← Book details Zaheedah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

Zaheedah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hargitse ya shiga dakin ganin Heedah na tsalle tana yarfe hannu tana kakkabe cikinta.
Da sauri ya qarasa ya riqe ta yana baby girl me ya faru, what's going on, ya aka yi.
Da qarfi ya riqe ta don taqi daina tsallen kuma taqi daina kukan.
Da kyar ya samu ya zaunar da ita yana qara tambayar ta.
Cikin kuka tace Yah wani abu ya fito man a ciki.
Yace baby girl wane abu buda na gani.
Rigar ta yaye masa kallon cikinta yy tare da zare ido don ganin yadda ya koma.
Innalillah ya fada ai kuwa ta qara rudewa ta kuwa qara saka wani ihun.
Da sauri ya tashi ya dauko mata hijab dinta ya saka mata.
Daukar ta yy don yaga kamar ba ta tafiya sosai.
Cikin mota ya saka ta, wani irin fisgar mota yake yi ita kuwa Heedah sai qwala kuka take kamar an aiko mata da saqon mutuwa. Shi kuwa Adeel sai tsula gudu yake kamar zai tashi sama.

Cikin 30 minutes suka isa gida, sunayin parking ta balle murfin mota ta fito shima a sakwane ya fito ko marfin motar bai rufe ba.
Gida suka shiga Heedah sai qwala ihu take.
Ihun Heedah ne ya fito da Mamy da Goggo wanda suke zaune suna fira don daddy bai dade da fita office ba.

Mamy ce da sauri ta kama Heedah tana tambayar ta wa ya rasu, me ya faru.
Kukanta kawai take yi.
Mamy ta juya wurin Adeel tace kai me ya faru ne, ka sanar damu mana kunzo duk kun tada mana hankali.

Cikin in ina Adeel yace Mamy wani abu ne ya fito mata a ciki.
Mamy tace Subhanallah me ya fito mata kuma.
Adeel ya matso kusa da Heedah wadda ke kuka har da su majina.
Hijab din jikinta ya yaye tare da dage rigarta yace Mamy kinga jiya lfy qlw muka kwanta yau muna tashi muka ga ya zama haka.

Ajiyar zuciya Mamy da Goggo suka sauke a tare.
Murmushi Goggo tayi tace yaro yaro ne dai.
Mamy tsoki tayi tace shine duk kuka bi kuka rude haka.
Ke Heedah yi ma mutane shiru. Ji yanda kk kuka har da su majina kamar wata qaramar yarinya.

Sai da Heedah tayi shiru sannan su Mamy suka zauna, Mamy ta kalli Adeel tace to soldier sai ka samu halin zama ko?
Kusa da Heedah ya zauna yana kallon yadda su Mamy basu dauki maganar da mahimmamci ba.

Mamy tace Goggo yi musu bayanin ko mi ke faruwa.
Goggo ta nisa tace wane bayani zan musu kawai a fadi musu kai tsaye.
Kai Adeelu matarka ciki ne da ita.
Cikin mamaki Adeel yace amma Wlh Goggo jiya bata da ciki yau fa ne ya fito.
Kuma yau dinma da safen nan.
Heedah ta ce Wlh Mamy jiya banda ciki yau ne ya fito.

Mamy tace har yanzu dai baku girma ba, ba kamar kai Adeel.
Yanzu duk symptoms din mai ciki kai baka ganewa girgiza kai yy tace to Heedah dai ciki ne da ita kuma tun ba yau ba muka sani.
Abunda dai ke ban mamaki yadda yy girma haka don a lissafin mu yanzu cikin watansa uku amma bamusani ba ko zai kai hudu. Wannan sai anje asibiti sai a auna a gani.

Adeel jin Heedah na dauke da babyn sa yasa sai washe baki yake dadi har a amadun kunnen sa.
Heedah ce dai tayi shiru don Ita kunya ma taji da aka ce tana da ciki.

Sai bayan zuhur prayer sannan suka wuce gida da sharadin zasu je asibiti a duba lafiyarta

Zo kuga tattali wurin Adeel bayan sun koma gida kamar zai maida ta ciki haka yake ji baya barinta tayi komai sai in ta matsa sosai sannan yake barinta shima ba mai wahala ba.
Sunje hospital kuma an tabbatar musu da twins ne cikinta..... .................................

Written by the 💅🌟✨DIVAS🌟💅

Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia.

(4 any comments or correction )👇
07032266308
[5/6, 7:36 PM] Aysha Mazoji: [4/29, 7:05 PM] Aysha Mazoji: 💏💍ZAHEEDAH💏💍7⃣4⃣

Authors note :--Don Allah ayi haquri da rashin posting da banyi ba for so long it's because I'm going through some phase of life so wish me luck please and I also need your prayers, and finally I love you all Heedah s lovers 😘😘😘😘😘😘

Bayan two weeks suka koma hospital don suna da appointment da Doc.
Da yake asibitin turawa ne wata Doc ce mai mutunci zasu ringa gani har ta haihu.
Sunan Doctor n Isabella so, suna kiranta da miss Isabella.
Sai da suka gaisa sannan taba ma Heedah hospital gown ta saka zasu yi mata awon jini sannan zaa dauki weight dinta sai da aka gama sannan tace ma Heedah ta kwanta bisa gado zaa mata ultrasound.

Wani dan gel kyakkyawar baturiyar ta dauko tare da yaye rigar Heedah, kallon Heedah tayi tare da h Yb Ybh murmushi tace this may be cold sannan ta zuba bisa cikin Heedah sannan ta dauko ta fara scanning din nan take computer n ya fara shuuuuu sannan sai ga faint heart beat har guda biyu.

Murmushi Doc tayi sannan ta kalli Adeel dake zaune bisa kujera ya riqe hannun Heedah gam.
Tace here are your babies, Adeel ya qara leqa computer yaga wani dishi2 yace I can't see anything here.
Miss Isabella tace here let me help you out ta fada tana nuna computer n tace right here is baby A and here is baby B, and they seem very healthy.
Wani murmushi Adeel ya saki saki tare da cewa Alhmdllh.
Doc tace do you want to know the sex of the babies da sauri Adeel yace no, no we want it to be a surprise.
Doc ta musu printing din pics din ultrasound din sannan suka mata godiyya tace next appointment in one month.

Kai tsaye gidan su Mamy suka wuce don tace tana son ganin Mamy.
Mamy tana ta murnan ganin Heedah sai nan nan take da ita. Adeel yace Mamy daga hospital fa muke, Mamy tace to hope komai normal ko? Yace eh ba wata matsala anyi ultrasound kuma ance yan biyu ne.
Mamy tace Kai Alhmdllh Allah abun godiya, tace wata nawa ne yace five months ne.
A nan suka yi yini sannan suka koma gidansu.

✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟

Bayan two months Heedah ce zaune tsakar parlour n su ta wani baje ga cikinta da yayi wani irin girma wanda in aka ce maka zata iya haihuwa da gudu zaka yadda.
Zaune take tana shan rake don tunda cikinta ya shiga wata shida take shan rake, rake baya isarta wani lokacin har bakinta da haqoranta ciwo suke mata amma haka nan take daurewa ta sha don ji take in bata sha ba to zaa samu matsala.
Don haka ko da yaushe ana aje mata rake.

Sallama Yah Adeel yy ya shigo parlour n, da sauri Heedah ta miqe duk da tana jin nauyin cikinta.
Qarasawa tayi ta rungume sa tare da cewa we miss you.
Yace I miss you too my babies.
Yace baby girl ba na hana ki tashi da sauri ba, don Allah ki bari, cikin shagwaba tace Yah nifa bana jin wuyar tashi Allah kuwa.
Yace Nidai na gaya miki bana son saurin da kikeyi wurin yin wani abu.
Jifa rannan Allah ya tsare gado ne bayanki kika fada to da qasa ne fa kk fadi ya zanyi.
Fuska ta bata tace Yah na gaya maka wannan ba laifi na bane wlh kicking dina yaran suka yi da qarfi, shi yasa.
Yace to in wurin saurin suka halbe ki fa, tace ai baza su mani haka ba ko babies din Abban su ta fada tare da shafa cikinta.
A hankali ya duqa wurin cikinta tare da kai kunnensa bisa cikin yace wai haka babies dina, baza kuyi kicking baby girl dinah ba.
Be the good kids you always have to be and stop kicking your maamah.
Addua yayi ma cikin sannan ya yi kissing dinsa.

Tashi yy tsaye yace but baby girl you have to be extremely careful okay?
Okay ta fada, riqe hannun sa tayi tace muje ka watsa ruwa sannan kaci abinci.
Yace daga gida aka kawo abincin ne? Tace ah ah na girka ne yace baby girl bana hana ki ba, tace Yah waina (masa) fa ce nayi da miya nasan kana so and it really test heavenly kaga cow tail ma nayi miyan da shi.
Kayi sauri ma kazo muci dan na qagara.
Yace baby girl me yasa baki ci ba da kk gama ba an hana ki zama da yunwa ba.
Murmushi tayi tace ai banji yunwa ba nasha rake da yawa kuma dazu Mamy bayan ka fita ta aiko mun da cabbage kuma naci sosai.
Good ya fada but na fasa wankan sai munyi taking lunch before nayi wankan.

...................................

Written by the 💅🌟✨DIVAS🌟💅

Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia.

(4 any comments or correction )👇
07032266308
[5/3, 1:17 AM] Aysha Mazoji: 💏💍ZAHEEDAH💏💍7⃣5⃣

Cikin Heedah ya shiga wata tara yanzu komai wahala yake mata don ma dai ta saba da aiki bata jin nauyin jikinta amma yanzu da cikinta ya shiga watan haihuwa wani irin nauyi cikin ke mata don har rinjayarya yake a times don madai wani lokacin tana boye ma Yah Adeel don bata so ya qara shiga wata damuwar wadda tafi wadda yake ciki.

Zaune take ita kadai a parlour n tana kallon cartoon network qwarai yana debe mata kewa in ta lallaba Yah Adeel ya tafi wurin aiki don da qyar take lallabasa ya tafi shima da yaje baifi yayi three hours ba ya dawo kuma throughout yana maqale da waya saboda ya sai mata waya don ya riqa jin lafiyar ta.

Kamar an jefo sa parlour n haka ya shigo Heedah tayi saurin yunqurawa amma ta kasa tashi don cikin ya mata nauyi ba kamar da ta dade zaune.

Da sauri Adeel ya qaraso kusa da ita sannan ya kamo ta yace baby girl gida zamu koma yau murmushi tayi tace what makes you change your mind so quickly.
Chapter 20 · 0% Book details