← Book details Zaheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 23

Sashe 21

Zaheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yy tare da shafo cikinta yace kinsan tunda babies dina suka shiga 8 months Mamy ta matsa mun dan na meda ki gabanta right? Ta daga Kai sannan ya ci gaba to yau bayan naje office mamy ta kira ni tace nazo za muyi magana.
Da naje sai tace mun the best solution shine na dawo dake gida cause in na fita wurin aiki labour ya kama ki fa kuma dama ni ina da damuwar barinki ke daya a gida to dan haka yau zamu koma gida.

Murmushi tayi tace yawwa dama in ka tafi office ina zama lonely Wlh.
Yace amma fa daki daya zamu riqa kwana fa.
Tabe baki tayi tace naji dai mu tafi.
Yace to bari nayi packing up ko?

Kaya akwati uku ya cika masu sai kayan babies din da yake sawowa akwati biyar.
Sai da ya gama kai wa cikin motar kafin yazo temaka mata ta tashi ya saka mata hijab din tare da saka mata maternity shoe dinta saboda duk takalman ta sun mata kadan.

Cikin 40minute suka isa gida don baya gudu wai don kada ya girgiza ta da yawa.
Kafin su isa har qafafunta sun kumbura kuwa.

Mamy dake tsaye tana jiran isowar su da sauri ta nufi Heedah ta kama ta tana mata sannu.
Bisa kujera ta zaunar da ita sai faman sannu take mata dan ba qaramin tausaya mata take ba.
Sosai Mamy ke kula da ita bata barinta tayi komai.

Ana saura kwana biyu EDD dinta ya cika tana zaune parlour ita kadai don Mamy da Goggo sun tafi barka amma bazasu dade ba.

Cartoon network take kallo. Yah Adeel ne ya shigo tare da sallama, da sauri ya aje brief case dinsa ya qarasa wurinta rungumo ta yy ta side don cikin baya barin normal hug.

Baby girl ke kadai a gidan daga Kai tayi tace yanzu su Mamy suka fita amma tace da sauri zasu dawo.

Yatsunta ya kama yy kissing Kafin yace baby girl qumban ki ya fito bari na yanke miki, tace kuma fa duka last three days ne Mamy ta gyara mun fa.
Yace kuma har sun fito, nail clippers and cutter ya dauko ya fara yanke mata suna labari.
Ji yayi tayi shiru sannan ta riqe masa hannu dagowa yayi don ganin meke faruwa.
Gani yy ta rufe ido sannan ta cije baki da sauri ya dawo kusa da ita yana baby girl me ya faru ko mu tafi hospital ne, da sauri ta qara riqe hannun sa tare da girgiza kai.
Sai da tayi one minute a haka kafin kuma ta koma normal.
Qara riqe mata hannun yy yace baby girl what just happened.
Tace Yah bafa wani abu bane it's just a contraction.
Da qarfi ya what? That's not just, your face shows that you were in a lot of pain.
Tace but Yah it's normal to have minor contractions before the labour itself.
Yace and who told you that.
Tace Yah Doc Isabella ta fada mun a last appointment din mu, tace zan ringa having this contractions.
Yace but ai baki fada mun ba tace that's because it's not a problem.
Zaya qara wata maganar suka ji sallamar su Mamy.

Ranar da EDD dinta ya cika tun asuba take jin ciwo ga kuma da taje tsarki taji wani ruwa na fitar mata kuma ba fitsari bane. Ciwo take ji amma ta daure bata bari kowa ya sani ba har Yah Adeel ya tafi wurin aiki, sannan ne tace ma Mamy zata danyi bacci ta shiga dakin ta.
Tun da ta shiga bedroom din take zagayen dakin don Doc Isabella tace mata in taji irin wannan ciwon ta dan ringa yawo kada ta zauna wuri daya. Ga Adduan da take tayi.

Haka tai tayi sai dai in wani ciwon ya taso ta riqe gado fam kamar zata karya shi, zufa take yi kamar ta hadiyi kunama.

Can taji ciwon ya fi qarfin ta ta kwala ma Mamy kira da gudu Mamy ta shigo dakin ganin Heedah a zaune qasa tana ta zufa yasa ta saurin kamo ta suka tashi, suna zuwa parlour wani ciwon ya taso ta riqe Mamy kam tana Addua.
Bisa kujera Mamy ta aje ta sannan ta ruga kiran Goggo.
A sakwane suka shigo tare suka kamata suka fita already driver is ready kawai mota suka shiga sai asibiti.
Da yake asibitin turawa ne daki daya aka ware ma Heedah sannan aka kira Doc Isabella.
Tana zuwa tace ina Adeel sai lokacin Mamy ta tuna basu gaya ma kowa ba hakanan suka taho.
Waya ta buga ma Adeel tace yazo suna hospital.
Ai kuwa cikin fifteen minutes sai gashi ya iso a hargitse ...................................

Written by the 💅🌟✨DIVAS🌟💅

Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia.

(4 any comments or correction )👇
07032266308
[5/6, 7:36 PM] Aysha Mazoji: [5/4, 7:21 PM] Aysha Mazoji: [5/4, 7:00 PM] Aysha Mazoji: 💏💍ZAHEEDAH💏💍7⃣6⃣

Yana isowa kai tsaye dakin ya shiga da sauri ya qarasa wurin Heedah wacce ke kwance an manna mata wata computer sai zufa take yi ga nurse guda biyu ga kuma Doc Isabella.
Murmushi Doc tayi ma Adeel tace are you ready to be a Daddy? Yeah yeah I'm, but how is she doing.
She is doing great, she is almost six centimeters dilated.

Salatin Heedah ya katse musu zancen da suke yi, hannun Adeel ta Kama ta riqe har sai da yy yar qara.
Sai da ciwon ya lafa sannan ta ringa meda nunfashi.
Qara jawo hannun sa tayi tace Yah bazan iya ba akwai ciwo sosai pls help me.
Shi ma hawayen ya fara yana sorry baby girl duk ni na jamaki kiyi haquri Don Allah.

Wani ciwon ya qara tasowa tuni ya rungumo ta yana shafa mata baya har ciwon ya lafa.
Doc Isabella ta qara duba ta taga har takai eleven centimeter dilated.
Murmushi tayi tace Heedah you are doing just great, you will feel an urge to push now don't hold it back, just do what you feel is natural okay? Da sauri Heedah ta kada kai.
Doc tace Adeel you have to hold and support her this is the birth part okay?
Da sauri ya kada kai ya koma bayan Heedah ya kwantar da bayan ta bisa qirjinsa.
Aikuwa sai ga ciwo tare da nishi sun taho tare tunda Heedah take bata taba jin irin wannan balain ba.
Da ciwon ya kwanta kuka ta saka ita wlh bazata iya ba, Adeel shi Ke lallashin ta wanda shima in ciwon ya taso kuka yake sakawa har sai ya lafa.
Haka suka yi tayi har aka samu kan daya ya fara fitowa amma time din ta riga ta galabaita sosai.
Computer n ne ya fara wani dan qara kadan.
Doc ta kalli Heedah tace you have to be strong okay Adeel tell her pls, she should not give up.
Da sauri Adeel ya kalli Heedah wacce idonta ya fara juye wa cikin kuka yace baby kada ki gaji pls kiyi haquri ki daure you have to do this for me and for our babies Pls.
Wani nishi ta qara yi da dukkan qarfinta ta riqe hannun sa kuwa har sai da hannun yayi qara.
Doc tace Adeel the baby is coming you have to witness the birth of your first child. Come here, da sauri Adeel yy wurin aikuwa yana leqawa ya sanqare kafin ya zube qasa sumamme..............................

Ruwa aka zuba ma Adeel kafin ya farfado aikuwa da sauri ya koma wurin kan Heedah dake nishi aikuwa kukan jariri ya cika dakin Doc ta kalle sa tace you have to cut the umbilical cord Daddy and it's a boy wani murmushi yy kafin ya ansa scissors yayi cutting umbilical cord din sannan ya karbe yaron daga hannun nurse din ya dawo wurin Heedah dake meda nunfashi.
Baby girl kalla boy din mu Masha Allah kallarsa. Nurse ta matso tace ya bata babyn zata masa wanka No ya fada da sauri nurse din tace look the other baby is coming ...........
Da sauri ya miqa mata shi ya koma wurin Heedah wacce sabon ciwo ya taso mata.
Cikin five minutes baby ya qara fadowa wannan karan ma baby boy ne kuma Adeel ne ya yenke cibiya.
Heedah shiru tayi kamar tana bacci don ba qaramin galabaita tayi ba.
An wanke jarirai duk ansa musu kayan da hospital din ke providing.
Matsala daya har yanzu afterbirth (uwa ) bata fito ba.
Doc hankalin ta ya fara tashi, wurin computer n da aka sa ma Heedah ta nufa tana dan dubawa.
Oh my goodness ta fada da sauri Adeel ya kalle ta yace what what's wrong.
Juyowa tayi tana kallon Heedah tace there is another baby ........................

Written by the 💅🌟✨DIVAS🌟💅

Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia.

(4 any comments or correction )👇
07032266308
[5/4, 9:24 PM] Aysha Mazoji: 💏💍ZAHEEDAH💏💍7⃣7⃣

Da sauri Adeel ya kalli Heedah wacce idonta ya raina fata.
Cikin ten minutes Heedah ta qara sunkuto wani baby n.
Ba abunda Adeel ke fada sai ALHAMDULILLAHILLADHI BI NI'IMATIHI TATIMMUSSALIHAT. (All praise is for Allah by whose favour good work are accomplished)

Wannan karon baby girl Heedah ta haifa Adeel hada su kuka da yaga triplets Heedah ta haifa.
An gyara yaran gwanin ban shaawa an saka ma boys din blue soft cotton unisex baby girl din kuma pink aka saka mata da yan hulunan su kamar ka sace su ka gudu.

Sai da aka gama gyara Heedah sannan aka nufi dakin Hutu da ita don ko babies din bata gani ba tunda ta haifa last babyn ta take bacci.

Adeel ya ma mance da zancen su Mamy sai da suka fito yana dauke da yara biyu sannan yagan su da sauri suka taso hada su Daddy suna yaya.
Adeel yace Daddy ga yaran da sauri Mamy ta amsa guda Goggo ma ta amsa guda.
Suna ta sam barka, Adeel yace Daddy Heedah yan uku ta haifa fa.
Dukkansu suka juyo kallonsa galala.
Gudar ya amso daga hannun Doc ya miqa ma Daddy yace ga Daddy's girl nan.
Aikuwa duka sai murna Mamy hada su kuka don farin ciki.
Dakin da aka kai Heedah nan aka kai babies din aka sa musu gado uku aka kwantar da su sai baccin su sukeyi.
Chapter 21 · 0% Book details