← Book details Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 18

Sashe 15

Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tak'arasa gabansa tace gani Mlm,yace Salwa babu gaisuwa tayi saurin sunkuyar da kanta,tace daman ina shirin gaishekan ne sai kayi maganar ,duk yafiskanci a tsorace take ,yayi fuska kinayin karatun kuwa ,kokuwa auren kikasa a gaba ,ita dai tayi masashiru ,yace Ashe har yanzo salwa bakidaina kwadayiba wato kedai Allah yazuba miki kwadayin naman kaza ko ,shi yasa a koda yaushe kike likewa "ya" yan manya ko to kishiga tai tayinki ,wuce kibani waje sai wata murna kikeyi zaki aure dan manyako ,to idan bakiyi wasaba duk saina gayamasa duk tantirancin da kikayi ,kinga shima saiya fasa ,saina daukeki idan nayi aure kidinga yiwa matata wanke -wanke da shara da rainon yara wuce kibani waje munafika ,nakasa daga k'afata sbd tsabar kunya ,dan a bayan wasu samari yayimin yasake daga murya yace wuce nace ballagaza ,da kukana nayi hanyar get dan ko jakata bantsaya daukaba kuka nakeyi sosai ,da dariya ya wuce yace shegiyar yarinya idan ta kalli mutum da idonta sai yaji wani abun a ransa tunda kintafi wlh test zanyi me muhimmanci daman basan karatun naki nakeyi ba,ya wuce office dinsa da sauri ,ya dauki sauran tarkacensa yayi cikin holl din,fauxee tana bakin bishiya taga wucewar Salwa da sauri kafin tayi yinkurin binta harta fice ,tace tabdijan wlh Salwa idan zaki dinga biyewa Mlm Abdul kullum sai kintafi gida ,danshi hakan yakeso ,tanacikin zancen taji sauran dalibai sunagudun shigacikin holl din ,itama da gudunta tak'arasa tana shiga taga Ashe test zaiyi ita kanta Allah ne yarufa mata asiri ,dan da zamanta zatayi dan wajen yayimata dadin zama ,minti talatin yabayar yace kuma duk Wanda beyiba yayiwa kansa ,itadai tace tasan dan Salwa yayi danya cuceta ,ita wlh hartafara tsanarsa ,mutum yatakurawa yarinyar mutane ,ita ba wani laifin take yi masaba ,ita tarasa wace irin tsana yakeyiwa Salwa ,itadai tarasa asalin gabar ,da haka dai tagama abinda takeyi ta tafi gida ,tana addu,ar Allah yasa karya kayarda Salwa dantaga da gayya yayi .

Koda Salwa takoma gida gaba daya duniyar tayimata zafi ,sai dai taitayin addu,a Allah yarabasu lfy dashi,dan tafara zargin shine yake gayawa samarinta wani abun suke fasawa Allah yayimata maganin munafikin ta ,shirye shiryen bikina akeyi sosai ,gashi kuma sauran wata uku nagama karatuna nikaina nayi mamakin Dabe kayar daniba ,Allah ne kawai ya tsallakar dani a wajen sa Allah bebashi ikon yin hakanba ,a yadda nazir yakeso so yakeyi ayi fati kamar kala biyar Amman gaba daya nahana sbd ba ra ayina bane ,shi kuma yace ko guda dayane sai anyi sbd "yan wajen aikinsu ,dolena Na hkr nabi ra,ayinsa ,shirye shiryen azumi akeyi gadan -gadan dan befi saura sati daya afaraba ,nazir yazo wai menake bukata na amfanin azumi ,nace wlh bana bukatar komai ,yayi-yayi dani Amman nakiyin mgn ,yace to shikenan saida yatashi tafiya yadiremin dubu goma shima saida mukayi rigima dashi sannan na kar6a mukayi sallama yatafi .

Mommy da Daddy suna zaune suna lissafin shekarun sultan ,mommy tace aini bana maita shekarunsa da ranar haihuwarsa ,domin ranarce ta bakinciki a rayuwata ,ranace dana rasa d'ana danafi so a rayuwata sai kawai tasa kuka ,daddy Abdul yace ni matsalata dake kenan duk lokacin da Muke hira irin wannan saikin 6atamin rai badama ayimaganar shekarun sultan saikinyi kuka ai kowa baya wuce lokacinsa ,Allah ne yabamushi kuma ya dauke abinsa addu,a ita yafi bukata a yanzo ,Allah yajikansa da rahma ,shine gatan da zakiyimasa kenan addu,arki ta dinga isa wajensa ,tashare hawsyenta tace abinne nakasa mantawa dashi a rayuwata ,sai dai ina fatan Allah yamantar dani har abada ,yace addu,a itace maganin duk wata damuwa ,tace inayi sai dai nak'ara akan wadda nakeyi ,yace to sai a bada himma ,tace Allah yabani iko da juriyar duk abinda zaisameni nan gaba nadauki dangana .

Sultan ne yashigo da gudunsa yana kuka sosai ,kukan da yakeyi yayi mugun yawa idonsa idonsa yayi jajir dashi ,sai neman shidewa yakeyi ,hajiya Aisha tamik'e da sauri ta rik'e shi tana tanbayarsa me akayimasa koda faduwa yayi ,tadinga dudduba hannunsa da k'afarsa ko zataga wani alamar ciwo Amman duk iya bincikenta bataga komaiba ,tarikeshi tana sake tanbayarshi yace ba babansu khairiyya bane yace karna sake shigar masa gida tunda ni shegene waini babata "yar iskace waini a titi babata ta haifeni ,ni kuma uncle yacemin ummata ta mutu har yace nadingayi mata addu,ar Allah yashiryeta kuma inayimata kullum ,wlh sainagayawa uncle dina yaje suyi fada yayi musu dukan tsiya ,hajiya Aisha ce tasake fashewa da kuka daman irin wannan ranar nake gudu ,wlh bazamu yadda ba kotuce zatarabamu ,mun rasa abinda mukayi masa a gaskiya a wannan karan kodakai kayadda mu bazamu yadda ba ,aigaramu yataremu yagayamana duk abinda yaga dama ,dayasamu k'aramin yaro yagayamasa ,tarike sultan din sukayi daki dashi ,yi shiru kaji k'arya yakeyi a Asibiti aka haifeka ba,a titiba ,yasake kallanta yace to mommy meye shege tace zaginefa karnasakejin kafada kaji sbd babu kyau ,wuce a zubama abinci kaci kaji,karna sake ganin kashiga cikin gidan yace to ai daman khairiyyace tace nazo muyi wasa ,to karka sake in uncle yaji zai zaneka yace bazansakeba ma,shigowarsa kenan aka labarta masa ,ranshi ya6aci sosai dandai antaushe shine ,Amman sbd tsabar takaici har kuka yayi ,yafice da sauri mommy tadinga kiransa ko tsayawa beyiba ,tace tashi kabimin yaronnan kasan halin zuciyarsa ,yace rabu dashi kinsan yau anta6a masa shalelensa ni kaina narasa halin Alh abubakar yanada saka ido akan abinda babu ruwansa ,yadade yana gayawa mutane sultan shegene to ayau zan nunamasa matsayin sultan a wajena yafice daga gidan yanata maganganu ,itadai hajiya Aisha addu,a takeyi Allah ya yayyafawa wutar ruwa,tunda alh yafita a fisace tasan anta6o shine inba hakaba babu ruwansa ,abinda yaganine ya dagamasa hankali irin mutanan da suke wajen ,be dadeba yafarajin jiniyar "yan sanda nan da nan mutane suka fara guduwa sbd tsoron kar,a hada dasu a tafi dasu daga zuwa kallo ,Abdul yagani yaci kwalar rigar alh abubakar shi kuma sai borin kunya yakeyi waishi begayawa sultan hakaba sai dai idan a wani wajenne aka gayamasa,Amman yaza,ayi da jankalinsa yagayawa sultan irin haka ,Wanda yasan bazai iya dauke maganar ba ,sudai " yan sanda suka tasa k'eyar alh abubakar sukayi gaba ,shi kuwa Abdul shida daddy sa suka bisu a baya ,daga tafiyarsu "yan unguwar suka dinga cewa daman duk me surutu karshensa bazaiyi kyauba ,suka dinga fadar irin munafincin da yakeyi a cikin unguwar ,yana hada matan aure da mazajensu fada duk abinda zaifada ba alkairibane ,aka dingayimasa Allah shikara yau yahadu da gamonsa ,tunda rigima tahadasu da manyan mutane sai Allah.

Wani babban mutum yace aini alh abubakar abinda yayimin baxanta6a mantawa dashiba ,ina jos banagari yayimin waya wai iyalina kullum bata wuni a gida wai kuma yanaganin wasu k'artin maza suna shiga gidana wai nayi saurin daukan mataki sbd " yan unguwa sunfara maganar ,raina yagama baci banyi wani bincikeba nataho banyimata bayanin inakan hanyaba ,sai da muka sauka a tasha nakirata nace tayimin tuwo ,nacemin yau zandawone nace nimadai bansani ba tarabu dani ,yasake kirana wai yanzo yaga wani yasauketa a mota nace masa to kawai ,atake nasake kiranta nace tazo tabani mukullina sai tacemin naturo kofar nashigo a bide take ,da saurina nak'araso dan nakamata batanan ina shigowa tananan banga alamarma tafitaba dinkima yakeyi nidai koda tayimin sannu da zuwa ko kulata banyiba ,a haka muka dinga rigima da ita yanzon hakama tana gidansu ,ashema number tawama a hannunta ya kar6a yatura "yarsa khairiyya ,kunga aini yagama cuta wlh ,sai yanzo nake danasanin mak'otaka dashi Ku kuma ina mebaku shawarar bincike kafin mutum ya yanke hukunci ,mutane suka dinga Allah wadarai da halinsa ,sukuwa acan Abdul ne yaketa magiyar a kaisu koto kawai ,sbd gara ayimusu tsakani dashi shidai yayi nadamar abinda yayiwa yaron sai bada hkr kawai yakeyi ,dagyardai alh yahakura yace kuma yafita daga harkarsu tunda abin yazama hakan ," yan unguwa kuwa tsakaninsu mutunta juna nan dai "yan sanda suka sasantasu kowa yadawo gida ,ita kuwa mommy dataga Abdul yashigo ta kalleshi taga yana dariya ,tace yaya dai ,yace kinga yadda yayi muguwar nadama sai hkr yake bayarwa wai in Allah yayarda bazaisakeba mommy tace to yamasake mana mu bamushiga harkarsaba shine xaishiga tamu ,aini wlh yazamar mana annoba a unguwar nan ,shi ai ba,a ta6a fadar mugun halinsa ba,kuma ansan yana dashi ,ai saidai kawai Allah yashiryeshi ,cewafa akayi har yankankai yakeyi harda dakin da ba a shiga a gidan Amman banganiba Allah natuba ,shidai Abdul sai dariyar mugunta yakeyi ,yace wlh mommy sai kinga idonsa kamar mutumin arziki duk yayi tsuru- tsuru ,yace mommy ina mutumin nawa ,tace bacci yayitayi da yaci kuma yak'oshi nayi mamakin wayon sultan ,ai wlh duk Wanda yayi kuskuren sake gayamasa kotoce zatarabamu ,tace to Allah ma yakiyaye gaba ,yace ameen .

Azuminmu yau idan munkai koma ,to ak'a idarsu Abdul idan azumi yakai goma suna raban kayan abinci ga wad'anda basudashi to awannan karanma hakan take ,rabo sosai sukeyi habu shine dan aken kawai ,sai wata giggiwa yakeyi sai kace shine alh dan idan yakai Aiken akabashi tukuci kin kar6a yakeyi wai anraina masa hankali sai kace wani yaro ,aishima shekara iwar haka shine merabawa,sai dai yawancin mutane sunsan halin karyarsa suyitayi masa dariya.

Kuyi hkr da wannan

💖💖💖💖ZAZZAFAN RABO💓💓💓💓

💫💫💫Aisha Umar Indabawa💫💫💫

🌟🌟🌟marubuciyar littafin Meka Maidani🌟🌟🌟

📱Typing📱

🅿️ 1️⃣6️⃣

🌹🌹🌹ina godiya masoya littafin zazzafan rabo🌹🌹🌹
Chapter 15 · 0% Book details