da baya da motar shida sultan, inajin sa yana cewa acigaba da xama da yinwa ,naga Wanda xai kaiki Asibiti kuma kicigaba dasa soyayyar namiji a xuciyarki wataran sai sun haddasa miki ciwon xuciya ,nidai idan dasabo nasaba dajin irin wannan maganganunsa,kodana shiga gidan umma kawai nagani Abba harya fita,nace sannu umma tace yauwa salwa ya jikin ,jiya naso xuwa nadubaki Abdul yace Na xauna babu wata matsala nayi xamana ,wannan yaron da kirki yake sai dai Allah yabiyashi ,koda Abba yabashi kudin sa kin kar6a yayi ,babu yadda Abba beyidashiba ya'ki kar6a, wai aishima yayan salwane ,dan xai iyayi mata komai akan ya faranta mata ,suka dinga yi masa godiya sosai dasa albarka ni kuma idan naxauna ina tunani sai kawai abin yadinga bani mamaki,gaskiya dai ya Abdul mayaudarine su duk a tunanin iyayena kaunata yakeyi tsakani da Allah ,basusan duk yaudararsu yakeyi ba ,duk maganar da tafito daga bakinsa ita yake dan'karawa mutane ,Ammansu su umma basu gane halinsaba ,koda yake ni kadai ya tsana sbd yadda ake fadar kirkinsa da girmama nagaba dashi ,gashi idan mutum yana ciwo yadinga tausayinsa kenan,ni kadaice baya tausayi ni yamace ya tsaneni baya kaunar ya bude idonsa ya ganni ,narasa abinda nayi masa,koda yake ga xargin da yakeyimin,ni kuwa Allah ne xaiyimin sakayyar 'kaxafin da yakeyimin ,da wuri yaxo muka wuce school kamar ko yaushe dai a get ya saukeni bayan ya sauke sultan ,daman shine laccar mu ta farko nashige Na xauna muka dinga hira da fauxee ,har take cemin kinyi shirin xana test din malam halifa kinsan shima babu daga 'kafa ,nace Allah ya kaimu goben ganin gobenshine wuyar ,yashigo yanata xuba 'kanshi sai dariya yakeyi matasan ajin sai xugashi sukeyi sai babban yaya ata6aka a ta6a masifa ,Allah yabarmana kai ,shidai sai dariya yakeyi ,yana cikin yi mana laccar sai yadaina yashiga wata mgnar "yan matanmu inayi muku nasiha a koda yaushe kudinga kare mutuncinku,dan ita mace abar tausayice ,dan Allah kugane kulura kumaida hankali akan karatunku dan yanxo shine gatanmu yanxo,bara nayi muku misali da wata yarinya ,saida tagama xubar da mutuncinta sannan takesan tayi aure Amman abin ya faskara,gashi San auren takeyi kamar ta kai kanta,duk Wanda yaji halinta saiya gudu dan Allah a dinga kame kai " yan matanmu,holl din yayi tsit kuwa yana jinsa,ni kuwa tunda yafara nasan dani yake dan dai babu halin yin mgn ne,Na yanke hukuncin gara kawai nafita,dan nasan ba 'karamin aikinsan ba ne yafadi abinda yafi hakan a kaina,ko yace musu nice,yace wataran xan kawomuku ita har nan kuganta kuyi mata nasihar ta canja halinta kotasamu mijin aure kodameso a cikinku,akasa ihu ,Na mi'ke da sauri memakon nafita ta inda dalibai suke fita sai kawai namike Nahau matattakalar da yake nadinga tafiya inata yanga dan ayau sai nanuna masa macema da iya kissarta,duk namijinda yake ta'kamar baya kula mace mara kamun kan da shiba dan iska bane ,kuma bega macen da ta isa taja ra,ayinsaba ,tunda nafito yaxubamin ido ,yakasa dauke idonsa a kaina,Na bangajeshi Na wucewata ta inda yake fita,.

Wannan page din mexafine ina San wannan littafin Na xaxxafan rabo ina godiya

080 60812041👏

💕💕💕💕💕ZAZZAFAN RABO💖💖💖💖
Na Aisha Umar Indabawa marubuciyar littafin Meka Maidani💕💕💕

🤳typing🤳

🦚page 10🦚

My whats app number 081 60812041

Ina matukar jin dadin yadda ake bibiyar wannan novel din Allah yabarmu tare masoyan xaxxafan rabo👏

Shi kuwa sai sosa keya yakeyi ,nan danan ya fice daga holl din da mugun sauri dan kunyace ta rufeshi sbd irin kallan da yabita dashi kome ya kaishi ohu ya daki kansa da karfi,su kansu sauran mutanan holl din mamakin abinda salwa tayi sukeyi ,dan sunsan Salwa da kunya da kawaici gashi batasan abinda xai jamata matsala a mkranta fauxee ce tafara xuwa inda take saune tace salwa kinsan kuwa yau abinda kika aikata,fauxee ina sane wlh abinda yakeyiminne yayi yawa wlh ,tunda ya daukeni yar iska xan nuna nasa ni babbar "yar iskarce ni ,bashida wacce xaiyi misali da ita saini ,dukfa abinda yagama fada danifa yake ,kuma bakisaniba irinsu sune tantiran " yan iskan ,danma yaga ana rabuwa dashine ni kaina banta6a xatan xan iyayi masa hakaba,har xuwa kallona aka dingayi waiga wadda taso ta rungume Mlm Abdul ,nidai saina dinga 6uya duk inda nasan mutane xasu ganni ita kuwa fauxee dake bata rabo da abin dariya wai wlh mun burgeta kuma mundace dama ya aureni ,nace bakida aikin yi ke kina ganin xan iya auren me wannan mugun halin Allah ya kiyaye ,saida akakusan tashi saiga aikensa wai naxo ,nace to ina xuwa,na share Na rabu dashi,nace da fauxee ni xan wuce gida ,tace kawai ki bari ya Muhammad yaxo saimu wuce tare,nace kenifa baxan tsaya laccar karsheba ,sbd ya Abdul nemana yake yi,tace nima bara mu wuce tare bara Na kira ya Muhammad din tace to,kinsan yaufa ana rana muyi sauri karfa yaritsani ,yace mata yanama cikin mkranta yaxo wajen nauwara,yayi mana kwatancen inda yake ,a tsaye muka sameshi sunata hirarsu harda dariya ,ni dai kawai sun burgeni sosai,natsaya ina kallan su dan bansaba ganin kahaba ,muka gaisa ya kallemu kunxo kawai xaku takuramana,muka sa dariya muka nufi inda ya ajiye motarsa ,iri daya guda biyu sak babu abinda yaraba kodan a firgice nake ne oho,Na wuce fauxee dan ita ta tsaya da wani suna mgn ,dan saurin da nakeyi karya tarfani ,na bude gaban motar kawai nashige ,kawai naga anxuge Gila's din motar gaba daya na juyo da saurina muka hada ido dashi ,yace a tunanin ki duk takunki bansaniba, harni xanyi kiranki ki'ki xuwa baki isaba wlh salwa kinyi kadan to ina kike shirin xuwa yau ,yau jarabar bin maxance ta tashi kenan ,ai wlh salwa abinda kikayi kin bani mamaki wlh sosai ma,acikikin dubban jama,a ki kunyatani ,kixubarmin da mutunci ,to aniyarki ta biki ,in Allah ya yarda baki isa kija ra,ayinaba ,wato da banyi saurin kaucewaba rungumeni kikayi niyar yikenan,Na juyo da sauri ina kallansa ,yayi saurin kautar da kansa,daina kallona dan wannan idon naki yana isa mutum yashiga wani hali,nayi saurin sun kuyarda kaina .
Chapter 9 · 0% Book details