← Book details Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 18

Sashe 3

Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****Jin fauxee nayi tanacewa toke Salwa akwai abinda yata6a hadaku dashine nace a a kawai dai unguwarmu daya dashi,kuka duk unguwar gidanmune kawai natalakawa shine masu kudin unguwar sukace yasiyar musu da gidan yaki ,sunyi sunyi yatashi yaki ,to kinji abinda yahadamu dasu
Tundaga lokacin fauxee tadinga bani wata irin kulawa da alama tayarda da abinda nagayamata idan yaxo yana gayamin maganganunsa sai dai kaji fauxee tana cewa da talaka dame kudi duk daya suke a wajen Allah sai tayi saurin bagarar da mgnar,tace kayi hkr mana Mlm katausaya mata mana sai yayi saurin barin wajen,shi kansa wataran tana bashi tausayin yana kuma jin kunyar abinda yakeyiwa yarinyar,sai dai shine hukuncinta,danshi yatsani mara kamunkai to ita kuma taxubar a titi.
Ni kuwa gaba dayan mkrantar ta isheni. Gasamarin Jami,a sundameni sai kawai nayanke hukuncin xantanbayi Abba yabani kudi xandinga hijabai,in Allah yatemakeni yabani ranar da daddare Abba yanacin abincin dare ga umma akusa dashi nayi musu sallama suka amsamin,nace dan Allah Abba idan kanada kudi kabani xandinka hijabai xandinga xuwa mkranta dashi becemin komaiba sai ummace ta kalleni tace to jeki yaji nace musu to namike nashige daki nakwanta ina addu,ar Allah yadai daitani da iyayena konasamu rangwamen wani abun,saida safe harnayi shirin school nayiwa umma sallama sai kawai naji kiran abbanmu nayi saurin xuwa kofar dakinsa nace gani Abba, naleko ina gaisheka Amman baka amsaminba,naxatama ko bacci kakeyi yace idona biyu kawai dai inayin wuridine .yamikomin kudi nasa hannu biyu na kar6a nace ngd Abba Allah yakara budi yace amin .nami'kawa umma kudin nace ta ajiyemin idan nadawo saina kaiwa ummi medinkin hijabai tunda har yadinan take siyarwa ko kuma idan tadinka masu kyau saina siya tace dama yafi nayi mata sallama natafi.
Bansan da test din da xaiyiba inaxuwa naji 'yan ajin suna cewa Mlm Abdul test xaiyi nace to Allah yasa muci duk sukace ameen,saidai dayashigo yaraba mana takaddun naduba naga babu abinda nasani domin baya barina naxauna bare nadinga gane abinda yake koyarwa saidai idan yafita natanbaya ayimin bayani .banwani wahalar da kainaba sbd ban iyaba dai kawai nasunkuyar da kaina akan takaddar kamar jin mutum nayi akaina nayi saurin daga kaina muka hada ido dashi,yayi saurin dauke idonsa .ke ki daina tsirawa mutum ido koke mayyace,kokin xata irin mutanankine,ni nasan da wannan idon naki kike yaudarar mutane ko mutum beyi niyar kallanki ba sai mutum yakalleki to ni nafi karfinki Salwa.nidai sunkuyar da kaina kawai nayi nace kayi hkr mlm .yace yine baxakiyiba nace ban iyaba sbd baka barina naxauna ,yace ke kika sani ni nayi nawa nagama kuma bansamu matsalaba yabar wajen kodayaxo karba kasa kaimasa nayi sai kawai narubuta masa karangwantamin ko naga dai dai akaratuna,Na rintse idona namika masa wani irin kallan tsana yakeyimin. Ko a office nata yafara dubawa yaga abinda tarubuta,yaduba nasauran yaga suma basucida yawaba yace kinci darajarsu dan da da yadda xa ayi nakoreki da tuni angama.

💕💕💕ZAZZAFAN RABO💕💕💕💕

💗💗💗Na Aisha Umar Indabawa marubuciyar littafin Meka Maidani💗💗💗

🤳typing🤳

🦚page 4🦚

Sai dai xanyi maganinki salwa,washe garin ranar yaxo yadinga yiwa dalibai ,masifa wai duk abinda yakeyi aikin banxa yakeyi domin baganewa akeyiba,to wallahi kowa yashiga hankalinsa,gaskiya a ranar yayi fada sosai aka dinga bashi hkr Amman yaki hkr sai dayayi dan kansa yahakura,ya fice daga holl din yanata tsaki.ni kuwa da naje siyan hijabin naga masu kyau naxa6a kala biyar ko wanne dana gwada yayimin kyau sosai,sainaga duk nacanja gaskiya hijabi suturane,da safe Dana shirya sai nadauki wani blue nasaka kalar atamfar danasa,sai naganni nayi kyau sosai,yaudai banhadu dasuba dukda irin sammakon da nayi,dan wani lkcin ina ganinsu shida sultan xai kaishi school, narasa abinda nayiwa yaron idan yaganni saiya kautar da kansa,tun abin baya damuna harna farajin wani iri a raina ,muna haduwa da 'kawayena suka dinga yimin dariyar hijib din danasa wai aiyayimin yawa ina xan kaishi,mace nafisansa a hakan ,muna xaune a bakin wata bishiya muna karatu ,kawai sai ganin mutum nayi a gabana ance ke salwa nayi saurin dago kaina,duk sauran 'kawayena suka xuba masa ido suga irin wulakancin da xaiyimin,yasa dariya su salwane yau da hijabi kamar gaske,da ace har a xuciyarki haka yake da kinji dadi,Ku kuma dakunsan abinda ta aikata da babu mesake sauraranta ko yaxauna a inda take harya dinga mu amala da ita,ko kuma yau nafada kowa yaji a huta,nadago idona dasuka gama rinewa daja sbd tsabar kuka,sai kawai yasa dariya yabar wajen,wata acikin 'kawayenmu tace gaskiya Salwa nafara yadda dan da ace sharri yayi miki da tuni kunyi fito nafito domin abin yayi yawa,ke kuma sai akaikin kuka,fauxee yace aikinsan ba halinku dayaba Salwa tanada hkr da kawaici kuma malamintane darajar wannan kawai yaci,kawai dai yatsani salwane kuma in Allah yayarda saiyayi danasaninduk abinda ya aikata ,tajamin hannu tace taso Salwa idan kowa xai gujeki ni baxanta6a gudunkiba duk rintsi ina tare dake,kidage kiyi karatu xakiga amfanin abun nan gaba,nadago idona dagyar nace ngd fauxee da irin kulawar da kike bani tace babu komai,nifa da ace nice datuni nabar masa mkrantar ,nace to naje ina kinsan kuwa da yadda aka nemomin mkrantar kuwa,kodan yana ganin dasa hannunsa shiyasa, ke xan iya cewama a gidansu akeyimin komai kudin motane kawai ake bani agidan mu shiyasa wulakacin yayi yawa Amman wataran sai lbr duk wani abu idan yayi tsanani da lokacin sauki tace hkne Salwa koda akaxo daukanta a gida sune suka kaini har gida,har nake nuna mata gidansu Mlm Abdul yana xaune a kofar gida shida sultan akan kafet ga Littafi a kusa dashi da alama dai karatu yake koya masa,fauxee tace wai wannan yaron dansane nace a a dan yayansane tace tabdijan Amman kowa yana San yaron nace sosaima kuwa ,akofar gida suka saukeni nayi musu gdy tace babu komai ai duk Wanda yatemaki wani Allah xai temakeshi ,tace gobe dasafe xataxo ta daukeni nace a a tabarshi kawai tace Allah sai taxo mukayi sallama nashige gida,ita kuwa tatafi tanata mamakin abinda nagayamata gashi yau tagani da idonta.

Dan yau tagani da idonta babu wani karamin gida idan banasuba,idan bagayama akayiba ko kagani da idonka baxaka ta6a cewa da irin gannan gidan a layinba,koda safe sukaxo muka tafi tasa tana bayantamu nasan kuma yaganmu yau ina murnar bamuda darasinsa,sai dai wajen karfe dayan rana saicewa akayi naxo inji Mlm Abdul, shikansa dan aiken yasan inacikin tashin hankali sosai,nace yana ina yace yana cikin office dinsa yace kiyi sauri nace to a sanyaye,gabana yanata faduwa nanufi office din nasa,Na kwan kwasa akace nashigo akan kafet kawai natsuguna nafara gaisheshi yayimin banxa ,sai kawai nace ganito,shima betankamin ba tun ina tsugune harna Gaji naxauna saida yatabbatar da nagama gajiya sannan yace daman tanbayarki xanyi nace masa to.
Ya tsuramin ido sannan yadaure fuska yace Salwa inasan duk abinda xantanbayeki kigayamin gaskiya nace masa to,ya kautar da kansa Salwa meyena komawa saka hijabi kodai kinada wata matsalarne kigayamin gaskiya xantemaka miki kuma babu meji dan Allah gayamin,na dago idona da suke fitar da hawaye,nace kadaina xargina domin ba haka nakeba, duk yadda kake tunanina bankai nan ba,Na sunkuyar da kaina nadinga kuka ,to fice kibawa mutane waje karwani ya xargeni kijamin masifa dan kuwa ke annobace a idon kowa.kuma idan nasake ganin wasu sunkawoki gida sai kingane kus kurenki,kema kwadayiko kinkai kanki inda Allah bekaikiba ko,duk dai mutum me kwadayi yana tare da wahala,Na mike na tsuguna nace ngd,harda cemin madallah,ina fitowa fauxee nagani a bakin office din natafi da guduna na riketa tace kiyi hkr nasan cinmitincinsane yatashi,koda aka tashi babu yadda fauxee batayi dani naxo mutafiba Amman naki xuwa,nace Mlm Abdul yahanani idan kuma baso kikeyi wani abun yabiyo bayaba,tace shikenan Salwa Allah yayi miki maganinsa nace amin.

Yau anyi wuyar mota sosai ga yinwa,koda nasamu abin hawan cewa yayi baxai shigar dani cikin layinmuba nace nayarda,ya saukeni a bakin layinmu nakarasa gida a kafa.da daddare muna xaune naji wai ance ana sallama da Abba,umma tace ace yana masallaciyace to ace xai dawo,inacin abinci kawai naga Abba da Mlm Abdul, nayi musu sannu da xuwa nadauke kwanon abincina nashige daki naciga dacin abuna,umma nagani a kaina tace kixo inji abbanku nace to nafita nace gani Abba gabana sai faduwa yakeyi,yace kin kyauta Salwa atunanin ban huce da bakincikin da kika dasaminba,bare harki karamin wani,iya tarbiyadai nasan nayi miki Salwa, nace kayi hkr Abba Amman bansan laifin dana aikatamakaba,yace aidaman melaifi bayasanin laifinsa, Abdul axix gaya mata laifinta,sai alokacin nakula da wanda yake kusada abban danni gaba dayana a tsorace nake.ya kalleni a gaskiya abba baxan 6oye makaba, Salwa bata karatu banda tara samari da kawayen banxa babu abinda takeyi,Na hanata taki hanuwa gani takeyi kamar takura mata nakeyi,ni kuma ina ganin kamar nine nafi kowa kusanci dana kula da ita,nadago idona nakalleshi ina hawaye ban iya cewa komaiba sbd banida bakin mgn,shi kuma ya sunkuyar da kansa,kodana fada ba yadda xai ayiba,yadinga gayawa Abba 'karya da gaskiya,shikuma Abba yayarda harda cewada Abba wai kullum yanxo idan antashi saurayine yake kawoni gida idan antashi yayi yayi dani akan nadinga biyoshi mudinga tahowa tare amman naki,wai karshema cemasa nayi babu ruwansa dani sai nadingayin kamar xan xageshi,gashi ina yawan kunyatashi a gaban dalibansa,Abba kuwa ya rufeni da duka sai ummace ta kwaceni shikansa yasan nadaku,yadinga bawa Abba hkr,yana cewa shidai yana Neman alfarma daya a wajen Abba,yace inajinka daman cewa nayi xandinga xuwa muna tafiya tare idan kuma lokacin tashinmu bexo dayaba sai kowa ydawo shikadai,Abba yace a gaskiya Abdul baxan sake yadda da wani ba,Wanda nayarda dashi shine yaci amanata bayan iyaba Abdul ,yadingayi masa magiya yace shikenan Abdul, dan Allah Abba kayafe masa badanniba,
Chapter 3 · 0% Book details