← Book details Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sauri kawai nakeyi dan nasan nagama makara ga test din da yake gabana,ta Mlm Abdul, ina tahowa shikuma yana shiga daguduna nakarasa,yadakatar dani haka nadinga rokonsa dan Allah yabarni nashiga koda ban amsa dukaba Amman kamar badashi nake mgnaba saidaya fito ya gallamin wata muguwar hara,yace suda sukafito da safe aisunsan muhimmancin abin,ni daman cos dina metsadane,bakowane wawane yakeciga,dan haka kisa aranki duk jarabawar da xaki xauna kixanamin kinyi abanxa dan baxaki ta6aciba wawuya ballagaxa Mara kamun kai,yawuce yayi tafiyarsa ,sauran dalibai kuwa sai mgnar sukeyi,wasu suna ganin laifinane meyasa banasan xuwa da wuri,nadinga binsa mana ta yadda yakeso mana. Idai yauma a cikin bakin ciki nakoma gida,ita kanta umma tagane nayau yafi nakoyaushe ,yaune ranar farko datace meke damunki, banji kunyartaba nagaya mata duk abinda Abdul yakeyimin,tace to ni ina ruwana,ranar danasanima tana gaba,duk abinda namiji yayi adone a wajensa ita kuwa mace har jikokinta ,kin6ata rayuwarki dasan xuciya,tawuce daki tarabu dani,nikuwa kuka sosai nadingayi dan gabadaya duniyar taficemin aka,wani me yasa ba ayiwa mutum uxuri dan wata kaddarar tafada masa,ya Allah kakawomin sauki,agida banji dadiba,awajema ban hutaba,nadaga hannuna ina rokon Allah ya yafemin,idan wani laifi nayi bansaniba,ko abincin dare kasaci nayi sbda bakin cikin da yake raina,awajen umma badadi nakejiba shikuwa,Abba gaisuwace kawai take hadamu dashi ,hakurin duniya nabashi yaki hakura,kwana nayi INA kuka kodana tashi babu Wanda yatanbayeni abinda yake damuna ko me yasa idona yayija ba bansamu wannan gatanba,haka nashirya natafi makaranta,kodanaje Mlm Abdul kin barina yayi nashiga,magiyar duniya Amman yaki barina ,ni kuwa tsabar bakincikin da yake raina ga wani irin Cowan kai cikina ya murda darashin cin abincin da banyiba yasa nadinga kwara amai naruwa kawai,sukansu kawayena abin wabasu tsoro sosai, wasu sukace akaini gida wasu sukace akaini Asibiti,, Suns cikin takaddamar saiga malam Abdul ya kalleni yasha kunu yace meke damunki,kasa yimasa magana nayi sai kawai naga ya girgixa kansa, yace ke fauzee sakamun ita amota xankaita Asibiti, takamani takaini nakin motar Amman sainaki shiga,nace ngd anemarmin mota natafi gida,ya sha kunu yace fauxee kushiga mutafi,adolena nashiga,domin dishi -dishi nake gani,gashi har,a lkcin bandena amanba ,yawani tsayar damota afusace,ke da Allah karki lalatamin mota,komeyema bakece kikajawa kankiba,ko dan kinga natausaya miki,xan kaiki hospital nima kawai abinda nakesan sani,wani karamin Asibiti yakaini sai cewa yayi da fauxee ta xauna a nan yashiga dani,tace masa to kawai,inarike da cikina muka shige wajen likitan,suka gaisa da alama sundade da sanin juna,dai kawai jinayi yace dan Allah Dr dubamin yarinyarnan muke danmunta,Amman kafinnan inasan ayi mata test din fitsari muga meke damunta sai kawai Dr yace haba abokina mekake nufi daman kayi aurene bansaniba,aisai naga kamar budurwace,koka canja haline bansaniba,dai kawai yasha uku har yanxo inanan a yadda kasanni,kawai dai kayi abinda nace maka kona canja Asibiti, da Sauri likitan,yace a a yanxo xanyi muku,ya kalleni 'yan mata shiga cikin toilet dinnan kiyi fitsari a cikin wannan robar,ya mikomin,namike kawai nafice daga dakin inata kuka,Ashe abinda yake nufi dani kenan,ya Allah kayimin sakayyar gaggawa,da sauri yabiyuni ,kinsan bakida gaskiya da kinada ita kistaya mana,sai kawai nakoma nayi yadda likitan yace namika masa,agabana yaxaro wani dan tsinke ya tsoma acikin fitsarin yaxare ya kalleni yace da Mlm Abdul babu komai yace beyaddaba,yace wlh babu komai kasan baxan 6oyemakaba,yace toya dubani dan yaga nawahala sosai yabani makunguna yace nadainasa damuwa araina dan hawanjini yana gafda kamani.

Agida ya saukeni ,itakuma fauxee yawuce da ita makaranta wato daman Mlm Abdul yasanni kenan yake nuna besanniba,komadai meye susuka sani,dake fauxee bame surutu bace babu wanda tagayawa.

💖💖💖ZAZZAFAN RABO💖💖💖

Na Aisha Umar Indabawa
Marubuciyar littafin Meka Maidani💕💕💕

🤳typing🤳

🦚page 3🦚

Duk Wanda yatanbayeta sai tace daga Asibiti gida akayi da ita,sauran dalibai kuma sunxata tausayin da yake nunawa sauran dalibaine shiyasa yayimin hakan su basusan da shirinsaba niya kawai yayi yatuxartani,sai kuma Allah bebashi iko ba,ciwo sosai nayi sai danayi kusan sati biyu a kwance,Amman kullum sultan yana xuwa dubani,dan wani lokacin hardasu kayan dubiyarsa idan nace waye yasiyama yace kakawomin sai yace uncle mana kuma yace yanayi miki sannu harma da mommy nace to duk kace ngd,ina xaune da yamma a tsakar gida saigasu mommy da Mlm Abdul, da sultan anyi masa kwalliya yayi kyau sosai,Na mike da saurina inayiwa mommy sannu da xuwa mommy ce kawai ta amsa nagaishesu,shi kuwa kamar Wanda aka takurawannan yaxo wajena,mommy tadinga yimin nasiha akan nadaina sadamuwa a raina komai mewucewane,wataran sai lbr,ina hawaye nace ngd,ita kuwa umma ko kallan inda suke batayiba ni kuwa kallan kudin da suka ajiyemin kawai nakeyi. Da umma tafito daga daki nanuna mata kudin da suka ajiye,tacetunda San xuciya yasaki kar6a to ni inada wadatar xuciya,kuma Na iya ri'ke talaucina bana nema a wajen wani sai dai Allah, kedai da kikesan abin hannun wani sai dai nace Allah yashiryeki yasa kigane gaskiya ajiye kudin kawai nayi a wajen nashige daki naciga da aikin tunanin rayuwar duniya wai yaunice kamar banida iyaye banida mebani shawara ko idan wani abun yana damuna nagayawa wani nikam nayi bakin cikin xuwana duniya naso ace inada yayye mata Amman banidasu sai tarin maxa,kuma maxanma mutum dayane yake tausayina yake damuwa da damuwa,nikam rayuwa tagama ficemin araina,Allah dai yadawomin da ya yaxid kona gayamasa damuwata,dagyar nasamu naci abincin dare,dan nasan babu mecewa naci sai dai idan da yinwa xan kwana kadan naci nakwanta inajin umma da Abba sunata hirarsu harda dariya nidai nayi namo a daki,saiga umma nan tashigo da leda ta diremin a gabana,idan kingadama kidauka kici in kuma bakiga damaba kibarshi yalalace nidai banyi mata mgn ba Na sakko daga kan katifar nabude namane yaji kuli-kuli sai kanshine yake tashi naci sosai kuwa dan yayimin dadi sosai,namike naje gaban Abba nace angode Abba Allah yakara budi,ko kallona beyiba namike natafi Na kwanta Amman in kaina nasan bawani bacci xanyiba inajiyo hirarsu,har Abba yana cewa nifa xaman yarinyar nan yafara isata duk dadai yaxidu yadage sai tayi karatu,Amman nafiso tayi aure tacigaba a dakinta tace hakan yayi dai dai,inajinsu har bacci yadaukeni koda natashi da safe shirin mkranta nafara sbd nasan inada aiki a gabana gashi munkusa fara exam nayiwa umma sallama nafito a kofar gida naganshi shida sultan yayi shirin mkaranta da alama kaishi xaiyi yana ganina yataho da gudu ya rungumeni nadagashi nace katashi lfy ya gida yace lfy lau kinji saukine aunty xaki mkranta xumuje nace da uncle ya kaiki Na girgixa kai nace karku makarakaji yace to nace ayi karatu da yawa yace to ,nace to jeka kutafi yagarasa da gudunsa yana dagamin hannunsa sai danaxo daf dashi harnayi niyar gaisheshi kawai saina fasa sbd yanxo xanjawa kaina wata masifar sai jinsa nayi yace sultan karka sake kula wannan aunty tunda bata ganin darajar manya ko banci darajar Wanda yagirmetaba ai naci darajar malamin shi kuwa sultan cewa yakeyi nima baxan sake kulataba tunda bata kula uncle dina yace yauwa yaron kirki ,ina kallansa yamika masa hannu suka tafa yabude masa mota yashiga a bakin titi suka ganni sultan ya kautarda kansa,waishi irin yaji mgnar da aka gayamasa dabe hanashiba da idan yadinga kwalamin kira harsai nagaji nidama yadaina kulani gaba daya dana huta.

Daman umma basan xuwanshi takeyiba,yana sauke sultan yawuce mkranta abinka da motar haya harya rigani xuwa sai dai bashine da laccar farkoba ina murnar yau dayadai xansamu darasinsa Amman yana shigowa yace nafita koshi yafita yabarmin ajin sainayi musu abinda xaiyi musu nan da nan dalibai sukace basu yadda ba haka nafita ina kukan bakinciki shikuwa banda dariya babu abinda yakeyi kuka sosai nayi gaskiya nakusa daina xuwa wannan mkrantar tunda batada wani amfani a wajena ,Abdul yatsaneni narasa abinda nayi masa Amman xansamu lokaci nabashi hkr koya sauraramin axuciyata tayi saurin gargadina karna soma idan ba wani bala,in nake nemawa kainaba haka dai harya fito yaxo kaina yatsaya ni kuma nayi saurin sunkuyar da kaina yace kinsan wani abu Salwa natsaneki banta6a tsanar wani abuba kamar yadda natsaneki har bana kaunar nadaga kaina nakalleki dan haka nakusa yin sanadin daina mkrantarki nadaga idona da sauri nace kayi hkr dan Allah yace daman kinayin mgn jibeta tamkar mutuniyar arxiki da aceke mutuniyar arxikice da kinga gatan da xanyimiki akan kisamu ingattacen ilimi Amman 'yar malam taki halin malam nidai banda kuka babu abinda nakeyi haka yawuce banida abinda xance masa to kwanabiyu dai yatausayamini yabarni ina shiga laccar sa saidai banida damar yaganni a cikin kawayena muna hira kokuma yaganni ina dariya sai dai kawai naganshi a gabana yana cewa idan bakiyi wasaba yanxo xan tuna miki asiri kowa yasan wacece ke sai dai nasunkuyar da kaina harya tafi,yana tafiya fauxee ta mike nifa gaskiya Salwa abinda Mlm Abdul yakeyi miki yayi yawa danyana malaminki sai kawai yadinga yimiki abinda yaga dama ko kuma akwai abinda yake tsakanunku ne bansaniba .nace babu komai fauxee kawai dai tsanata yayi kawai Toni xanje nagayamasa abinda yakeyi baya kyautawa.dasauri nace kirufamin asiri kema kirufawa naki asiri kar kema yatsaneki dan Allah kirabu dashi wataran idan ance yayi baxaiyiba idan mutum abu yasameshi bawai aibatashi xakayitayiba sai dai kace Allah ya shirya mutum.
Chapter 2 · 0% Book details