Sashe 7
Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zabura Yarima yai jin abinda maman tace wai shi za'a aurawa waccan mahaukaciyar yarinyar to ba gara ya mutu baiyi aure ba wayar dake hannunsa yai wurgi da ita cikin sakan ya burkicewa mama shigowar dady kenan ganin abinda yake faruwa da sauri ya karaso yana tambayar lfy maimakon ya bashi amsa sai yai baya luuuuu zai fadi cikin sauri dady ya tare shi har ya suma cikin gaggawa mama ta debo ruwa suka hau shafa masa Zainab na gefe tana kallo sauke ajiyan zuciya yai yana bude idonsa sai kuma ya sake rufewa girgiza shi dady yai amma ya kara suma dan haka yaci gaba da shafa masa ruwan har ya samu ya farfado kalmar farko daya ambata shine "Zainab ke nake so ba wata ba kada ki bari wani ya shiga tsakanin mu"shiru sukai jin abinda yake fada Zainab kan da sauri tabar gurin cikin faduwar gaba kallon dady mama tai sai kawai sukai murmushi a tare dady yace "tunda haka ne da kansa zaije ya fadawa mai martaba ga wacce yake so ba yazo yana suma ba "dariya sukai dai dai lokacin daya bude idonsa ya tashi zaune ganin duk jikinsa ruwa yasa yace "lafiya "? Mama tace "kai zamu tambaya lafiya kazo harda suma"cikin mmk ya kalleta "suma dai "? Dady dake masa dariya tun dazu yace "babana karka tsaya bata lokaci kaje ka samu mai martaba da kanka kace ga wacce kake so zai fahimceka tunda abokin kane "shiru Yarima yai bayan ya gama tuna abida ya faru yace "nifa bance inason wata ba"wani kallo dady ya masa yana cewa "naga alama tashi kaje tunda baka ce kana son wata ba muma ai bakaji munce kana son wata ba "mama data bishi da kallo tace baby Allah ya shirye ka bata fuska yai ya fita a palon ko takalmi bai dauka ba haka ya tafi part dinshi.
Hhhhh wasa ne
Gaisuwa dai maman khaleepha Allah ya kara zumunci.
INDO ina godiya sosai Allah ya barmu tare.
ABLA'S ke ta daban ce.
RABI'AHH kina raina har bansan yadda zance ba.
MRS TSARI wannan sai Naja'atu Musa Abubakar.
#
##
###
####
#####
#YUSRAHMS ABUBAKAR #
Mrs Al'ameen Ahmed ce.
[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: (*() *) (*()*) 📲Typing
👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑
💫ANNURI WRITING ASSOCIATION💫
Dedicated to
Safiyya Aliyu
&
Zarah Musa
#YUSRAHMS ABUBAKAR
Moral lesson
If people care for you, you also show care for them.
MANZON ALLAH (S*A*W)
You are unique, the first and the last, no success without you, you are the mirror of life, you are everything, you are the answer to every question, you have no limit YA RASULULLAH.
*Page 6
Mikewa mama tai bayan ficewar Yarima ta shiga part din da Zainab take a bakin gado ta same ta ganin mama yasa ta sunkuyar da kai murmushi mama tai tana zama ta rike hannunta ta soma mgn "dota kinji abinda ya faru ba sai na sake yi miki bayani ba shin kin amincewa babyna zaki aure shi eh ko a'a? kada ki ji kunyata fada min gaskiyar abinda ke ranki idan baki amince ba babu mai yi miki dole kara sunkuyar da kai Zainab tai ta kasa mgn gabanta na faduwa ganin tai shiru mama dake kallonta tace "haka yana nufin baki amincewa baby ba baki sonshi"? Cikin sauri ta girgiza kai muryan ta na rawa tace "amince zan aureshi halaccin dayai min bansan dame zan saka masa ba daya wuce nai abinda ya nema yanzun zanyi masa biyayya bazan saba masa ba zai sameni mai ladabi a gareshi"rungumeta mama tai cikin jin dadi tana sa mata albarka.
Ba yadda mama batai da Yarima ba akan yaje ya samu mai martaba amma yai kirmishishi yaki zuwa ganin idan ta biye mai wankin hula zai kaisu dare yasa ita da dady sukaje gurin mai martaba ba wani boye boye suka fada masa komai mai martaba da shima haushin angama mgn da iyayen Hajara yasa yace "to meyasa tun wuri baizo ya fada min ba gashi yanzu an karba masa auren wata to saidai ya hada su duka biyun ya aura ya tafi dasu sbd bazai yiwu mu mayar musu da magana ba "amincewa sukai duk da mama bata ji dadin hakan ba to amma ba yadda zasuyi suna nan zaune ya shigo fuskarnan a matukar murtuke dan ya kasa boye damuwarsa mai martaba dake kallon shi yace "Muhammad kayi hakuri nasan zakaji babu dadi amma kasan mu idan munyi alkawari bama canjawa ina so ka cire damuwar komai a ranka in Allah ya yarda zakaga riba da nasara a gabanka"numfashi ya sauke ba tare dayai mgn ba har kuwa suka bar gurin mai martaba ba wanda yaji muryar sa suna shiga palor mama ta kalleshi tana cewa "baby me yasa bakaje gurin mai martaba kayi masa bayani ba gashi yanzu ka jawa kanka auren mata biyu dan me kaki zuwa tun ranar da abin ya faru"? Shiru yai babu amsa dan shi kadai yasan abinda zuciyarsa ta shirya masa.
Yau saura kwana goma Yarima ya bar kasar mai martaba kuma yace bai amince ba ya gaji da ganinsa ba aure sai dai ayi bikin cikin kwana goman din daya rage ya tafi dasu sbd idan ya tafi ba'a san ranar dawowarsa ba Yarima ya firgita lokacin daya ji wannan mgn amma sai ya dake bai cewa kowa komai ba har saida ya basu mmk musamman daya nuna rashin damuwarsa akan mata biyun dazai aura Yaha kan dataji labarin wai Yarima zai auri Zainab yar karamar hauka tai dan gani take bazatai nasara ba Zainab tamkar barazana ce a rayuwar ta musamman dataji ance iya na Zainab din za'a daura ita Hajara saiya dawo tunda karatu take babu kunya taje gaban mai martaba da kukan ta tace a daura harda Hajara karatu baifi aure ba duk sanda suka dawo taci gaba mai martaba yayi mmk ganin irin kukan da take amma sai yace mata shikenan za'a daura farin ciki kamar ta mike tayi rawa a gaban sa.
Yarima baiso mai martaba ya amincewa Yaha ba amma sai yai burus da zancen.
musamman mama ta dauko mai gyaran jiki ake kula da Zainab tayi kyau tai fresh abinta har mmk take idan taje gaban mirror kamar ba ita ba.
Yaha ce zaune a palor kamar a mafarki taga Yarima ya shigo ba tare daya kulata ba yai hanyar dakin Hajara da sauri Yaha ta mike tana cewa "malam me zakayo anan kayi ajiya ne"? Batare daya juyo ba yace "niko nai ajiye tunda gurin mata ta nazo bai shafe kiba idan kuma so kike ki ganewa idon ki abinda yafi karfinki saiki shigo"yana fadin haka ya bude kofa ya shiga takaicine ya kama Yaha to uban me zaiyiwa Hajaran da har zata shiga ta tuno abinda daya fada mata tajuya zuwa palo tana jiran fitowar sa, Hajara dake kwance cikin mmk ta mike zaune tana zaro ido waje tace "lafiya "? Harde hannu yai yana kallonta yace "lfy nazo Duba lafiyar mata nane ko tana cikin farin ciki "da sabon mmk ta kuma zuba masa ido cikin jin dadi anya kuwa ba mafarki take ba Abdul-malik ne yazo duba ko tana lfy katse shirun yai da cewa bani number abbanki zan kira shi mu gaisa a matsayinsa na suruki na baban mata ta kuma uwar 'ya'ya na ya kare maganar da dage mata gira alamar ita yake jira jiki na rawa ta dauko waya tana cewa "gashi dauki"hade rai yai "fado min "fada masa tai sannan yace "tnk my wife take care good night "bai saurari wani abu daga gare ta ba yai waje dan bukatar sa ta biya ko kafin Hajara ta fito har ya fice Yaha ce ta tare ta "ke lfy ina zakije "? Ihu Hajara tai tana rungumeta tace "umma ki tayani murna Abdul-malik da kansa yanzu ya kira ni da matarsa wallahi umma ya fara sona"cikin mmk Yaha ke kallon ta amma batai mgn ba dan ita hankalinta bai kwanta da zuwansa ba gani take kamar wani abu yake shiryawa.
Ranar alhamis masarauta ta cika tab da baki na sauran wasu masarautun Yaha tayi mamakin rashin ganin dangin su na masarautar maidiguri amma data kira abban Hajara sai yace mata duk gobe zasu zo kafin ayi daurin aure sai sannan hankalinta ya kwanta.
Yaha na zaune taga wata budurwa ta shigo tana karewa part din kallo kamar mai duban tsafta mikewa tai tana kallonta tace "wace ke me kike nema anan ko kinyi batan kai ne idan ma makancewa kikai to maza ki saitawa kanki hanya ba nan ne part din da ake bikin ba har kike wa mutane kallon banza daga ina kika fito"? Dan murmushi tai tana duban yaha tace "ni bakuwa ce munzo biki daga masarautar Bauchi sunana Salmah part din Ibrahim Abban Mahmud nake nema"cikin faduwar gaba Yaha ta kuma bude ido a kanta tace "nan ne lfy"? Kai Salmah ta girgiza ba tare datai mgn ba ta juya ta fice a part din kasa zama Yaha tai tana tunanin ita kuma wannan ubanwa ya aiko ta amma tafi zargin Amina ce (mama) tana cikin zagaya palo Abba ya shigo tararsa tai da cewa "Ibrahim wacce yarinyar daka turo tazo ta min wulakanci"? Ko kallon ta Abba baiyi ba ya wuce da gudu tasha gabansa tana huci tace "me kake boyemin wacce ita "? Kallo mai ma'ana da yawa Abba yai mata kafin yace "i think ta fada miki sunanta Salmah daga masarautar Bauchi right nine na turo ta domin baki zo da part din daga masarautar kuba kuma kada ki sake ki rufe kofa dan anan tace min zasu kwana "wata ashar ta saki batare data shirya ba tahau masifar me yake nufi da haka amma ko ta kanta baibi ba ya fice abinsa haka ta karaci kumfan baki ita kadai tai shiru.