← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 20

Sashe 16

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shiga palon ammi mama ce a gaba Zainab na biye da ita cikin murmushi ammi ke kallon mama da farin ciki zatai mgn idonta ya sauka akan Zainab a firgice ta mike tana nuna ta da yatsa murya na rawa tace "Amina a ina kika samo wannan "?da mmk mama tace"matar baby ce ammi lafiya "? cikin tashin hankali ammi ke girgiza kai tace "Amina duk inda yarinyar nan ta fito jinin Khadija nace kalli kamar mana dakyau jini baya buya"zubawa Zainab ido mama tayi cikin wani irin yanayi ta kasa mgn.

Yarima dake tsaye dama yasan haka zata faru karasowa yayi yana nuna photon yace"ammi itafa kinga mahaifiyar ta "karbar photon ammi tayi tana kallo kuka ne kawai ya kwace mata a wannan lokacin mama da itama cikin mmk take kallo tace"dota a ina kika samo wannan photon "? Zainab da duk jikin ta yayi sanyi dakyar tace"mahaifiya tace"mikewa tsaye mama tayi cikin zaro ido tace "Khadijan dama itace ta haife ki? kedin jini nace 'yar gidan kanwa ta uwa daya uba daya ban sani ba innalillahi wa inna ilaihi raji'u"shine kadai kalmar da mama ke iya maimatawa ammi kam babu bakin mgn sai hawaye daya ki tsayawa.

Mustapha shigowar sa kenan yaga Zainab a firgice yace"Zainab Umar dama kina nan"? Kallonsa ammi tayi "ka santa ne"? kai ya jinjina Fati dake bayanshi itama ta kame dan mmk gani take kamar a mafarki ba Zainab ce a zahiri ba.

Cikin magiya ammi tace wa Zainab "dan Allah ki fada min inda Khadija na take naje na ganta"Zainab da itama yanzun ta kasa rike nata kukan tace"ta dade da rasuwa tun ina shekara 12 salati ammi keyi tana cewa "shikenan Khadija sallamar karshe mukai dake zaki tafi makaranta ashe shine rabuwa ta dake saidai naga jininki Allah yaji kanki da rahma"sun dade ba mai iya lallashin wani saida kowa ya daina kukan dan kansa.

Mustaphan ya bada labarin abinda ya sani game da ita fati ita ce ta bada dan cikakken bayani cewa.

*Mrs Al'ameen Ahmed ce*

Love for ever yan ANNURI 😍🍒ana tare.
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲

*👑Yarima Abdul-malik*👑

*ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫

*#YUSRAHMS ABUBAKAR*#

🅿️1️⃣1️⃣

Fati ce ta bada dan bayani kadan game da zuwan Khadija anguwar su kamar yadda taji ummanta na fada tace"kaka Abdullahi yace wata rana suna zaune da Umar suka hango ta tafe tun daga nesa har ta karaso kusa a yanayin ta bai nuna tasan inda take nufa ba ganin haka yasa kaka Abdullahi yai kiran matar sa cewa tazo ta rike ta a zaton idan suka bata abinci taci zasu samu dan wani bayani daga bakin ta amma shiru sai kaka Abdullahi ya soma shawarar yi mata magani a zaton sa sammu ne daga baya dayai mata maganin ya fahimci cewa ba maganin gargajiya cutarta ke bukata ba yayi shawara da Umar suka kaita asibiti aka fara yi mata magani domin a yadda bincike ya nuna allura ce aka mata dan ta manta komai na rayuwarta ta baya anyi nasara ta dawo hankalinta amma da aka tambaye ta danginta ko gidan su da wani abu data tuno tace batasan komai ba a haka ta zauna a gidan kaka Abdullahi zuwa wani lokaci kafin Umar ya bukaci aurenta kaka Abdullahi ya bashi da kudin sadakinta ya kara nasa kudin akai ya mata kayan daki dukda Umar yana da mace Bilkisu a haka suke zaune har bayan an haifi Zainab da shekara 12 duka ta rasa mahaifanta ta koma rayuwa cikin wahala a hannun Bilki wannan shi kadai na sani a labarin Khadija ki ammi"Fati ta karasa maganar cikin sauke numfashi dan ganin yadda jikin kowannen su yayi.

Babu mai mgn ammi tace"tabbas Habiba ta cuce ni ta rabani da farin ciki na biyu a lokaci daya a ranar da zata mutu ta nemi gafara ta cewa itace silar batan Khadija sbd taga irin son da Ahmad yake mata sai tasau tsanar duniya ta dora mata har tayi sanadin barinta gidan nan bayan ta tafi makaranta tasa aka dauke ta a mota tare da yi mata allurar da zata manta komai nata da naji haka ban fidda rai da zan ganta ba koda ba a cikin hankalinta bane amma hakan bai samu ba shi kansa Ahmad dayaji abinda Habiba ta fada kafin mutuwar ta ya tsoma masa zuciya ya kuma tayar masa da hankali dahar yasa ciwon hawan jini ya kama shi wanda shine ajalinsa Habiba ta cutar damu shikenan yanzu nida Khadija saidai naga jininta"ta fada tana share hawayen dake kara zubo mata.

Ganin duk guri ya rude yasa Yarima rike hannun Zainab suka bar palon dan ta samu nutsuwa dan indai tana gurin suna kallonta abin ne zaiyi ta yimusu gizo ne.

Ameen 👏🌹🌺
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲

*👑Yarima Abdul-malik*👑

*#Mrs Al'ameen Ahmad#*

🅿️1️⃣2️⃣

Washe gari tun wuri ammi tace suje gurin kaka Abdullahi domin yi masa godiyar abinda ya musu na maganin Khadija da rike ta dayayi tamkar 'yar daya haifa lokacin da kaka Abdullahi ya gansu kuma suka mai bayani ya jinjina al'amarin yayi farin ciki ya kuma yi mmk dayaga cewa iyayen Mustapha mijin jikarsa Fatima sune kakanun Zainab babu wanda ya taba tunanin hakan zata kasance.

Hjy Asma'u kan harda rawar farin ciki tayi a gaban su suna ta yi mata dariya Asma'u tace"sau dubu idan zan bude ido naga danginki Zainab to sai nayi rawar jin dadi "murmushi Zainab tayi tana cewa "dan Allah inason naje gurin umma "tsayawa Asma'u tayi tana kallon ta tace "badai kina nufin kije gurin Bilki ba mai zakiyo mata kin manta duk abinda data miki kenan "? Cikin marairaicewa Zainab tace"dan Allah ina so na ganta ne kawai "hararar ta Fati tayi tace"da yake abin arziki ta miki ba shiyasa zaki nemeta "banza Zainab ta mata tana kallon Asma'u tace"abinda ta min ya riga ya wuce nidai ina so naje mu gaisa"girgiza kai Asma'u tayi tana cewa "Bilki dai ko kinje bazaki same taba domin jiya 'yan sanda suka zo har gida suka kamata kawarta Aliyah ce tayi kararta akan ta cinye mata kudi kuma ba ita kadai ba mutane da yawa ta narkar musu da kudi dan haka tana bayan kanta saidai idan candin zakije".

Cikin damuwa Zainab tace "eh fati tashi ki rakani zan biya kudin a fito da ita "Fati dake duba waya tace "bazanje zo ki daura min igiya a kafa sai kijani kikai watan tsoron ki bai kama ba 'yar me abin duka kawai"shiru Zainab tayi tana tunani zuwa wani lokaci tace"to rakani gurin inna "Asma'u dake shirin barin gun tace "inna ta sauya anguwa tabar nan wasu yan hayar ne a gidan "dole Zainab ta hakura dan an gama kure ta tana gani suka bar anguwar kamar zatai kuka domin taso zuwa gidan sosai dan Asma'u taki barinta ne.

Kwanan su biyar amma Zainab bata samu damar ganin Bilki ba dan Yarima ya hanata zuwa dole tabar batun suna zaune a palon ammi ana fira su Ahmad suka fito shida Rufaida 'yar gidan Mustapha zama sukai a kusa da fati mama tace"dota hadawa yaran nan kayan breakfast tunda sun tashi"to Zainab tace tana bude kulolin tana kallon Ahmad tace"boy wanne kake so "? dauke kai yayi daga kallon kulolin alamar babu mama da hankalinta ke kanshi tace"me kake nufi bazaka ci ba"? daga kai yayi yana cewa"grandy nifa bana cin wannan nafi son tart "harararsa Zainab tayi tana cewa "kafi son tart ba a London kake ba idan na karajin bakinka ya kira tart din nan saina rushe ma wadannan kananan hakoran"Ahmad daya rike kunnansa tunda Zainab ta soma fada alamar ya tuba yace"mum nifa yau azumi nake"ba shiri Zainab ta kau da kai tana murmushi jin abinda yace dariya mama tayi tana cewa "baby ka masa mgn ko zaici "cikin shagwaba Yarima yace"haba dai ki barshi yayi koma lokacinsa ne ko my boy"? dariya gabadaya akai ganin yadda yake shagwaba san ransa a gaban yayansa .

Zainab ta hada tea tana jawo ahmad ganin yana shirin guduwa tace"zan saba makafa boy ka bude min bakin ka "kuka ya fara sai data zazzare masa ido sannan ta samu ya soma sha Mustapha yace "nifa ban gane ba naga tunda kuka zo gidan nan baya cin abinci da kansa sai kin dura masa meyasa haka"? kallon Yarima Zainab tayi alamar in fasa kwan aikuwa ya cillo mata harara rufe baki tayi tana dariya tace"ka tambayi old man dinshi zai baka amsa abinda dayasa baya cin abinci da kansa "cikin haushi Yarima yace "kinga ki kiyaye ni"kallonsa Musty yayi "kaga malam daga ance na tambaye ka shine abun fushi"Yarima dake harararsa yace"ban sako dakai ba uban 'yan shishshigi da mata ta nake"dariya Musty yayi"gaskiya ne dadyn boy wannan action din naka yayi, aunty me yasa yaron na bayacin abinci da kansa"? mama tace "nima ban sani ba a gurin babansa ya gada shima har yayi aure dura nake masa"dariya sosai Musty keyi cikin tsokana yace"saidai hakan fa ashe gado ne baka da laifi yaro gaskiya prince Allah ya shirye ka kaidin dan asara sai kace wani baru sai ana maka dura "banza Yarima ya masa mama ce tace"bansan iskanci fa Mustapha aiba laifi bane danna bashi abinci a baki gata ne ya kawo haka"danne dariyar Musty yayi yace"haka ne aunty ayimin afuwa".

Ahmad da shagwabar shi ya nufi gurin Yarima yana cewa"dadyna mum ta cika min cikina zai fashe"Yarima yasan mai Ahmad yake nufi mikewa yayi yana goyonsa ya fara yawo dashi a palon Zainab dake dariya tace"wannan abin yana bani sugar "a kule Yarima yayo kanta tayi tsalle ta koma kusa da ammi musty yace"gaskiya kai mugu ne daga tace haka rama abinda kaiwa aunty yake yi "yarima baiyi masa mgn ba ya dire Ahmad zai zauna kenan farouq ma ya mika masa hannu ganin suna neman karasa shi yace"ku tashi muje kusha ice cream "cikin murna suka mike harsu Rufaida suka tafi
washe gari sukai shiri suka koma Abuja bayan sunbar su ammi da kewar su.
Chapter 16 · 0% Book details