← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 20

Sashe 12

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👑Yarima Abdul-malik 👑

💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫

#Mrs Al'ameen Ahmed ce

*Allah dakai ne nina dogara, kaine kake min dukka sutura, duka halitta kai take jira, ya mai sifar girma da gagara.

🅿️8️⃣

An gama komai na mgnr auren Abba da Salmah jikar sarkin bauchi ba wanda ya sani a cikin Yaha da mama saida biki ya rage kwana goma suka ji mai martaba na zancen kai akwatuna da za'ai wai Yaha kam ba kunya a gaban mai martaba taci kwalar Abba tana kururuwa da kuka tana faduwa kasa dan Allah mai martaba ya hana Abba karya mata kishiya kukan ta saida ya firgita kowa amma ido da ido Abba yace babu abinda dazai hana shi yin wannan auren sai mutuwa lokacin daya fadi haka ihu Yaha tai ta yanki jiki ta fadi a sume sai asibiti aka kaita.

Kishi kumallon mu inji masu magana.

Yarima na palor suna waya da Mustapha Musty yake ce masa "Abdul-malik idan na gama abinda nake inason zan biyo tanan na kawo muku ziyara naga matar ka mu gaisa"Yarima dake kallon Zainab data dago itama tana kallon shi ya maida hankalin sa kan wayar da yake yana cewa "no thank basai kazo ba ba bukatar ku hadu yanzu ka bari sai lokaci yayi idan kuma kai asarar kudin ka kazo to zan hana abarka ka shigo gidan kaga kazo a banza gara ka wuce Nigeria daga nan zaku hadu wata rana "cikin haushi Musty yace "wai dan Allah Abdul-malik me yasa kake min haka? kasan Allah idan muka hadu saina shuka ma rashin mutunci sbd bakin ciki matar taka ma baka so na gani saika dafa ta ka cinye "murmushi Yarima yayi yana matso da Zainab kusa da shi yace "saika shuka rashin mutuncin naka yanzu kaga kafin mu hadu ya girma, cinyewa kuma bazan cinye ta ba amma bari na mata abinda da zakaji "kiss ya sakar mata kumatun dama da hagu wanda yasa Musty kashe kiran yana dariya yace "Allah Abdul-malik baida kunya ko kadan.

Kallonsa Zainab tayi tana "dawa kake waya "? rungumeta yayi yana cewa "da wani uncle dina ne yake damu na ya cika takura kamar gidan haya "dan matsawa baya Zainab tayi ganin mai musu aiki ta fito a kitchen tace "ga siana ta fito ka sake ni "dagowa yayi yana kallonta yace "mene ruwan ta damu ke kike naki yi bahaushiya kawai"dukawa siana tai tana gaida su ba kunya saida Yarima yai kissing bakin Zainab sannan ya amsa wanda saida Zainab taji tamkar ta nutse a kasa babu ruwansa sau tari Siana na palon sai yaita zuba soyayyar sa cikin shagwaba Zainab tace "dan Allah ka bari wannan ai saita raina ni"kallonta yayi yana murmushi ya maimaita kalmar saita raina ni lallai Zainab akwai son girma siana a kalla zatai 27 years take kiran zata raina ta ita mai 20 mikewa yai yana daukar ta yace "haka ne zata raina ki anan muje inda bazata gani ba na baki wani abu mai kyau "ya fada yana wucewa da ita.

Duk tunanin Yaha idan Abba yaga wannan kukan datai da ramewa zai janye mgnr auren sa amma sai taga yaci gaba da hidimar sa ko a silifas dinshi wanda hakan ba karamin daga mata hankali yayi ba ko akwatuna dayai mata cewa tai bata so yakai wacce take bukata ba tare daya nuna damuwa akan abinda tace ba ya hade su da wanda za'a kai bauchi Yaha tayi kukan bakin ciki harta godewa Allah amma Abba yai kamar baisan me take ba dan ya gaji da halin ta gara ya auro wacce tasan abinda takeyi duk da kasantuwar ta yarinya dan Salmah bazata wuce 25 ba sai kyau da diri.

Hhhh Abba banga laifin ka ba yan ANNURI shoki zamu diba ranar daurin aure.

Yaha na zaune duk abin duniya ya dame ta gashi Hajara ta fara gagarar ta bata isa da ita ba duk wannan ma bashi bane abin daya fi mugun daga mata hankali yau ake daurin auren Abba gida tab yake da baki Yarima shima yazo amma banda Zainab acan ya barta.

Cikin harara yaha kebin dangin Salmah da suke kai kawo a part din da Salman zata zauna zuwa part Abba ji take kamar ta kunna wuta kowa ya kone ayi mutuwar kasko jin gidan ya kacame da algaita da kirari yasa jiki na rawa Yaha tasa hijab ta fita turus tai ganin an bude mota amarya ta fito a lullube ihu ta zunduma tana kuka ta juya part dinta da gudu shewa wasu daga cikin yan kawo amarya sukai suna cewa "lallai aiki ga mai yinka kishaya dai tazo kuma baza a mayar ta ba dan Salmah ita da Ibrahim mutu ka raba haka zaki ganta haka zaki barta dan tafi karfinki gaba da baya "yaha na shiga bedroom dinta taga Hajara na rawa Mahmud na mata liki da kayan anko a jikin sa hannu ta daga ta wanka mai mari tare da daukar wayar tasa daya kunna wakar ta buga ta a jikin bango ganin bata fashe ba taci gaba da dokawa saida screen din wayar yai damage sannan ta cillar da ita cikin masifa tace "so kuke ku kashe ni dame zanji daku koda wadancan tsinannun masu kama da aljanu zaku cika min kunne mitsiyatan yara "tabe baki Hajara tai tana cewa "umma meyai zafi bafa mune muka karo miki kishiya ba mijin ki ne aishi zakije kiwa ba mu yan gayyar sodi ba "kanta Yaha tai tana cewa "dan ubanki ni kike fadawa mgn mitsiyaciya "ganin ta nufo ta aguje ta fita daga dakin tana dariya sannan ta leko tace "umma baki sun shigo da amarya suna jiran ki a palor zasu baki amanar ta ki rika mata wanki da guga kina dafa mata abinci da sharar part dinta "ashar Yaha ta sakar mata daidai Mahmud zai fita tasha gaban sa ganin ya dauka mata ATM tace "gidan ubanwa zaka kaimin atm "? kallonta yai yana cewa "haba umma kiji wata tambaya ki fasa min waya kuma ki tambayi me zanyi da atm dinki kudin wayata zan cira na sayo wata million daya ne da dubu dari biyu ba yawa karamar kika fasa min bani code din zan tafi "banza tayi dashi ta gefen ta ya wuce yana cewa "ok na manta ashe last moon na ciro miki kudi a account naki code din 1834 ne ni na wuce "fita yai yabar Yaha ta rasa inda zata dura kanta.

Wayyo abin tausayi 😔abin dariya 😂.

Bayan wata hudu da auren Abba komai ya fara sauki ba kamar da ba.

Yarima na zaune suna video call da mama Zainab ta fito tana saukowa daga stairs da mini riga a jikinta dan yanzu inba kananun kaya tasa ba ita ma bata jin dadi purple din din riga ce ta matse ta sosai tayi kyau ta kara kiba da haske cup ta dauka tana hada kyakkyawar madara ta zauna a dinning tana sha.

Yarima dakewa mama murmushi ya dago yana kallonta da hannu ya mata alama tazo mikewa tai tana zuwa inda yake jawota yayi yana zaunar da ita akan kafar shi yace "mama ga dotar taki da kike nema yanzu ta tashi a bacci sai ki tambaye ta basai na zama jakada ba "zaro ido Zainab tai dan ita batai tunanin waya yake ba ga mama free tana kallonta da sauri ta mike ya maida ita yana cewa "mgn fa zakuyi ina zaki kuma "? kasa daga ido Zainab tai ta kalli mama sbd kunya mama kuwa cike da wani irin mamakin dayasa taji kanta na juyawa take kallon Zainab tana cewa "baby wai dama dota ciki ne da ita amma baka fada min ba"? dan kallon Zainab yayi yana cewa mama "sorry mom dinna mantawa nai "cikin farin ciki mama tace "to mezai hana ka dawo da ita nan idan ta haihu saita dawo tunda yanzun nan ammi ta kira ni take cemin an tsayar da ranar auren Mustapha kaga gara ta haihu a gabana"bata fuska Yarima yai jin abinda mama tace cikin shagwaba yace "a'a dan Allah mama abar zuwan nan lokacin dawowar mu Nigeria baiyi ba anan din ma za'a kula da ita "mama da tun dazu Zainab take kallo mmkn ta ya kasa karewa ganin cikin ma yayi wayo sosai tace "to baby shikenan Allah ya sauke ta lf, amma zaka zo bikin Mustaphan ai"? dan shiru yai sai kuma yace "gaskiya bazan samu zuwa ina da aiyuka bayan haka banzan iya tahowa na barta ita kadai ba amma zan kira shi zamu yi mgn"to mama tace tana kallon Zainab da tunda suka fara mgn bata iya dagowa ba tace "dota kinki mgn ko yaushe ne haihuwan "? tashi Zainab tai da sauri tabar wurin dariya mama tai tana cewa "dan Allah baby ka kula min da yarinyar nan ina sonta sosai "insha Allahu yarima yace bayan sunyi sallama ya kira Musty suna waya yana bashi hakurin cewa bazai samu damar zuwa ba madam tayi nauyi dariya Musty yayi "naji to dan iska basai ka fada min tayi nauyi ba kawai kace bata da lfy malam kai baka iya fulatanci ba "yarima yace akan me zan iya bayan bashi bane ka taya ni da addu'ar Allah ya sauke ta lfy na samu kyakkyawar baby nai kama da ita "rike baki Musty yai "lallai prince ka wuce ma tunani na to Allah ya kawo yan biyu "ameen Yarima yace "kamin addu'a mai kyau ni inada son yara ko yan goma ne Allah ya kawo su dan haka sai anjima ka dame ni "dariya Musty yayi daidai zai kashe wayar yace "sannu uban yan sharri sai anjima nima gurin tawa abar kaunar zan tafi na tsaya kana bata min lokaci "sallama sukai.

Yau anan zan tsaya ayi hakuri typing din baida yawa aiki zanyi ne.

*Mrs Al'ameen Ahmed *

Dukka muradi baya cika saiyai bara a gurin ka mai duka dakai makaskanci ya daukaka kaine kasa ka'aba a garin makka.

Manzon Allah (s.a. w) a farkon bukata ta kaunar ka itace abinda na roka.

#Yusrah Musa Abubakar.
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲

*👑YARIMA ABDUL-MALIK*👑

*💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫

WHATSAPP NO:+2349055273614

*#YUSRAHMS ABUBAKAR*#

*🌹TAMBARIN 👉🏻YMA DUTSE*🌹
Chapter 12 · 0% Book details