← Book details Zaheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Zaheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Biki yazo yan uwa duk yan uwa sun zo yan uwan Zaheeda dubu dari biyar suka hada suka kawo wa Goggo wai asai mata wani abu, Daddy yace ai an gama komai amma tunda haqqinta ne sun riga sun bata to asiya mata wani abu.
An shiryo mata lefe na gani na fada lallai masu abu da abunsu wannan tsadadden lefe sai kace wadda za a kai wa diyar shugaban qasa.
Biki yayi biki Mamy da kanta take shirya Amarya da qayatattun shiga da ga wannan zuwa wannan, shiga ta burgewa da qayatarwa amarya tayi kyau har ta gaji da kyau sai kace tauraruwa in ka ganta kamar ka sace ta ka gudu ta zama kamar furen flower dan kyau.
Cikin zuciyar ta kuwa kamar ta fito saboda tsabar tsoro yau zaa hada ta da makashin to.
Qawayenta su biyu kawai suka zo saboda su Kadai suka sani daga zeey sai Feedausi kurfi.
Deelah dai ce ta gayyato friends dinta kamar ita ce amaryar su Baseera Umar Iro, saadatu Karfi, Zainab Ndagi, su Fateema Inde da dai sauran su.
Su fatee sai shewa suke suna tsokalarta ita kuwa abun duniya duk yabi ya dame ta ta rasa ya zatai kawai sai ta fashe masu da kuka😭😭 ai kuwa nan suka hau lallashi da kyar suka samu tai shiru.
Bayan sallar magriba aka zo daukar amarya kuka take Sosai gani take kamar baza ta qara ganin su ba kamar mutawa zatai.
Da kyar aka samu aka banbareta da ga jikin mamy aka sata mota 🚗 suka tafi.
Deelah ta miqo mata waya tace gashi mamy nason magana dake ta karba sai sheshheka take Mamy tace baki bar kukan ba kenan oya ki nutsu kiyi addu'oin dana baki kafin ku isah kuma kiyi na shiga gidan sannan ki shiga da qafar dama tace to Mamy Nah.
Gida ne ba qarami ba babba ne ya hadu Fateema Inde sai santin gidan suke Zainab Ndagi ta gwale ido 👀 sai abun duniya take gani 😉.

Gidan amarya kowa ya fashe an barta sai ita kadai tsuru a wannan makeken gidan sai kuma mai gadi da yake bakin gate.
Jin motsin bude gate yasa yan cikinta juyawa dif ta dauke wuta.
Jin qarar bude qofa 🚪 Yasa wata zufa karyo mata dan tasan yau ta Mutu.....................

🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨✨🌟✨

Written by the 💅🌟✨DIVAS🌟✨💅

Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Junia.

(4 any comments or correction) 👇
07032266308
[1/27, 9:17 AM] Aysha Mazoji: 💏💍ZAHEEDAH💏💍1⃣4⃣

Murda qofar yayi 🚪 ya shigo dakin daga kansa yayi ya ganta zaune duk ta wani takure nan take ya daure yace ke mi kk yi a room dina nan take gabanta ya fadi dama room dinsa ne? Ita ai bata sani ba tunda suka zo nan akayo da ita cikin hargagi yace am I not talking to you cikin in ina tace yah kayi haquri bansan room dinka bane.
Wata muguwar harara ya wurga Mata yace to akwai room din ki ne duk cikin gidannan yace oya get out of my side before I remove your eyes from there socket, stupid kawai.
Tashi tayi amma ta kasa tafiya saboda ya na tsaye bakin qofar bata hanyar da zata wuce. Ke wai wasa nake dake ne oya zoki wuce ta gefensa ta raba ta wuce amma sai da suka gogi juna ta wuce ta fito parlour nan ta rasa ya zatai kada ta shiga wani room din ya kuma cewa nasa ne kawai sai ta Samu kujera ta haye nan take kuwa bacci ya dauke ta.
Fitowa yayi cikin pyjamas dinsa zai nufi kitchen domin hada coffee ya ganta a parlour ta wani duqunqune kan kujera yaja tsaki yayi wucewarsa ya gama abunda zaiyi yayi wucewarsa dakinsa.........
Sai dai kuma mi koda yagama aikinsa sai bacci ya gagaresa sai tunanin heedah yake tashi yayi ya nufi qofa ya murda...............

🌟✨🌟✨🌟✨🌟🌟✨
🌟✨🌟✨🌟✨🌟

Written by the💅 🌟DIVAS🌟✨💅
Aysha, Nafeesah Mazoji &Amira Jibia.

(4 any comments or correction) 👇
07032266308
[1/30, 12:42 PM] Aysha Mazoji: 💏💍ZAHEEDAH💏💍1⃣5⃣

Har ya je wurin kujerar kuma sai ya fara tunanin what the hell is wrong with me, what am I doing? To ina ruwa na da ita ne
Kwafa yayi sannan ya juya ya koma dakinsa yayi kwanciyarsa.

******************
Da asuba ya tashi ya yo alwala ya fito yayi tafiyarsa masallaci har ya dawo bata tashi ba saboda gajiyar da tayi zuwa yayi inda take kwance ya sa qafa ya dan buge ta yace ke dama arniya ce ne bakya sallah? Cikin in ina tace yah deel bansan asuba tayi bane yace yanzu ai kin sani yayi wucewarsa daki.

Ta dauki tsawon lokaci a tsaye don tana jin fitsari gaya bata san inda zata nufa ba ai kuwa sai gashi ya fito yace au baki tafi sallar ba kenan tace yah bansan toilet din ba .
Tsaya wa yai kallonta sannan yace do you know that you are very stupid and I'm not going to tolerate your stupidity. Of all the rooms in this house yet you don't know how to get to a toilet. kwafa yy yace kafin na fito daga kitchen ki bace min daga sight yayi wucewarsa zai hada coffee.
Ai kuwa ta nufi wata qofa ta shiga nan take ta sauke ajiyar zuciya da taga bedroom ne, ta shiga toilet tayo alwala tazo ta bude gyalenta tayi sallarta bisa carpet sai data gama addu'o'in ta sannan ta Kwanta bisa bisa carpet din ai kuwa sai bacci soboda ta gaji sosai.......

Written by the 💅🌟✨DIVAS✨🌟💅
Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira jibia
[1/31, 9:17 PM] Aysha Mazoji: 💏💍ZAHEEDAH💏💍1⃣6⃣

Bacci tayi sosai don sai wurin 10 ta farka ta tashi ta shiga toilet taga sabon toothbrush tayi sannan tayi wanka ta fito daure da towel ta rasa to ina zata samu kayan da zata sa kawai sai ta maida kayanta tana tsakar zuge zip dinta kawai sai ganin mutun tayi ya shigo tai saurin dauko veil dinta ta rufe jikinta.

Kwafa yy sannan ya wurga mata phone 📱 kawai yai tafiyarsa yana tunanin she's really a big villager daga shigarsa ta wani rufe jiki kuma wai da kayafa a jikinta. Kwaila kawai da ita.

Ita kuwa tayi tsaye da phone a hannu ta rasa me zatayi dashi can taji an kira ta duba taga number n Mamy ai kuwa taji wani sanyi ta daga ta gaisheta Mamy tace ya kadaici tace Mamy nayi missing dinku wlh tace ai zaki saba tace yawwa Mamy kayana fa tace ki duba cikin closet zaki gansu tace wane room tace ko wane room akwai kayanki so ki duba tace na aiko muku da breakfast Don Allah kici nasanki da rashin cin abin ci.
Tace zanci Mamy yaushe zaku zo tace zamu inshaa Allah tace Mamy deelah fa tace kufa bakwa rabuwa da shirme daga kwana daya sai kuma ta kama zuwa.
Kin dai san halin yayan naku so you have to be extremely careful with him tace to Mamy Nah zan kiyaye. To Allah ya yi muku albarka.

Suna gama waya ta bude closet sai kuwa taga kaya daidai ita ta dauka ta saka sannan ta dauko zunbulelen hijabinta ta saka ta fita palourn tayi hanyar da taga kamar dining room ai kuwa taga dainin cike da breakfast ta zauna tadan ci sannan ta tashi ta wuce dakin da ta kwana tayi zauniyarta ta kunna plasma din da ta gani ta gano CN (cartoon network) taci gaba da kallo don tana son cartoon.

Shi kuwa ya cika yayi dam kamar zai fashe tsabar fushi don yarinyar ta bata masa rai sosai 😡.Tashi yayi ya nufi room din da take yana tunanin yau sai ta sani kuwa..............

Shin me ta masa? Guess

Written by the💅 🌟✨DIVAS✨🌟💅

Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia.
[2/2, 7:24 PM] Aysha Mazoji: 💏💍ZAHEEDAH💏💍1⃣7⃣

Kallon ta take Hankali kwance tun kafin ya Shigo qamshin perfume dinsa yai mata sallama ta dago da sauri cikin bugun zuciya ai kuwa sai gashi kamar wani zaki ya wurga mata harara yace ke wai wace irin wawiya ce ke ne?
Cikin rawar murya tace yah me nayi yace kina tambayana me kk yi ba tun dazu na kawo miki phone dina ba me ya hana ki meda mun da kk gama.
Tace yayah I'm sorry na manta.
Ya kalli idanunta duk sun cuko da hawaye
Yace ke kuma baki da aikin yi sai ba mutane haquri komi you are sorry.
Nidai kinsan ba wasa nake da keba so kibini a hankali yayi kwafa ya juya yayi ficewarsa daga dakin.
Kallon da batai ba kenan ta ci gaba da rera kuka ita batasan me yasa yah Deel ya tsane ta ba ita a tarihin rayuwarta kaf bazata iya cewa ga abin da ta taba yi masa ba hakanan dai ya tsane ta.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨.

Kwanci tashi anyi sai da aka yi sati biyu da bikinsu sannan Mamy tace ta fara girki don kullum daga gida ake kawo musu tsakaninta da boss din kuwa ba kome sai hantara ba wata maganar arziqi dake hadasu shiyasa ma take wuni a daki in ta fito to saidai in abinci aka kawo.
Wani lokacin haka nan zai shigo har bedroom din yai tai mata fada na ba gaira ba dalili.
Shiga kitchen tai ta hada delicious lunch Fried rice with Ham & Hotdog (some may misunderstand Hotdog for a recipe made with dogs 🐶, so to avoid any misunderstanding "Ba da kare ake yi ba ").
Ta hada juice dinta na watermelon 🍉 mai sanyi duk ta jera bisa dining table.
Ta wuce tayi wanka tayi kwanciyar ta.
Chapter 3 · 0% Book details