← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 20

Sashe 11

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari tunda Zainab ta koma part din mama ta kasa hada ido da ita mama yi tai kamar batasan me take ba taci gaba da hada mata kayanta sai bayan sallar la'asar suka bar masarautar bayan sunsha dunbin addu'o'i a gurin su mai martaba mama dai jitai kamar sun tafi da ranta saboda kewa.

Sautin kukan Hajara ne kadai ke tashi a bedroom din Yahanasu cikin kuka take cewa "wallahi umma bazan yarda ba nima na fasa karatun auren nake so ni Abdul-malik nake so wacce bata da asali ma ta same shi balle ni jinin sarauta gaba da baya dan Allah kije ki samu mai martaba nima a daura nawa na bisu London din "cikin lallashi Yaha tace "kinga Hajara ki kwantar da hankalin ki wata hudu tamkar kwana hudu ne aure kuma zaki aure shi dan Zainab ba matar sa bace kashe ta zamuyi ke kadai zaki zauna baki da kishiya amma saikin nutsu "kara volume din kukan ta tayi "ni wallahi bazan yarda ba kije kawai kuyi mgn da su mai martaba "cikin bacin rai Yaha ta mike tana cewa "dan ubanki bazan jeba kije da kanki tunda ban isa na fada miki ba bakyajin shawara sai kije ki karata ko ki kashe kanki aishi gaba takai shi dama bason aurenki yake ba ranar juma'ar nan akanki tun daka part dinsa yake jana tamkar ya sayo sabuwar akuya a kasuwa har gaban mai martaba yamin rashin mutumci saida naji kamar na hadiyi zuciya na mutu dan bakin ciki idan kika kuma yimin mgnr sa indai ba dawowa yai ba saikin tattara kayan ki kin koma gida "tana fadin haka tai hanyar fita a bedroom din cikin kunkuni Hajara tace "wallahi ba wanda ya isa ya sani nabar masarautar nan a yanzu ko mai martaba ne saidai in na auri Abdul-malik "juyowa Yaha tai tana kallonta tace "zaki ci ubanki shegiya duk kin bata fuskar ki da mai"da harara Hajara ta bita tana cewa "wa yace idan ban shafa man nayi fari ba yarima ko kallo ban ishe shi ba "? Banza Yaha ta mata ta fice tsaki Hajara tai tana goge hawayen fuskar ta ta gyara kwanciya tana cewa "ba hakura nai ba dakai Abdul-malik saina aure ka.

Aiki gamai yinka mukan yan kallo ne.

Su Yarima basu sauka ba sai cikin dare dagowa yai da niyyar yiwa Zainab mgn yaga ashe ita bacci ma take abinta cire mata bel din yayi ya dauke ta a haka yake saukowa daga matakalar jirgin sosai aka zo tarar sa abokai da mutanen arziki babu bata lokaci suka wuce bayan ya shiga mota har gida sukai masa rakiya yakai Zainab daki yazo suka gaggaisa kafin ya musu saida safe ya koma wanka yai ya dauro alwala yayi sallar isha da ake binsa yasa kayan bacci ya kwanta.

Koda asuba ya riga ta tashi sai da yai alwala sannan ya tashe ta zaune ta mike bata lura da yanayin jikin ta ba sai data sauka a gadon zaro ido tai tana kallon shi batare daya kalle ta ba yace "kije kiyi alwala ki rama sallar da ake binki kar lokaci ya kure "waje ya fita zuwa masallaci ita kuma ta dauro alwala ta sa kaya ta fara gabatar da sallah ta kuma yiwa Allah godiya da sauyin rayuwar dayai mata bacci ta koma bayan sallar asuba kafin gari ya waye, karfe 10amta tashi tai wanka saida gama komai taje saka kaya taga babu wanda mama ta sako mata ko daya dubawa ta farayi ganin ba wanda yai mata yasa ta zauna shiru a gaban akwatin har ya tashi a nasa baccin yai wanka ya shirya cikin kayan soja ya gama komai tana zaune dan kallonta yai yana kallon akwatin yace "sauri ki shiya ke nake jira ina da meeting kada ki bata min lokaci "kamar zatai kuka tace kayan babu wanda zansa wannan kuma na arna ne "ba shiri ya dago yana kallonta kayan ya fara dubawa yana cewa "daga yau sune kayan sawar ki atamfa ko lace kin baro su a Nigeria "ya karasa maganar yana dauko wata bakar doguwar riga yace "sa wannan mu gani ko na arnan ne "turo baki tai "wallahi ni bazan iya sa wannan kayan ba "jin abinda tace yasa ya mike tsaye yana takawa inda take da sauri ta jada baya kanta farga yasa hannu ya jawota ta fado jikin sa daure fuska yai yace "yaushe na fara wasa dake "? Tsoro ne ya kamata ta soma bashi hakuri shareta yai yana sa mata rigar da yake fara ce sai bakar rigar ta mata mugun kyau sosai rigar ta nuna shape dinta saidai itama tsaga tun daga cinya har kasa kuma ta gaba ma kusan rabin kirjinta a waje ta baya ma kusan rabin bayan ta a waje tsayawa yai yana kare mata kallo cikin sauri tai niyyar juya masa baya ya rike hannuwanta yaci gaba da kare mata kallo runtse ido tai cikin kunya ganin ta rufe ido yasa yace "bude idonki "kara kullewa tai da yake a gaban mirror suke saiya juyar da ita yana zagaya hannunsa a cikin ta yace "baki jiba "? Kin budewa tai amma jin ya daura hannunsa a saman kirjinta yasa cikin sauri ta bude ta mudubin suka hada ido ganin har lokacin kallonta yake sai kawai ta sunkuyar da kanta jan hannunta yai suka sauka stairs yace "ke bakya jin mgn ko? zanyi maganin ki ne bari dare yayi"batai magana ba har suka sauko dinning shake da kayan abinci kala Kala zama sukai Zainab kam Yarima ta zubawa ido taga yau daba mama daya zaici abinci ga mmkn ta mint tea ya hada a mini cup yana sha ganin ta kure shi da kallo yasa ya daga mata gira alamar tambaya kai ta girgiza tana ci gaba dacin abincin ta saida suka hada ya mike ya wanke bakin sa yana fita a gida Zainab daki ta koma suna waya da mama tambayar ta mama tai yaya jikin ta da sauri ta kashe kiran tana rufe ido kamar maman na gurin .

Da dare hartai bacci bai dawo ba sai da safe ta ganshi ko takwas batai ba yasa ta shiya suka tafi wani kayattaccen guri ga mmkn ta makaranta ce bata sake tsinkewa ba da Yarima yace zata dora karatun ta saida taga ya fito da takardun makarantar ta abin yai mugun bata mamaki bata tambaye shi ba saida suka dawo gida ta kalleshi tace cewa "a ina ka samu takardun makaranta na dady ya tambaye amma nace masa sun fadi "dan kallon ta yai "au dama kina mgn ai na dauka kurma na aura "rufe fuska tai tana dariya yace "lokacin dana bige ki a mota naga jakan ga sauran abubuwan ciki" mika mata yai ta karba tana kallon photon ummanta wanda lokaci guda ta shiga yanayi shima ya fahimci damuwar da take ciki dan haka ya dau abarsa sukai daki ya matar da ita duk abinda ke damun ta.

Hayaniya inna dake daki ta jiyo da sauri ta fito duk zaton ta koda Zainab ne dan yau ta dawo daga garin su shigowar ta kenan ko hutawa batai ba da sauri ta karaso ganin Bashir ya shakewa Bilki wuya cikin tashin hankali inna tace "dan Allah Bashari sake ta bari kada kai kisan kai "sakinta Bashir yai yana huci yace "wallahi kinci darajar wannan tsohuwar da yau saidai ki kwanan lahira "mmk ne ya kama inna amma batai magana ba dan sunfi kusa juyawa tai zata bar gurin da sauri Bilki ta rike ta tana kuka tace "dan Allah inna kimin rai ki hana bashir zuwa gidan nan wallahi zai kashe ni "wani kallo inna ke binta dashi domin a iya sanin ta tun kafin tazo bashir ke zuwa gidan nan amma yau rana tsaka take neman a hana shi zuwa lallai akwai mgn Bashir da tun dazu yake kallon Bilki sai yanzun ya mayar da kallonsa gun inna yana cewa "danfa inajin kunyar kine na kyale ta amma yau da sai naga ta daina motsi dana barta dan ta raina min hankali shekara ta nawa tana cin kudina amma danta kori Zainab shine zatai min halin yan duniya, duk abinda kikeji dashi na fiki iskancin da barikin sai na ga iya kwarewar ki "ya kasara mgnr yana kai mata naushi da sauri ta koma bayan inna wacce taji maganar kamar saukar aradu wai Bilki ta kori Zainab juyawa tai tace "da gaske Bilki kin kori yarinyar nan? wai me tamiki haka a rayuwa da bakya kaunar ta da alkairi yanzu kinsan a wanne hali take ko abinda ya sameta gaskiya ke butulu ce da Umar yasan zaki wulakanta bayan sa daya fadawa yarinyar nan asalin sa ko bayan ransa taje ta same su hakkin Zainab bazai taba barinki ba har kabarin ki da nasan abinda kika aikata kenan bazan fito ba inya so Basharin ya kashe ki ni wannan gara na sauya gidan haya dan idan naci gaba da zama anan wata rana harni za'a kashe a kakalo masifarki "tana kaiwa nan ta wuce tana takaicin yanzu ina Zainab din take a wanne yanayi take ganin Bilki ta biyo ta yasa ta karasa daki da sauri tana rufo kofa cikin bacin rai kuka Bilki keyi Bashir kuma yai fitar sa a gidan kallon Hindu dake kwance ga ciki ya fara fita tai sai kawai ta durkusa tana kuka yanzu me zata cewa iyayen yarinyar nan, nikam nace oho.

Fati ce kwance a daki duk ta rame saboda damuwar batan Zainab hjy Asma'u ta shigo tana cewa "Fatima dan Allah ki hakuri haka ki dau dangana ya zamuyi da kaddara ta riga fata tun farko saida nacewa baba Abdullahi ya bani Zainab nai rainonta amma yace aa bai kamata a karbe ta daga hannun Bilkisu ba gashi yanzu abinda ya biyo baya kinga kiyi hakuri in Allah ya yarda za'a ganta tashi kici abinci "mikewa zaune tai tana karban plate din kwata kwata bata so haka ba sai lokacin farin cikin su za'a tarwatsa musu rayuwa.

Masha Allah bintu Musa Abubakar ta gama typing yau cikin yardar ubangiji sai Allah ya tashe mu lafiya gobe zamu ci gaba.

*Mrs Al'ameen Ahmed ce *
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: Typing 📲
Chapter 11 · 0% Book details