← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 20

Sashe 20

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

@Mrs Al'ameen Ahmad.
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲

👑Yarima Abdul-malik 👑

💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫

Dedicated to
❤Maman Khaleel
Zarah Musa dan Adam

#YUSRAHMS ABUBAKAR #

🅿️1️⃣6️⃣

Kuka ta fara yi masa ganin ana kallonta yasa yace"haba princess so kake mutane su dauka sato ki nayi? kinsan Abeed balle kice zai sayar miki da yara".

Cikin shagwaba tace"to ba kana jina ina tambayar ka ba ka rabu dani kuma kasan aida zafi raba d'a da uwarsa"

Yarima dake kallonta ganin da gaske take maganarta yace "to princess koda ma ace Abeed sayar dasu zaiyi ai ba damuwa tunda zaki sake haifa min wasu bibiyu sau biyar kinga goma kenan har sun ninka na da ".

Make kafada tayi tana cewa "nidai a'a bana son wasu ni yayana nake so dan bazan samu kyawawa kamar su ba".

"Tab waye ya fada miki zaki samu finsu ma kalli mana ai dadyn sune kyakkyawan ".

Kai ta girgiza "nifa bana so kawai kace masa ya kaiwa aunty Feshen yaran kafin mu koma danni ban yarda dashi ba"murmushi Yarima yayi cikin tsokana yace"Allah yasa kafin mu koma ya sayar dasu sai naga yadda zakiyi kodan gaba ta kaimu shikenan mun dawo sabi dal kamar amarya da ango wani ma inya kalle mu sai yayi tunanin honey moon zamuje "rabuwa tayi dashi karshe daya dameta sai kawai ta toshe kunne karma taji me yake ce mata.

Sai dare suka sauka ga mamakin ta wani matashin balarabe ne yazo ya dauke su kuma taji suna larabci da Yarima ko a mafarki batai tunanin ya iya ba.

Matarsa da farin ciki ta karbe su sakamakon tasan Yarima shekaru da suka wuce liyafa mai girma aka hada musu Zainab kam saida turanci suka gaisa ashe abokin Yarima ne a US suka hadu sunansa Aliyu shima yaransa biyu Aynul-hayat da Afrahim sun juma suna hirar yaushe gamo Aliyu na tambayar sa ina yaransa yace suna London suma sunzo yin sallah ne.

Bayan sunyi hajji ma basu tafi ba saida suka sake kwanaki Zainab harda rama tayi sbd tunanin su Ahmad ranar da zasu tafi murna kamar tayi fuffuke ta ganta a London haka taji Yarima na hankalce da ita amma baiyi mgn ba dan a yadda yaga tana zumudin nan saiya hora ta kafin ta gansu.

Lokacin da suka isa London karfe biyar bayan sunyi wanka sun huta Zainab ta tayar da rigima tana cewa " tunda mun dawo kaje ka karbo su ko ka bani adireshin gidan Abeed din ni naje da kaina na taho dasu"

Yarima kememe yace" ba zanje ba kuma bazan baki wani address ba sai sanda Abeed yayi ra'ayi dan kansa ya kawo su idan kuma yace yana son su zauna a gurin sa na bar masa su kawai saiki haifa min wasu".

Jin abinda ya fada yasa ta fara masa kuka amma ya rabu da ita ta dauka wasa ne abin nasa taga an shafe kwana goma da dawowar su Yarima yayi kirmishishi abinsa tana masa mgnr yara zaice ya barwa Jesmin da Abeed gara ta ware ta haifi wasu.

Abeed kam baisan sun dawo ba har sukai wata guda dan duk wata hanya da zasu hadu saida Yarima yasan yadda yayi baya bi iya tashin hankali ta shiga karshe sai mama ta kira a waya.

Cikin kuka tace"mama dan Allah kiwa soulmate fada kawai ya kama yabawa abeed yaran duka idan na masa maganar yaje ya karbo su sai yace wai bazai kyauta ya karbe ba ya riga ya bawa Abeed su gara na ware na haifi wasu ki jishi fa mama kyautar yara har hudu ga amra ta biyar dan kawai baisan zafin haihuwa ba".

Ba mama kawai ba dady dake jin abinda Zainab din ke fada domin hand free mama tayi saida yayi dariya yace"dota in banda abinki aida wasa yake miki shi dinne zai iya kyautar da har biyar idan kika rabu da shi zai dawo miki dasu ganin kin damu ne yasa yake miki yawo da hankali ".

Zainab tace"Allah dady idan na rabu shi shikenan ni dasu bada wasa yake ba dana masa zancen zaice karna dame shi akwai mutumin da yayi kyautar yaya goma kuma ya haifi wasu balle ni mai hudu".

Murmushi mama tayi tace"dota har yanzu kin kasa gane halin baby ki kyale shi ki daina masa mgn da kansa zai dawo miki dasu ta ruwan sanyi "Zainab tace"wallahi mama idan na rabu dashi shikenan ni da su har abada"dariya sukai mata jin abinda tace dady yace"gaskiyar ki dota ki ta masa naci har ya gaji ya dawo miki dasu kinji ko".

Shiru Zainab tai mama cikin tsokana tace"to mukam ba abinda zamuce saidai Allah ya mayar da alkairi "tana fadin haka ta kashe wayar tana dariya tace"kaji dota da wani shirme babyn ne zai iya kyautar da balle ba guda daya ba lallai da anyi ruwa harda Kankara".

Murmushi dady yayi"zan kira shi naji dalilin maida yaran can kinsan shakuwar uwa da d'anta mama tace"babyn da zasu tafi nace ya barmin babana amma ya rufe ido ya tafi da kayansa balle ya bawa wani "dady yace"dama dan baza ta gane bane ta riga ta rude bari zan kira shi lallai ya maida mata karanta".

Bani da chaji👉🏻📱

*🌹Mrs Al'ameen Ahmad*.
[11/25, 5:29 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲

👑Yarima Abdul-malik 👑

*ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫

*@Yusrah M Abubakar*

🅿️1️⃣7️⃣

Watan su Ahmad biyu sannan Yarima yaje ya karbosu murna kam Zainab tayi ta kara har saida taso bawa Yarima dariya ya dan kalleta yana murmushi yace"momyn twins dina sai hankali ya kwanta gasu nan na dawo miki dasu sai rigima ta kare"ya fada yana kallonta harararsa tayi tana hada yaran ta suka bar palon.

Mikewa Yarima yayi yana bin bayansu yace "a'a wallahi baki isa ki raba yara da dadynsu ba gara na biku bansan kus-kus din da za'a saka musu ba dan naga kina min kallon uku saura sisi".

Yanzu komai alhmdllh zainab an zama likita babban asibiti Yarima ya gina mata da kwararrun ma'aikata wadanda suka san abinda suke yi nan da nan ta shahara kowa ya santa ta zama hamshakiya babbar mace.

Bilki duniya ta nuna mata halinta tayi kuka tayi nadama musamman ranar da Hajiya Asma'u taje har gidanta ta fada mata Zainab ta samu danginta kuma tana cikin kyakkyawar rayuwa abin yabawa tayi bakin ciki rashin haduwa da Zainab har ta gode Allah amma tasan zai wuya idan zasu sake haduwa a duniya.

Hajara ta sake haihuwar namiji Mahmud yasa sunan Yarima kowa yayi farin ciki kuma sunzo suna Yarima yayi bajinta sosai a bikin sunan ya zubar da naira ta mmk su mai martaba sun cika da murna ganin komai ya zama daidai yanzu babu wata matsala Yaha dama ba'a magana an shiryu ta gane gaskiya idan kaga suna wasa da dariya da kowa sai abin ya baka mamaki.

Zaune suke a palor suna hira cikin nishadi
Farouq ne ya shigo yana dariya da alama daga makaranta suke yayin da Ahmad ya biyo bayansa rike da hannun Amra yana harararsa karasowa palon sukai.

Amra tace"mummy yau wasu a makaranta sukai fada akan bros dina harda baki aka fasawa wata a cikin su tana ta kuka"da mamaki Zainab tace"su waye suke fadan a kanka? kaga fa bansan iskanci ka daina shiga safgar yaran mutane kana sawa suna fada yaudin su waye sukai fadan"?.

Shiru Ahmad yayi baiyi magana ba amma ya cika yayi fam dashi kamar zaiyi bindiga cikin tsokana Amra dake gaban fridge tana tsiyaya juice tace"wai sonshi suke da friend daya ma cewa tayi duk wacce bata daina kula shiba saita zo da wuka makaranta ta kashe ta".

Zaro ido Zainab tayi tana cewa "subhanallahi abin yayi yawa yayan su waye ne wannan wai Ahmad ba kai nake tambaya ba ka bani amsa "wani tagumi Ahmad yayi yana kallon Zainab yace"mum karya fa take ba wanda yayi fada a school din mu ".

Cikin sauri Farouq ya dawo kusa da Zainab yana cewa "wallahi mumy ba karya Amra take ba kinsan July ta gidansu Elijah? kai Zainab ta daga Farouq yaci gaba "to itace suke fada da pretty kowa son bros take shine angeli tace duk yarinyar da taga ta sake masa mgn sai ta zubar mata da hakora".

Zainab tace"ina abin bai kainan ba gara a sauya masa makaranta ba zafi"Amra tace "mum ranar ma viki sunyi fada da nazi dakyar aka raba su"kallon Yarima Zainab tayi taga ko a jikinsa".

Tace "kana jin mufa dan Allah kawai a sauya masa school ni bana son tashin hankali ko kuma a mayar dashi gurin mama yayi karatun sa acan muma hankalin mu zaifi kwanciya".

Murmushi Yarima yayi yana kallonta yace"babu inda boy dina zaije yana nan tare da 'yan uwanshi dan wasu yara na fada akanshi duk haukan su suke mai zaiyi da kirista idan ya tashi aure a mutum biyu zai zabi daya ko dai ya auri 'yar gidan Abeed minat ko kuma 'yar gidan Aliyu Aynul-hayat amma ba wata viki nazi da zai so.

Dariya Farouq yayi yana kallon Ahmad yace"ni kuwa dama nace sultana Aisha nake so bros kuma na zaba masa Aynul-hayat tunda balarabiya ce"Zainab tace"a'a duka biyun zai aura shikenan ina da suruka baturiya da balarabiya"bata fuska Ahmad yayi yana mikewa yabar palon Farouq yabi bayansa shi da Amra akabar iya twins.

Yarima dake kallon Zainab yace"kinyi waya da small mum dina suna lafiya"? cikin rashin fahimta Zainab tace"wacce haka"Yarima yace"matar Mustapha nake nufi shidin tunda uncle dina ne"Zainab dake shirin tashi ta koma ta zauna tana cewa "na fita fa ko lokacin da muke zuwa makaranta na girmeta".

Murmushi Yarima yayi"albishirin ki ko shekara dubu kikai a duniya dole kice mata mama tunda babanki Mustapha ta aura inta kama kika tashi gaida ita ki rika durkusawa kamar yadda kike wa mama da dady" .

Zainab tace"tab aikwa ba zata samu ba wuce nan"mikewa tayi zata tafi ya rike ta yana cewa "haba princess fushi kike dani soulmate dinki guda tafiya zaki ki barni"kafa ta fara bubbugawa cikin shagwaba tace"nidai a'a sake ni tunda ni yyarinya ce".

Kara rungumeta yayi yace"haba mummyn boy waye yace ke yarinya ce bayan kina da zaratan samari har hudu kaga mum din Ahmad gatan Farouq ummin twins gaskiya ina mutuwar sonki mamata kin gama min komai a rayuwa burina Allah ya barmu tare ni da ke".

Murmushi tayi tana cewa"nice ya kamata na maka gdy domin ka taimaka min a lokacin da nake cikin kuncin rayuwa kayi tattalina ka kareni daga makiyana kaban abinda har abada wata mace bazata samu ba kayi min kyautar xuciyarka bani da wata kalma dazan iya gode maka kawai saidai nace ina matukar kaunar bazan guje ka ba muna tare har karshen rayuwata soulmate ".

Juyowa yayi da ita suna fuskantar juna cikin jin dadi kowa ke kallon dan uwanshi murmushi suka saki tare suna kara rungume juna daidai su Ahmad sun fito suka mike suna karasawa dining cikin farin ciki gasu ga zuri'ar su.

*🌹ALHMDLLH*
*Masha Allah*

*Ya Rabbi salli ala sahibul mukami Annabin da mai sonsa bai zama a hammi sa alihi da sahabban sa zul kirami a'alal ula duk makiyin su ya makanta*.

#YUSRAHMS ABUBAKAR #

Ana tare 'yan ANNURI gaisuwa mara adadi.

*Mrs Al'ameen Ahmad ce* . ❤🌹
Chapter 20 · 0% Book details