← Book details Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A hanyane sultan yake cewa wai kawai a dauko aunty tadawo gidansu da zama tana hadamasa kayan dadi shidai Abdul dariya kawai yakeyi ,to idan munje masallaci kadinga yin addu,a to uncle kasan inasan aunty me kirki ,to sultan Allah yabiye bakinka yace da sultan din kace amin yace to ameen uncle duk sukasa dariya ,yana tsayar da motar yashige gida da gudu yana kiran mommy ,kinga kayana da aunty me kirki tabani ,ta kar6a tace a lallai taburgeka to kawo na 6oyemaka dan nasan halincin zakinka shi kuma uncle din naka batsawatar maka zaiyiba ,ya mi'ka mata karkicimin dan Allah, tace mezanyi tasa dariya tadibar masa guda biyu Tamika masa yatafi dagudu waje ,habu direba yatareshi yanacewa yasammasa yanayi masa wasa ,yami'ka masa guda daya yace a a wasa nakeyima yaja hannunsa yace zumuje muga doki kaji nadoraka akansa ,yace ni gaskiya tsoro nakeji karya cijeni ,yasa dariya habu direba yace babu abinda xaiyima yarike hannunsa sukayi 6angaren inda Abdul sukeyin kiwon dokona ,suka dinga zagayawa har sultan yanayiwa habu direba tanbayar wai yayaga wannan fari kuma duk yafi sauran kyau ,to ai kowane da kalarsa wannan fari gakuma ja wancan kuma baki eh hakane kuma ,Amman uncle yacemin yafisan farin yace aishine yafi hawa shine jurau dinsa ,ahaka har suka 6ata lkc sosai sai wajen gaf da magariba sannan suka fito ,suka hadu da Abdul yace Ashe Ku kunanan inacan ina Neman Ku ,to ayi sauri ayi alwala sbd karmu makara ,shima habu yayi suka wuce masallaci ,su abdul basu dawoba sai da akayi sallar isha,i sannan suka dawo gida suka tarar da mommy tana nannade sallayar da tayi sallah ,Abdul yayi mata sannu da gida ta amsa masa duk sukayi kan table yana budewa yace yau kuma mommy tuwo akayimana ya dauko guda daya yasaka akan fleet yabude namiyar miyar agushice da taji naman kashi da busheshen kifi yaxuba yatura a gaban sultan to bisimillah ,sunaci suna hira kamar da babban mutum shi sultan dinne yake bashi lbrin dokin wai idan yagirma abar masa to kacigaba da maida hankalinka yace to uncle ai inayi yace tabbas banda matsala dakai to Amman kadage kaji yarona yace to uncle ,

Yajin aikin da aka sanar "yan Jami,a sunfara a daren jiya ,wanda ba nasan ranar komawarsuba harsai baba tagani Abdul yadinga mita mommy tace to kai meye naka aciki ,wlh mommy daliban nake tausayawa dan kinga wasu sauran wata uku sugama kinga anjaza musu an 'kara musu lkcin gamawa tace HK ne Allah ya kyauta ,yace ameen ,yadauki sultan yakaishi mkranta yawuce office din sa dan daukan wasu takaddu ,yaga dalibai duk hankalinsu a tashe ,yadinga basu hkr ,yanacewa su kwantar da hankalinsu in Allah yayarda za a dai daita yabar school din yanajin tausayinsu ,salwama dai bataji dadin abinba sai dai babu yadda xatayi ,tashirya tace ita gidan yaya yazid zata koma har sai ankoma mkranta ,ummanta tace Allah yatemakasaiki bari idan abbankuyadawo kigayamasa to Allah yasa yabarni tace to ameen lkcin da yadawo take gymasa yace to Allah yakiyaye hanya ta hada kayanta ta tafi ,daman sun saba da matarsa daki daya aka waremin nasake sosai ,idan yafita suyita hirarsu ko suyi kallo ,dadewar da tayine mutane suka ankara da ita har akafarayin sallama da ita to Amman ita abin baya gabanta sbd tasan abun baxai ta6a yiwuwaba gani takeyi kamar baxata ta6a aure a rayuwartaba sbd irin matsalolin da akesamu a aurenta nata.

Suna zaune da magariba wani yaro yayi sallama yashigo ya gaishesu suka amsa ,aunty tace muhusin yaya akayi ,yaya nazir ne ya aikoni wai ana kiran bakuwar gidan nan ,nayi saurin cewa ni yace eh ,nace kace banananan anti tace a a kace tana xuwa ,yafita dan sanar da aiken da akayimasa ,nace aunty ya zakiyimin hk ,shikenan Salwa sai akace kindaina kula kowa a duniya ai ba,a hk ,bakisan kowaye mijinkiba sai Allah ,ba haka bane aunty kinsan matsalata banasan ayimin tanbarin wani sunan banda Wanda akayimin ,tace ai komai daga Allah ne kiyi hkr in Allah yayarda komai yaxo 'karshe to shikenan aunty ,nadauki mayafina nayi waje gabana yayi mugun faduwa sainaga kamar ya Abdul sai danakarasa kusa dashi sai naga ashe irin tsayiwarsace kawai ,nagaisheshi ya amsamin da dariyarsa ,toya gida Salwa Allah yasa bantakura mikiba ,nace babu komai ya gyara tsayiwarsa ina fatan kowa lfy nace lfy lau ,nidai sunana nazir kuma ni dan unguwarnanne ga gidanmu can ,yanunamin wani hadaden gida ,kuma nine babba inadakanne Bihar hudu mata saimu biyu nida kanina nidai asalinmu"yan katsinane gaba da baya aikine yakawo iyayena nan ,sai inda nake aiki a kanfanin dan gwate kingane nadaga masa kaina ,kumani da gaske nakeyi babu wasa dan ina ganinki naji kawai kece matar tawa nadanyi murmushi shima yatayani ,to "yan matana meye ra,ayinki a kaina,nace to kabani lkc ba yanxo zanbaka amsaba babu damuwa Salwa to bara nawuce dan naji anfara kiran sallah ,nace to Allah yabamu alkairi yace amin Salwa nawuce gida shima yatafi ,bamuyi wata mgn da aunty khadijaba har saida mukayi sallar isha,i naci abinci dan ita da mijinta sukeci ,nake gayamata duk yadda mukayi dashi,tace gaskiya kinyi sa a dan nazir mutumin arzikine gasan addini sai dai ubangiji yasa albarka nidai dariya kawai nayi ,tace da alama dai yayi nasara tunda naga kina dariya nace nidai banceba tace zakicene wataran duk sukasa dariya ,nidai yaya yana dawowa najege daki danna barsu susake dan nasan aunty khadija saita gayamasa ,nidai tun safe natashi nayi duk abinda xanyi harya fice becemin komaiba nima kuma bangayamasaba a hirar da mukayi da Aunty ne takegayamin irin murnar da yayi nidai murmushi kawai nayi ,yau kuma sai bayan isha,i yaxo da kamar karna fita saida aunty tayi mgn ,tundaga nesa nahangoshi gaskiya nidai akace na aureshi nayi sa,a dan gaskiya irin mijin da nakesone gakyau ga iya gayu Allah yatabbatar mana da alkairinsa ,ya'karaso to ginbiya kinkasa k'arasowa to ni gani a gabanki sai yadda kikayi dani nayi murmushi ,nace kai kuwa da abin dariya kake ,nagaisheshi ya amsa nanfa muka dinga hira ,haryakecemin wai ummansa tana gaisheni nace to ina amsawa,to Salwa gani gareki meye sakamakona ,kaikuwa da gaggawa kake ainace maka kabani lkc ,to bani tarihinki tunda kinji nawa to aini kasan unguwarmu kuma tunda kasan yaya aika sanni yace hk me to yanxo mekike karanta naji yayanmu yace kina karatu a B u K tace hakane (social science) yace dakyau Allah yabada sa,a nace amin mukayi sallama nashigeyaa gida ,tunda nashiga gida nake tunanin yadda mukayi dashi kawai nakeyi ,nidai addu,a kawai xandingayi Allah yasa munafikin da yasaba 6atamin aure Allah karyabasu ikon 6atamin wannan domin nasa raina da samun masoyin arziki ,wasa wasa soyayya mekarfi tashiga tsakaninmu da nazir yadda wani bayasan 6atawa dan uwarsa rai,duk "yan gidansu sungama sanina duk da ina gidan ya yazid kowa cewa yakeyi nayi sa,ar samun yaron arxiki sai dai Allah yasa ayi a sa,a yau dai nashiya tunsafe nace sai wajen ummana ,aunty yadinga magiyar naxauna kodai wani abun yayimin nace Allah babu komai nafara hada kayana tadinga magiya.

Kuyi hkr da wannan kunsan typing da wahala
💘💘💘💘ZAZZAFAN RABO💞💞💞

💫💫💫Aisha Umar Indabawa💫💫💫

🌟🌟🌟marubuciyar littafin Meka Maidani🌟🌟🌟

📱typing📱

🦚page 1️⃣4️⃣🦚

Kuyi hkr masoyana kunsan typing da wuya ga hidimar gida,

Ina barar addu,ar ku ,d'an makotanmune yarasu yaro meshiga rai Allah yajikan Ahmad yayi masa rahma 😭😭😭
Chapter 13 · 0% Book details