← Book details Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 18

Sashe 14

Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

***kiyi hkr naje gida nakwana biyu ,Amman xandawo insha Allahu ,tace saida kikasabamin da xaman mutum biyu sannan kice za kitafi ,nace kiyi hkr zandawo mukayi sallama nafito duk fuskarta babu dadi sbd yaya sai dare yake dawowa ,a bakin layinmu aka sauke ni,nikuma nak'arasa da kafata cikin layinmu ,a dai dai get din gidansu Na hangoshi a tsakiyar mutane sun shinfida babban cafet da alama yana cikin farin ciki ,nace to Allah yatemakeni nawuce lfy ,dan nasan halin mutumina ,Na sunkuyar da kaina banasan yaganni asheyaganni ,harna kusa wucewa yace Salwa andawo daga yawan tazubar dinne ,nace la yaya bangankabane ina wuni nayi saurin tsugunawa ,anje gidan amare aci naman kaji ,dan Allah Salwa kirage kwadayi dasan abin duniya ,kamar Na nutse dan kunya yadda naga sauran abokan nasa sunsa dariya ,na sunkuyar da kaina nawuce ina takaicin abinda yakeyi min a gaban mutane shi gani yakeyi kamar burgewa yakeyi ,nadawo da farin cikina Amman tun kafin nak'arasa gida ya wargazamin komai ,Allah kadinga sakamin akan irin wulak'ancin da yakeyi min tunda nidai nasan babu abinda nakeyi masa ,bazan iya fada dashi ba ,dan umma ma gani takeyi rashin kunya nakeyi masa dan batasan abinda yakeyiminba ne sai dai Allah yayimin maganinsa shi kuwa Abdul bayan ta wuce dariya yasa ,wani abokinsu yace gaskiya Abdul abinda kakeyi bekamataba ,kai bakada wani abinyi saidai kadinga kunyata yarinyar mutane ,idan Santa kakeyi kafito mana kagayamata ,Amman abinfa yayi yawa ,in kuma bakaso to ni inaciki Santa nakeyi da gaske bawasaba ,yace to ni ina ruwana ,aini koda kyau ta akabani Salwa babu abinda zanyi da ita ,idan har kaga nakar6i Salwa to saidai idan a aljanna akace za,akasa ko mommy tace idan ban auretaba zata tsinemin albarka ko tace babuni babu ita to aguje zanyarda ,Amman "yar aikin gidana tafita matsayi da mutunci tunda ita bata wulak'anta kantaba ,Amman kai idan kanaso zanshegema gaba Amman duk abinda yabiyo baya babu ruwana,Na tabbar da idan ummanka taji babu abinda zai hana ta zazzabgama mari tace bakada hankali ,duk sauran abokan sukasa dariya ,wani daga cikinsu mesuna amir yace gaskiya katsani yarinyar nan aiko cikin shege tayi iya horon da za,ayi mata kenan ,idan nice yarinyar sainayi maganinka tunda kaine munafikin ta ,yanxo tasamu miji na kece raini Amman kayi mata bakinciki ,yace kodai kaima kanacikine amir ,aini idan inaso munafincinka bazaiyi tasiriba a kaina ba dan dai khairiyya tashigemin gabane ,dana shiga kuma sati biyu za asa agama komai tunkafin irinku munafikai kushiga maganar ,to tunda kun maidani munafiki abar maganar nabarku da halinku sukasa dariya wai yaji tsoro, suka shiga wata hirar,shi kuwa habu direba banda dariya babu abinda yakeyi yaji mugunta suna hada ido da Abdul saiya gintse fuska kamar ba shine yakeyin dariyarba ,yace kai zonan yaxo ya tsuguna kamar xaiyimasa sujjada ,yakama kunnensa yace banhanaka irin wannan munafinciba ,to shiga gida kace da nana me aiki takawo mana lemo da cake da wannan zaman banzan da mukeyi mundan tauna yashige gidan da saurin sa ,sukace gaskiya Abdul wannan direban naku yanada abin dariya ,kasan kwanaki a titin gidan gwanna naganshi yatsayarda wata yarinya ita kuma daga ganinsa a babbar mota sa kankanba takeyi masa,shi kuma sai dashe uban baki yakeyi ,kai idan kaga abin saiya baka dariya ,lokacin kuma yaci wata arniyar shadda wannan takance da wannan telan ya6atamaka wadda ko sawa bakayiba yace naganeta ,yace ranar kuma yayi sa,a a motar megida take kaga abin yayimasa dai dai kenan ,Abdul yace aishi haka yake ,ai ina ganin Na mema masa auren Salwa koda zankashe miliyoyin kudine tunda bawata tsada zatayiba ,wani ya kalleshi yace yanzo natabbarda bakada hankali Abdul sai kace "yarka ,to ko da " yarkace aika tanbayi ta,ayinta "yan wajen sukasa dariya ,lallai Abdul ka6atawa Ammar rai shida baya magana saida kak'ular dashi yayi magana,in Allah yayarda bakada mata sai Salwa ,kafin yak'arasa yakifamasa mari ,Allah ya isa tsakanina dakai kuma hakan bazai ta6a kasancewaba mugu kawai me mugun baki kagani a kanka .

Yace aini idan an bani inaso tunda duk yadda akesan mace takai ,sai dai tanada mahassada a gari masu kashemata aure ,kaidinma wada kakeyi abokina dakasan abinda tayi daka gujemata ,kometa ni ina Santa ai akwai kaddarar mutum kuma indai Allah yarubuta babu Wanda ya isa yahana ,shima habu direban dan naga 'katan 'kauyene shiya kuma rufamata asiri xaiyi wani yace aiko me Salwa tayi bazata rasa me aurentaba wlh ,dan Allah to abar maganar munafincin yarinyarfa mukeyi kenan ,saikace kannen uwarta munafikai kawai ,yadauki mukullin motarsa yafice da gudu sunsan halinsa bayasan irin wannan abun ,danshi ko maganar budurwa bayaso bare yace ya nasan wata Ammar kenan sai dai idan sunayi yace Allah yashiryeku tunkafin kutafasa zaku kone ,ita kuwa salwa da bakinciki tashiga gidan ko ummanta saida tagane a fuskarta tadaiyimata shirune ,itadai Allah yasa bada matar yayan natasukayiba ,dan bata kaunar ace itace ta turata danta takura musu ,tagaida umman tata tace kowa lfy sai a lokacin hankalinta ya kwanta ,a hankali kuma tasaki ranta sukaci gabada da hirarsu da salwan ,mamaki sosai salwa tadingayi dan kullun umman tata cikin yimata fada take akan taki yin hankali ,sai da salwan tayi tunani sosai sannan tagane sakin fuskar umman tata ,zuwan nazir ne ,to ko dai itama Allah ya amshi addu,ar da tadade tanayine .

Sai da akayi kiran sallar magariba sannan tamik'e danyin haramar sallah ,saida aka idar sannan umma tace to Salwa ga abincinan saiki zuba kici ,tace to umma ,tamik'e dan taduba taga umman metadafa ,sai taga tuwan shinkafa da miyar zogale ,miyar sai kanshi takeyi dan tayi niyar tabari sai tayi sallar isha sannan taci ,Amman budewar da tayi taji baxata iyaba tazuba tafito tsakargida hartanacewa da umma yaushe tayi wannan girkin batasani ba ,kinata aikin bacci ai bazaki saniba itadai tasa dariya ,abbanta bayadawowa sai anyi sallar isha,i ita kanta taga tsabar farincikin da yanuna da yaganta ,yace kaga "yan Hutu har gidan yayan naki ya isheki ,nidai nayi dariya nace sannu da zuwa Abba ,yace saukar yaushe nace da safe ,nace dagyar suka barni nadawo ,yace ai kuwa bakomawa zakiyiba ,bakiga yadda Abdul yake mitar tafiyarkiba ,wai kintafi bakya duba littattafanki gashi yajin aikin yayi nisa kuma kuna komawa xaku fara jarabawa nidai nayi shiru,yace Salwa iyayen yaronnan da kikasamu a gidan yayanki ,sunsameni a kasuwa wai sudai da gaike sukeyi tunda yaron da gaske yakeyi ,wai yamatsamusu basasan a dauki wani lokaciba nidainarufe fuska sbd zancen banawabane ,munacikinyin maganar saiga ya Abdul nan yashigo banso Abba yagayamasaba sainaga yawani washe baki yace Allah yasanya alkairi yasa ayi damu ,gaskiya Abba a wannan lokacin kar,a dauko wani dogon lokaci sbd abinda yake faruwa ,yace insha Allah hakan bazaifaruba ,yace Allah yasa.

Kamar da wasa abu ya kankama angama komai sunkawo kudin aurensu dansu a yadda sukeso Abba yasa musu sati biyu sai dai k'arfin badayaba ,dole suka hkr akasa wata uku shima ba,asan ran angonba .

Iya kuwa Salwa gdy kawai takeyiwa Allah shi kuwa Abdul duk ba,nasan ransaba ,sbd yanacewa Salwa bata cancanci samun yaro kamar nazirba sbd nutsuwarsa dasan addininsa shi kuwa yafisan tasamu babban mutum Wanda yayi sa,a da babanta koma yafi abban nata ,sabida acewarsa tazubar da mutuncinta da kimarta a idon wadanda sukasan wacece salwan saidai hakan Allah yanufa ,shida da yazowa da Abba akan mgnar habu direba tunda shima yafinkanci dan duniyar kansa sai kuma Abban yafara xuwar masa da mgnar shi kuma yanajin kunyar abban bare yayi bayani ,to Amman duk da hk yasan yadda zaiyi ,shi wlh gabadaya yatsani salwan koyace ba ita yatsanaba halinta yatsana ,danshi baya shiri da marakamunkai Salwa batasamu komawa gidan yayantaba sbd komawa makaranta da sukayi ,shi kuwa Abdul yanatasan suhadu da Salwa dan yayimata tatas to bashida hanya sai a school ,bayan sun fito saga laccar sukasamu wata bakin bishiya suka xauna daman kawai kujeru a wajen ,fauxee yace Salwa nifa yinwa nakeyi dan bankaryaba Amman kinga dan guzirina a jaka ,tazuge jakar tafito da cake da kaza da lemon roba tace to bismillah Salwa,kinga nifa nakarya ta harareni tace ai yanzo ya zazzage tunda yaufa mun wahala ,ta dauki cake takai bakinta tace kinsan kuwa rahma ta haihu ,nace dan Allah me akasamu tace "yan biyu duk maxa mukace to Allah yaraya mata mukace amin a tare ,takai hannunta kan kazar kenan ta dauki cinya kenan takai bakinta suka hada ido dashi ,yayimata alamar tazo da hannunsa ,ita kuwa tunda suka hada ido dashi gabanta yafadi ,banda innalillahi babu abinda take fada

🌹🌹🌹🌹ZAZZAFAN RABO🌹🌹🌹🌹

💫💫💫Aisha Umar Indabawa💫💫💫

🌟🌟🌟Marubuciyar littafin Meka Maidani🌟🌟🌟

📱typing📱

🦚page1️⃣5️⃣🦚

______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

💞💞💞ina godiya masoyan wannan littafin ina matukar jin dadin yadda kuke kaunarsa 💞💞💞
Chapter 14 · 0% Book details